Matakai 10 Da Za A Bi Don Magance Ƙwatar Waya Da Sauran Laifuffuka Da Matasa Ke Yi

Matakai 10 Da Za A Bi Don Magance Ƙwatar Waya Da Sauran Laifuffuka Da Matasa Ke Yi daga bakin alƙallamin Muhammad Tajajjini

Satar Waya

Tijjani M.M.

Yanzu dai ƙwatar waya da rana tsaka na nema ya zama ruwan dare a cikin al'umarmu inda za ka ga matasa sun tari mace ko namiji da muggan makamai kai har ma da bindiga su ce a basu waya ko su kashe mutum.

Banda wannan yanzu abu ne da ba komai ba ka samu matasa da dududu ba su kai shekaru ashirin ba sun yi garkuwa da mutane wasu ma iyayensu, y'an uwansu, kannensu, makwabtansu da dai sauransu don neman kuɗin fansa.

Ga kuma waɗanda za ka samu sun haura katanga sun yiwa mata da yara ƙanana fyaɗe su yi sata sannan su kashe na kashewa don an gane ko su waye a yayin aikata wannan aika-aikar.

Sannan ga wasu matasan musamman mata da ake haɗa baki da su wajen shunawa mutane ko masu arzinkin unguwa b'arayi don shiga ayi musu satar gwalagwalai lokacin biki ko ta mota ko na kuɗi cikin dare.

Sai wasu da ƙawaye za su shirya a ɗauki mace zuwa wajen y'an tsafe-tsafe,  tsubbu da shirka don mallakar miji ko neman kujerar muƙami ko ta siyasa banda kawalai masu kai ƙawaye, y'ay'ansu da ma matan aure wajen manemansu na haramun.

Duk kuwa ire-iren waɗannan abubuwan masha'a na faruwa ne mafi akasari saboda rashin aikin yi ko ƙwaɗayin kuɗancewa ko ta halin ƙaƙa da masu aikata hakan su ke yi. Hakan kuwa ba ƙaramar barazana ba ce ga yin rayuwa ingantacciya ga al'umarmu.

 

MATSALAR DAKE AKWAI

Muna nema ne mu barwa matasanmu rashin zaɓi a rayuwa idan ba na yin laifuffuka da ta'addanci ba saboda tsabagen rashin adalci daga shuwagabanni da iyayen yara da matasanmu.

Rashin ADALCI kamar yaya? Na ƙin bawa mai haƙƙi haƙƙinsa a kan lokaci.

INA MAFITA?

1. Dole a gina wani tsari wanda lallai-lallai mai dorewa ne na koyar da aiki ko sana'a a yayin da ake ilimantar da matasa. A bawa kowane yaro ko yarinya tun suna ƙanana zaɓin me suke sha'awar koyo, yi ko iyawa.

2. A samu wani ƙwararre ko ƙwararriya a dora musu nauyin koyar da yaro ko yarinya wannan aiki ko sana'a har sai ya ko ta iya shi sosai da sosai sannan a bada shaidar hakan wato kwalin satifiket.

3. A bawa matashi ko matashiya damar nuna iyawarsa ko wani sabon salon fahimtarsa wajen gudanar da aiki ko sana'ar da suka koya tun kafin ace sun fita daga hannu malamansu.

4. Dole a koyawa yaran yadda za su nemi a biyasu haƙƙin aikin da suka yi a bisa tafarkin gaskiya da kyautata wato ba kawai a koya musa sana'ar ba a'a a kuma koya musu yadda ake neman kudin aikin a rubuce.

5. Koyar da yin gaskiya a dukkan lamarin waɗannan yara matasa mazansu da matansu abu ne da ya kamata ya samu gurbin zama ko ajin kansa na yin kankankan a muhimmance wajen koya musu aiyuka da sana'o'i.

ɓ. Bacin an tabbatar sun iya aiyuka ko sana'o'in nan toh a dora su akan hidimtawa wani ko wata oga da take cikin al'amari ta koyon salon gudanar da aiki ko sana'a na tsawon shekara biyu (2) cir kafin su kafa tasu kafar.

7. A koyar da su haka kuma a basu ƙwarin gwuiwa wajen kafa tasu masana'antar wato in mutum ba zai iya yi shi kaɗai ko ita kaɗai ba toh su nemi waɗanda tasu ta zo ɗaya su kafa kamfanin tare.

8. A tabbatar an koya musu yin aikinsu bisa sahihanci ba tare da ha'inci, ƙwange ko tauye mudu ba. Kuma ya zama daidai da yadda za a same shi da kyau da karƙo kamar na ko'ina a faɗin duniya (International Quality & Standard)

9. In matasan nan sun gudanar da aikinsu kuma komai ya ji toh a biya su haƙƙin su ba tare da jinkiri ko b'ata lokaci ba kamar yadda Manzo SAWS ya yi umarni wato kafin gumin goshinsu ya bushe. $annan kar tsintsinka musu kudinsu don kyashi da bakin cikin sun samu.

10. Daga ƙarshe dole hukuma ta tabbatar ba a zalunci mai gaskiya ba daga masu sana'ar har waɗanda suka ba su aikin. Duk inda aka samu matsala a nemi sulhu a daidaita tsakani kowa ya yi abinda ya dace a dora tafiyar cikin yarda da amincewa juna.

Toh in har matasan nan suka tabbatar da samun kudin shiga na halal kuma a bisa tafarkin ci da guminsu ba tare da an zalunce su ba a yayin da aka gina su akan tsoron Allaah da tsayuwa ran lahira a gabanSa zai yi wahala su zaɓi yin aiyukan tir da ashsha.

Don haka dole ne al'uma baki ɗaya daga Gwamnati har zuwa magidanta da daidaikunmu y'an unguwa da maƙwabta a koma a sake lale ta yadda kowa zai san cewa in dai zai nemi halal toh in sha Allaah zai sameta kuma ta ishe shi komai tabbas ita zai zaɓa ba cutar da kai ko cutar da wasu ba.

Wannan rubutu mallaki ne na Tijjani M. M. (2022)

Post a Comment

0 Comments