Matakai 10 Na Tarbiyantar Da 'YA MACE

 Abubuwa gome (10) da iyaye ya kamata su mayar da hankali kansu domin tarbiyantar da 'ya'ya mata.

Tarbiyyar 'Ya Mace
Daga
Tsangayar Malam Tonga 

Yi wa diya mace tarbiya ba ɗaya yake da yiwa ɗa namiji ba. Ita ɗiya mace tana bukatar matukar kulawa na musamman saboda yadda Allah Ya tsara rayuwarta.

Yiwa 'ya mace tarbiya na gari shine sirrin samun zaman lafiyan kowace al'uma. Duk iyayen da Allah Ya albarkace su da haihuwar 'ya'ya mata ba karamin daukaka da gata ya musu. Ba ma ku haifa ba, kuma rike su har su girma a karkashin kulawar ku, babban nasara ne.

Ga wasu hanyoyin yiwa 'ya'ya cikin sauki a zamance:

1: Koyar Da su Addini: Daura diya mace akan koyarwar addini abu ne da yake da mahimmanci fiye da koyar da diya maza.

Ganin yadda kashi 60 na kula da tarbiyartar da 'ya'ya yana hannun mata, samar mata da illimi musamman na addini zai taimaka mata wajen zaman aurenta.

Kamin ta yi auren cusa mata addini a zuciya zai hanata aikata duk wasu abubuwan da Allah Ya haramta tare da kula da abunda Allah Yake so a masa.

Idan zaku yiwa diya mace tarbiya na addini ku mai da hankali wajen tsoratar da ita da azabar da Allah Ya tanadar musamman akan namiji ya taɓa jikinta, yin karya da gulma.

Yara sun fi damuwa da tsoron su shiga wutar Allah a kan kwaɗayin shiga Aljanna. Shi ya sa yara suke kaucewa abunda aka sanar da su zai iya kai su wuta fiye da yin abubuwan da zai shigar da su Aljanna.

2: Kiyaye Bukatunta: Ita diya mace ba a sakar mata hidimominta da kanta. Dole ne iyayen da suke burin yiwa yarsu mace tarbiya na gari, su tabbatar da suna kula da duk wasu matsalolinta.

Daga lokacin da ta soma al'ada iyaye su tabbatar suke tanadar mata kunzugu, sutura, kayan kwalliya da tabbatar da cewa ba a barinta da yunwa.

Kada ka dauka tun da yarka tana jami'a yanzu ba kai zaka kula da ita ba. Muddin dai ba aureta ka yi ba, duk wani abunda kasan zata bukata ba sai kun jira ta nema ba. Gaza yiwa 'ya'yanmu mata irin wadannan abubuwan yake baiwa wasu mazan damar yaudaransu akan kudin da zasu sayi auduga sai ta bada kanta.

3: Kada Ku Saba Bata Kuɗi: A kula da buƙatun ɗiya mace musamman mai karancin shekaru kada a saba bata kuɗi. A tanadar mata abunda take so yafi dacewa da bata kuɗi a hannunta domin sayen abunda take buƙata. Amma idan mace ce wacce ta mallaki hankalin kanta hakan ya zama wajibi domin gudun kada kwaɗayin kuɗi ya jefata tarkon maza.

4: Ku Guji Yi Mata Duk Abunda Take So: Kada ku sabawa 'yarku mace da yi mata duk abunda ta buƙata daga gareku. Ku nuna mata akwai wadata kuma akwai rashi. Ku karantar da ita ba koyaushe mutum yake samun abunda yake buƙata ba.

Saboda nan gaba idan tayi aure zata fahimci babu da kyau.

5: Yi Mata Horo: Bama ɗiya mace , ko da namiji masana tarbiya sun yi hani akan yawan dukan yaro. Don haka ita ɗiya mace kada a saba mata da duka a matsayin horo.

Akwai hanyoyi da dama na horon ya mace idan tana karama ku hanata yin abunda take sha'awar yi a matsayin horon laifin data yi. Ko a sayawa 'yan uwanta kayan kwalamar da suke so ita a ki bata a hana kowa ya bata. Haka barazana na dukan yaro yafi yin dukan tasiri.

Idan kuma macece babba. Nuna mata matukar bacin ranku akan laifin datayi shi ya dace. Tare da nuna mata hadarin da zata iya fuskanta muddin tana bakanta muku rai. Dakatar da ita ga wasu abubuwan da ta saba yi ko take yi shi ma hanya ce ta horon diya mace.

6: Karfafa Mata Gwaiwa: 'Yaya mata sunfi 'ya'ya maza kaifin basira, sai su mata basu cika samun goyon bayan iyayensu ba a wasu lokutan ko dai saboda dalilai na addini ko kuma na al'ada.

Idan kun fahimci abunda diyarku mace take burin cimma a rayuwarta wanda bai kaucewa addininku ko al'adar ku ba. Ku karfafa mata gwaiwar cimma wannan burin nata. Idan kuma abunda ta zaban akwai matsala, cikin natsuwa da fahintar da ita zaku mata bayani tare da kawo mata wasu a madadin abunda take son yin.

7: Kada A Barta Ita Kadai Tana Kwana: Wasu iyayen suna da dabi'ar warewa diyansu mata wajen kwana su kai. Hakan yanada kyau idan bazawara kuka ajiye a gida. Amma muddin macece wacce bata taba aure ba komin yawan shekarunta ta zauna daki daya da kannenta mata ko yayyunta yafi, idan kuma batadasu to sai ta zauna ita da mahaifiyarta idan masu wadatar makwancine da maigidan yake da turakan kansa.

Hakan na iya rage wasu tabara da 'ya'ya mata suke tafkawa da samarinsu ta waya idan dare ya tsala. Hakan kuma zai baiwa uwa daman fahimtar 'yar tasu sosai cikin hikima.

8: Ku Zaba Mata Kawaye: Duk iyayen da suke zabawa 'ya'yansu mata kawayen da zasu yi mu'amala dasu, ana iya samun saukin wajen yadda kawaye ke iya watsar da tarbiyan da iyaye suke yiwa diyarsu mace.

Hatta wannan iskancin na Besty ba za a taba samunsa ga yaran mata masu tarbiya ba. Don haka yana da kyau iyaye su kula da kawayen da yayansu suke mu'amala dasu tun daga yarintarsu har girmansu. Da zaran kun ganta da wacce hankalinku bai kwanta ba, taka mata burki da hulda da ita.

9: Binciken Abunda Ke Cikin Wayoyinta: Ba gata bane a sayawa diya mace waya mai tsada idan tanada karancin shekaru. Idan kuma ta girma ko an saya mata ne saboda karatu. Ya zama wajibi musamman ga iyayensu mata su rika kula da abubuwan dake cikin wayoyin 'ya'yansu mata.

Yana da kyau uwa ana zaune kawai tace ta miko mata wayarta. Ta kuma bi wayar sannu a hankali domin gano irin hiran da take yi, da kuma irin bidiyo ko hotunan da take ajiye dasu a wayoyinta.

Muddin yarki ta fahimci kina iya binciken wayanta ako wani lokaci, zata rika kiyayewa.

Wayoyin hannu suna taimakawa wajen gurbata tarbiyan da iyaye suke kokarin yiwa yaransu. Don haka duk yawan shekarun diyarku mace muddin bata taba yin aure ba, kada ku bata damar yin abunda taga dama da wayarta.

10: Zaɓa Mata Makaranta: Ku zabawa diyarku makarantar da zata nemi Illimi musamman na addini yanada mahimmanci kwarai da gaske.

Dole ne iyaye su fahimci tarbiyar da masu makarantun da malaman makarantun suke da shi. Wacce irin akida suke koyarwa akai. Gano wadannan kamin ku saka 'yarku inda zata samu karatun addini yanada matukar amfani. Domin idan har aka samu gurbatattun malaman addinin da zasu iya lalatawa yara tarbiya, sai sunyi illa fiye da Malamai na boko masu lalata Yara.

Waɗannan wasu daga cikin dubannin hanyoyin da za a iya yiwa 'ya'ya mata tarbiya na gari a zamanance. Da fatan Allah Ya taimaka mana wajen yiwa yaranmu tarbiyan tsoronSa da bauta masa.

SHARE 🔔

Post a Comment

0 Comments