Da wuya a ce akwai wani Bahaushe kuma mazaunin ƙasar Hausa da bai taɓa jin ko da ɗuriyar waƙar Jaruma ta Makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) ba. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya feɗe wannan waƙa domin manazarta.
MATANIN WAƘAR JARUMAR MATA TA MAKAƊI HAMISU BREAKER
Daga
Prof. Sa'idu Muhammd Gusau
Bayero University, Kano
Makaɗi: Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker)
Waƙar: Jarumar Mata
1. Jagora:
Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciyata ba,
: Komai ruwa da iska a kan ki ba za na daina
kewa ba,
: Idan na samu zarrar samun ki ba za na tanka
kowa ba,
: Ni ban ga mai harara ba, bare na waiwaya
ba.
2. Jagora: In
dai a kanki ne za na jure wahalar zuwa garin nisa,
: Da an taɓa ki a
jira ni don ko tilas na zo na ɗau fansa,
: Jimirin Jiranki nai don ki zo na kalle ki
gimbiyar Hausa,
: Sirri na rayuwata ke ce kawai da kin kira
da na amsa.
3. Jagora:
Zuma a baki daɗi gare ta
kin ba ni taki na lasa,
: In dai a kanki ne na yi nisa,
: Don ba kiran da zan amsa.
4. Jagora:
Tilas ganin mu tilas barinmu,
: Ƙaunarki
tun da nai nisa,
: Sam ba batun na fasa ko za a ce mun in ba da
rai fansa.
5. Jagora:
Tsarin zubin ki daidai ne,
: Ya kama zuciyata ne,
: Ina ji kamar mafarki ne,
: Ina son ki so mataki ne.
6. Jagora: Ni
ban da damuwa in har zan buɗe ‘yan idanuna,
: In kalle ki ga ki dab da ni,
: To me za ya dami ƙalbina.
7. Jagora:
Yau za na yo amo,
: Tun da na gane kina da tausaina,
: Dan yanzu na zamo ya mafatauci mai
biɗar gurin
kwana.
8. Jagora: Na
ƙwallo shela dan sanar da iya maƙiya
kalamaina,
: Daga zuciya nake kwatanta ina zayyano
jawabaina.
9. Jagora:
Idan babu ke ina ne zan saka zuciya ta bar yawan ƙuna,
: Kowa da nasa amma ni ke ce cikar muradaina.
10. Jagora:
Yau ga ni a ruwa kusa da kada,
: Zo ki ceci ƙarkona,
: Komai da maffuta kar da ki saba da farta ban kwana.
11. Jagora:
Ina ji ina gani yadda nake son ki ya fi ƙarfina,
: Na san a duniya da wanda yake janye duk
tunanina.
12. Jagora:
Soyayya rayuwa wani sa’in sai ta zama wutar ƙuna,
: Duk wanda ke cikinta shi ne jurau amma fa a
gurina.
13. Jagora: So
na faranta rai da ruhi ya sa ka zam kamar Sarki,
: Kuma rayuwa da so misali ne yana kama a mafarki.
14. Jagora:
Samari mu yi hakuri idan har mun sami so mu sa sauƙi,
: ‘Yanmata mui hakuri idan har mun sami so mu
sa sauƙi.
15. Jagora:
Masoyi yana da rana ne,
: Masoyi yana da rana ne,
Jagora: Masoyi yana da rana ne.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.