Ticker

Amaryar Ango

 Wata amaryar sati biyu ce, bayan fitar ango da awa biyu, ta kira shi tana kuka wai ya zo gida, a guje ango na tuntuɓe ya baro kasuwa, shagon ma maƙwabcinsa ya barwa. Yana zuwa gida ya gan ta a kitchen cikin mamaki ya ce "lafiya kika kira kina kuka kuma na ganki a kitchen? "

 Amarya ta ɗan yi farrrrr da ido, ta goge hawaye, ta dan karkace ta turo baki cikin shagwaɓa ta ce "Baby maggi za ka ɓare min, na yi na yi sun ƙi ɓaruwa, hannu na da maiƙo."  

Yanzu dai an ce ya kumbura bakin amarya dalilin marin da ya kai mata, ashe ba mijin novel ba ne shi😡, 'yan mata a riƙa kula😥

Post a Comment

0 Comments