𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assslamu alaikum, Malm ko akwai wata magani da zan sha don daina sha'awa ko rageta, wllh ina da matsaninciyar sha'awa wanda ko da yaushe inna ciikinta shi ne nake tsoron faɗawa halaka, don Allah a taimaka ni budurwa ce.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa'alaikumussalamu. Toh da farko dai lallai ki Kamewa daka gane-gane domin
kallace-kallacen wasu abubuwa da hotunan tsiraici masu motsi sha'awa yana kai
mutum zuwa haram. Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa ki ji tsoron
Allah ki daina. Ki yawaita yin azumi Ki daina hirar batsa da maza ko mata
yan'uwanki.
Hanyoyin rage tsananin shaawa ga maza ko mata ⤵
Hanyar da za a rage tsananin sha'awa ga wadanda ALLAH
madaukakin sarki yajarabce shi da Ita.
1. Shan ruwa mai sanyi makwalwa dai-dai.
2. Za a samo kuzbara busassa wanda aka yi garinta
kwatankwacin karamin cokali sai azuba aruwan mai sanyi da yamma har zuwa asuba
sai asanya sukari a sha, Insha ALLAH yana saukaka tsananin sha'awa ga namiji ko
mace. Amma idan akwai hali yin Aure yafi, idan kuma mace ɗaya gareka ka kara su zama
biyu, idan biyu ne kanada hali kara ta uku, idan ukune kanada hali to kakara ta
huɗu, domin karika samun cikakkiyar gamsuwa, Ubangiji Allah ya
sa mu dace Ameen.
.
3. Za a samo wani haki da'ake cemasa Arrajla sai arika
tafasawa ana shan sa shi ma yana saukaka tsananin sha'awa ga maza ko mata, za
ki iya samun sa amma sai dai a Kano.
4. Ko kuma ka samo zait Kafuur sai arika diga ɗan kaɗan a cikin kofin shayi suka
ce idan ana shan wannan yana kashe tsananin wutar sha'awa...... Amma lallai
idan da hali yin aure yafi... Ko kuma yin Kari ga maza!!!
5. Ko kuma a samo Yansun da kako sai arika tafasawa ana
sha, shi ma yana saukaka tsananin sha'awa.
6. Ko a samo kwayoyin Salak Irin wanda masu lambu suke
shukawa yafito sannan su dasa shi yagirma ya zama Salak, to wannan kwayoyin
da'ake yafawa su za ki samo sai kirika tafasawa kina sha suka ce wannan hanya
yana yanke tsananin sha'awa gaba ɗaya, sannan wanda yake fama
da yawan mafalakai ko da yaushe amma da wannan hanyar za a iya samun waraka.
Ubangiji Allah yabamu dacewa, masu yawan yimana
tambaya a kan yadda za su rage tsananin sha'awa ga hanya...... Lallai ga wanda
yake da tsananin sha'awa ko bashida da mata.. ko ba ta da miji, kuma babu halin yin Aure to
amaimakon yin Istiminai (musterbution) to kwara bin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin domin asami
sauki!!!
Allah ta'ala ya sa mu dace
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DTrJJCF04ƘpACEtA7hyu4R
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.