Ticker

    Loading......

Hausar Rukunin Masu Sana’ar Waya A Garin Gusau

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsuna da Al'adu, Jami'ar Tarayya Gusau.

Wayoyin Hannu


Hausar Rukunin Masu Sana’ar Waya A Garin Gusau

Na

ABDURRAHMAN TUKUR 

SADAUKARWA

      Ni Abdurrahman Tukur na sadaukar da wannan kundin bincike, mai taken ‘’Rukunin Hausar Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau’’ ga mahaifana musamman marigayi Alhaji Tukur Ibrahim Barmo kotorkoshi, da mahaifiyata Hajiya Raliya Usman Na’iya kurah kotorkoshi da ƙanen mahaifina marigayi Aminu Usman kotorkoshi, da matarsa Mama Sa’adatu Bello Zauro a bisa ɗawainiyarsu a gare ni tun ina ciki har ya zuwa wannan lokaci. 

   Haka kuma, na sadaukar da wannan bincike zuwa ga ƙanwata marigayiya Aisha Tukur Ibrahim Barmo da kakanni na mal. Ibrahim Barmo, da Mal Usman Na’iya ƙofai bai kotorkoshi da kuma marigayi ɗa na Ahmad Abdurrahman Tukur da fatar Allah ya gafarta maku gabaɗaya. Hakazalika, na sadaukar da wannan bincike zuwa ga ƙanne na maza da mata musamman IbrahimTukur, Ni’imatu, Safina, Idris, Madina da kuma matata Nusaiba Ismail Mafara da ‘yayanmu Ahmad da Alamin da kuma  sauran yan uwana, da abokanai.

     A ƙarshe, na sadaukar wa malamai na na islamiyya da makarantar boko tun daga matakin firamare, da sakandare, da kwalejin Ilimi har zuwa wannan Jami’a mai albarka da wannan kundin bincike musamman malamanmu na wannan sashe mai albarka.

 

GODIYA

   Yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki a kan ni’imominsa da ya yi a gare mu na bayyane da kuma na ɓoye. Tsira da aminci su ƙara dauwama da tabbata ga shuganmu annabi Muhammadu (S.A.W) farin jakada da alayensa da sahabbansa da mabiyansa masu nagarta har zuwa ranar sakamako.

   Bayan haka, haƙiƙa aikin bincike aiki ne, wanda yake da matuƙar wahala a ce mutum ya kammala shi ba tare da taimakon wasu mutane ba. Saboda haka, ya zama dole  in miƙa godiyata ga dukkan waɗanda suka ba ni gudunmuwar ganin wannan aiki ya cimma nasarar kammalarsa.

  Hausawa kan ce, ‘’Tushiya mafarin dawa’’, tilas ne in miƙa godiya ta ga mahaifana a bisa ɗawainiyar da suka yi  a kaina musamman don ganin na samu ilimi tare da addu’o’insu na fatar alheri a gare ni tun daga haihuwa har ya zuwa wannan rana .

    Hausawa na cewa, ‘’ Daga wawa sai mahaukaci ke mance mafari’’. Saboda haka, ya zama tilas in miƙa cikakkiyar godiya maras adadi tare da jinjina da yabo ga malamina  tun daga aji biyu, uku har ya zuwa aji huɗu a wannan Jami’a wato Malam Isah Sarkin Fada a bisa juriyar duba wannan aiki tun daga farkonsa har zuwa kammaluwarsa, tare da gyara da shawarwari da kuma nasihohi irn na ɗa da mahaifi domin ganin wannan bincike haƙarsa ta cimma ruwa. Bugu da ƙari, ina roƙon Allah mai ƙarfi, girma da buwaya da ya ƙara ɗaukaka da shekaru masu albarka. Haka kuma, ina miƙa godiya ta zuwa ga shugaban wannan sashe mai albarka wato Dr. Adamu Rabi'u Bakura bisa ga damar da aka

iv.

ba ni na zama ɗaya daga cikin ɗaliban da aka bai wa damar karatu a

wannan sashe mai albarka tare da ganin mun samu ingantaccen ilimi a wannan sashen.

  Hakazalika, ina miƙa godiya ta ga hukumar wannan jami'a da fatar alheri a gare su bakiɗaya bisa ga damar da ta ba ni domin zama ɗaya daga cikin ɗaliban wannan makaranta mai albarka. Nagode Allah ya saka masu da alheri.

   Har ila yau, ya zama dole in miƙa godiyata tare da jinjina da fatar alherai zuwa ga ɗaukacin malamanmu na wannan sashe mai albarka gabaɗaya waɗanda, da bazarsu ce muka taka rawa  har muka samu abin da muka samu na ilimi a wannan sashe, ta hanyar karantarwarsu da shawarwari da nasihohinsu daban-daban a gare mu. Ina maku fatar alheri har kullum Allah maɗaukakin sarki ya saka maku da mafificin alherinsa. Amin

  Saboda ajizanci na ɗan’adam, ina ba da haƙuri ga duk wanda ba a ambaci sunansa ba a wannan fage, ya yi haƙuri don Allah!!!

TSAKURE

A duk lokacin da aka samu waɗansu mutane sun keɓe kansu a wani muhalli na daban, a kan samu wanzuwar wasu maganganu waɗanda suka keɓanta ga waɗannan mutane kaɗai. Saboda haka ne, aka gudanar da wannan bincike a farfajiyar garin Gusau domin nazartar Hausar masu sana’ar waya.

  Wannan kundin bincike mai taken Rukunin Hausar Masu Sana'ar a Garin Gusau, bincike ne da ya binciko tarihin garin Gusau da sana’o’in Hausawa, da rabe-raben su da kuma muhimmancin sana’o’in. Haka kuma, an yi bayanin ma’anar sadarwa, da rabe-rabenta da kuma muhimmancin ta.

Hakazalika, an yi tsokaci a kan masu sana’ar waya a Gusau  tare da bayyana ma’anar wayar salula, da samuwarta, da amfanin ta da kuma illolin ta. Har ila yau, an bayyana ire-iren wayoyi da ayyukansu  tare da  bayanin yadda ayyukan wayoyin wani rukuni suka bambanta da na wani rukuni.

    Bugu da ƙari, an yi bayanin wuraren da ake sayar da waya a Gusau da, da kuma yanzu. Bayan haka, an rattabo misalan sunayen da ake yi wa wayoyi na Hausa, da sunayen kuɗi a kasuwannin waya a Gusau. Bugu da ƙari, an rattabo misalan kalmomi da kuma jimlolin da  masu sana'ar waya kan yi amfani da su ta amfani da sunayen  'yanƙwallo musamman Turawa ta hanyar yin amfani da lambar jesin 'yanwasa daban-daban. A ƙarshe kuma, aka bayyana sakamakon wannan bincike da shawarwari da kuma manazarta. Idan aka nutsa sosai da sosai a cikin wannan kundin, za a ga yadda aka rattabo waɗannan bayanai daki-daki.

 

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0. SHIMFIƊA

Wannan aiki mai taken "Rukunin Hausar Masu Sana'ar Waya a Gusau", bincike ne da ya binciko yadda al'ummar garin Gusau musamman masu sana'ar waya ke yin Hausarsu a wurin kasuwancinsu na sayar da waya a kasuwanni daban-daban a cikin garin Gusau da kewayensa.

   Wannan babi shi ne fitila wanda ya haskaka dukkan abin da ya wakana a cikin wannan bincike, domin shi ne ke ɗauke da dukkan tubalan ginin wannan aikin. Domin samun sauƙin gudanar da wannan aiki, an kasa shi zuwa babi-babi.

   A babi na ɗaya, an tattauna abubuwa da dama kama daga; manufar bincike da kuma hasashen bincike. Bugu da ƙari, an yi tsokaci a kan farfajiyar bincike, da kuma matsalolin bincike. Haka kuma, an duba muhimmancin bincike da kuma hanyoyin da aka bi domin gudanar da wannan bicike, daga ƙarshe kuma aka ɗan yi bayanin naɗewa.

   Yayin da a babi na biyu kuma, an yi tsokaci ne a kan abubuwa da dama waɗanda suka shafi bitar ayyukan da suka gabata. A ƙarƙashin bitar ayyukan da suka gabata, an yi tsokaci a kan abubuwa da dama, kama daga; duba bugaggun littattafai da kundayen bincike da kuma maƙalu da mujallu waɗanda hannu ya kai gare su. Daga ƙarshe kuma, an yi bayani a kan hujjar ci gaba da bincike da kuma bayanin naɗewa.

   A babi na uku kuma, an yi taƙaitaccen bayani a kan tarihin Gusau ta Sambo, da  ma'anar sana'a, da rabe-raben sana'a da kuma muhimmancin sana'a. Haka kuma, an yi tsokaci a kan ma'anar sadarwa, da rabe-raben sadarwa. Bugu da ƙari, an bayyana ma'anar waya tare da tarihin samuwarta. Daga ƙarshe kuma, an kalli amfanin wayar salula da illolin wayar salula a cikin garin Gusau da kewaye.

  A babi na huɗu kuma, an yi tsokaci a kan wuraren da ake sayar da waya a Gusau, da wuraren da aka fara sayar da waya a Gusau can da, da kuma wuraren da ake sayar da waya  Gusau a yanzu. Bugu da ƙari, an duba masu sana'ar waya a Gusau da ire-iren wayoyi, kama daga anduroyid da kifad da kuma simbiyan. Haka kuma, an tsakalo sunayen da ake yi wa wayoyi wato ( Bahaushen suna) da kuma sunayen da ake yi wa kuɗi a kasuwannin waya a Gusau. Daga ƙarshe kuma, an duba kalmomi da kuma jimlolin da masu sana'ar waya kan yi amfani da su wajen gudanar da cinikayya tsakaninsu a kasuwanni daban-daban a cikin birnin Gusau da kewaye.

  A babi na biyar wato babi na ƙarshe, an yi bayanin sakamakon bincike, da  shawarwari da kuma jawabin naɗewa da kuma manazarta.

1.1 MANUFAR BINCIKE

Manufar yin wannan bincike ita ce a yi ƙoƙarin fito da abubuwa da dama domin a nuna wa al'umma wani abu sabo wanda ba a sani ba, ko kuma an san shi amma ba a fito da shi ba a fagen ilimi, domin a ƙara samun haske da fahimta a ilmance.

   Bugu da ƙari, daga cikin manufar wannan bincike akwai fito wa al'umma da Hausar masu sana'ar waya a sarari, da sunayen wayoyi, da jimloli da kuma sunayen da masu sana'ar waya kan yi wa kuɗaɗe (keɓaɓɓun sunaye) musamman a wajen cinikin waya tsakaninsu.

 

1.2. HASASHEN BINCIKE

  Idan an kawo ƙarshen wannan binciken, ana hasashen cewa binciken zai zaƙulo ko ya fito da Hausar masu sanaar waya a sarari a ɓangaren mahangar harshe da nazarin walwalar harshe. Bugu da ƙari, binciken zai bayyana kalmomin fannu waɗanda masu sana’ar waya kan yi amfani da su wajen cinikayya tsakaninsu da kuma wasunsu musamman masu saya domin yin amfani da waya. Bayan haka, ana hasashen cewa aikin zai iya zama abin nazari ga masu bincike game da harshe musamman a ɓangaren abin da ya shafi Hausar rukuni ko ilimin walwalar harshe.

    Hakazalika, ana hasashen cewa, wannan bincike zai kawo ci gaba wajen ƙarin bunƙasa harshen Hausa da kuma yaɗuwarsa. Haka kuma, wannan binciken ana hasashen zai iya zama fitilar da za ta haskawa wasu manazarta domin cike wani giɓi ko gurbin da ba a cike ba a ɓangaren nazarin Hausar rukuni da ilimin walwalar harshe na wani bincike wanda zai taso nan gaba.

1.3. FARFAJIYAR  BINCIKE.

Wannan aiki an gudanar da shi ne a fannin harshe. Haka kuma, ko a ɓangaren harshe ya shafi ɓangaren ilimin walwalar harshe wato (socio-linguistics). Bugu da ƙari, an keɓence wannan binciken a farfajiyar garin Gusau musamman kasuwanni da wurare daban-daban waɗanda ake sayar da waya. Bayan haka kuma, binciken zai kalli sunaye, da kalmomi da kuma jimloli da waɗansu abubuwa masu  muhimmancin gaske waɗanda masu sana'ar waya kan yi amfani da su a wurin Hausarsu waɗanda suke aiwatarwa ko suke gudanar da su a magance ko kuma a aikace a cikin farfajiyar garin Gusau da kewayenta.

 

1.4. MATSALOLIN BINCIKE

A kowane irin al’amari na rayuwa wanda aka samu nasarori bayan an aiwatar ko kuma bayan an gudanar da shi musamman a lokacin da ake yin sa, to lallai ana iya fuskantar ƙalubale da wasu yan matsaloli. Don haka, a yayin aiwatar da wannan binciken an haɗu da wasu 'yan matsaloli. Kaɗan daga cikinsu akwai:

1. An samu cikas wajen tambayoyi ga masu sana’ar waya domin sau da yawa a kan yi wa masu sana’ar waya tambayoyi, amma wasun su ba su son amsawa. Saboda haka, an ɗan samu cikas wajen samun bayanai.

2. An samu rashin littattafai wadatattu da maƙalu da kuma kundayen bincike waɗanda suka yi magana kai tsaye a kan Hausar masu sana’ar waya na wani gari, wannan ya haifar da wahalhalu wurin samun bayanai.

 3. Bugu da ƙari, an samu cikas wajen zirga-zirga ta yau-da-kullum saboda wannan annoba ta sarƙewar numfashi ( covid19) da ta addabi duniya gabaɗaya. Haƙiƙa wannan ya ƙara samar da matsaloli da wahalhalu wajen gudanar da wannan bincike.

A taƙaice dai, waɗannan su ne kaɗan daga cikin matsalolin da aka samu a yayin gudanar da wannan bincike.

1.5. MUHIMMANCIN BINCIKE.

Kamar yadda muka sani cewa duk abin da mutum zai yi to, tabbas yana da muhimmanci ƙwarai da gaske ga mai yin sa. Alal haƙiƙa wannan bincike yana da muhimmancin gaske a fagen ilimi da kuma nazari musamman ga manazarta da ɗalibai masu karatu da nazarin harshen Hausa. A taƙaice dai, babban muhimmancin wannan bincike shi ne samar da bayanai nagartattu kuma ingantattu a kan Hausar masu sana'ar waya da kuma bayyana wannan Hausar da masu sanaar suka samar wa harshen Hausa. Hakazalika, an bayyana irin rawar da sana'ar ke takawa a wajen samar da aikin yi ga matasan Hausawa da kuma magidanta tare da rage wa matasan raɗaɗin talauci a cikin al'umma da kuma samun abin dogaro da kai.

   Sana'ar waya na sahun gaba a cikin jerin gwanon manya-manyan sana'o'in da Hausawa ke bugun-gaba da su a wannan ƙarni. Sana'ar tana bayar da gagarumar gudunmuwa wajen bunƙasa sana'o'in zamani da kuma bunƙasar tattalin arzikin al'ummar Hausawa. Hakazalika, masu sana'ar waya sun sa harshen Hausa ya ƙara yaɗuwa da bunƙasa ta hanyar samar da sababbin kalmomi da sunaye da kuma jimloli a yayin gudanar da kasuwancinsu. Wannan yaɗuwar ce ta sa har an fara saka harshen Hausa a cikin jerin gwanon harsunan wasu wayoyi, da shafunkan sada zumunta wato (social media plattforms). Abin nufi a nan shi ne, a halin yanzu mutum zai iya zaɓar harshe Hausa a matsayin harshen da mutum zai yi amfani da shi a kan ƙwaƙwalwar wayarsa a wasu shafukan sada zumunta. Alal misali, shafin sadar da zumunta na Facebook da sauransu. Wannan kuma, ba ƙaramin ci gaba ne ba ga kowane irin harshe na duniya.

1.6.  HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE.

Hanyoyin gudanar da bincike hanyoyi ne daban-daban da manazarci ko mai aikin bincike ke bi domin samun bayanai waɗanda suka dace da abin da yake nazari a kai.

  Hanyoyin da manazarci ko manazarta ke bi domin samun bayanai suna da yawa. A yayin gudanar da wannan binciken an bi hanyoyi da dama domin samun nagartattun bayanai. Waɗannan hanyoyi kuwa sun haɗa da;

i. Duba bugaggun littattafai.

ii. Duba kundayen bincike.

iii. Duba mujallu da muƙalu masu alaƙa da wannan bincike waɗanda hannu ya kai gare su.

  Bugu da ƙari, an yi fira ko tattaunawa da wasu mutane musamman masu sana'ar waya a garin Gusau kama daga tsofaffin yan kasuwa da sababbi da kuma wasu shuwagabannin masu sana'ar a Gusau domin tattaro bayanai ingantattu masu nagarta da armashi.

1.7. NAƊEWA

Kamar yadda bayani ya gabata a wannan babi, an yi tsokaci a kan wasu muhimman abubuwa da dama kama daga manufar bincike da hasashen bicike da farfajiyar bincike da kuma matsalolin bincike. Bugu da ƙari, an yi tsokaci a kan muhimmancin bincike da kuma bayani a kan hanyoyin da aka bi domin gudanar da wannan bincike.

 

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0. SHIMFIƊA

A wannan babin , wato babi na biyu an yi tsokaci ne a kan bitar ayyukan da suka gabata waɗanda masana da manazarta da dama suka gudanar a shekaru daban-daban. Bugu da ƙari, a ƙarƙashin bitar ayyukan da suka gabata, an tattauna a kan abubuwa biyu zuwa uku waɗanda suka haɗa da; duba bugaggun littattafai da kundayen bincike da kuma maƙalu waɗanda hannu ya kai gare su. Bugu da ƙari, wannan babi zai ƙara haska mana fitila a kan wannan bincike da ake aiwatarwa.

2.1. BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA.

Masana da manazarta da dama sun yi ƙoƙari ainun wajen samar da ayyuka daban-daban a ɓangaren Hausa kama daga ɓangaren harshe, da ɓangaren da ya shafi adabi, da kuma ɓangaren da ya shafi al’ada. Sobada haka, an samu sauƙi wajen bitar ayyukan da suka gabata domin cimma gaci a yayin aiwatar da wannan bincike.

Masana da manazarta da kuma marubuta da dama sun yi ayyuka da dama waɗanda suka shafi sana'o'in Hausawa na gargajiya da ma na zamani. Wannan dalilin ne yasa kafin a aza tubulan ginin wannan aiki aka ɗan yi ƙoƙarin bitar wasu daga cikin ayyukan da suka gabaci wannan kundin bincike masu dangantaka ko alaƙa da wannan aiki gwargwadon abin da hannu ya kai gare shi. Dalili a nan shi ne, saboda a bambance wuraren da binciken ya yi musharaka da wasu ayyukan da kuma inda suka bambanta da junansu.

  A yayin gudanar da wannan bincike, an duba ayyuka da dama waɗanda suka haɗa da; bugaggun littattafai, da kundayen bincike da kuma makalu da  makamantansu. Don haka, daga cikin ayyukan da hannu ya kai gare su akwai;

2.1.1. BUGAGGUN LITTATTAFAI.

Akwai wallafaffu ko bugaggun littattafai da dama masu alaƙa da wannan bincike. Daga cikin wallafaffun littattafan akwai;

  Alhassan, da wasu (1982) a cikin littafinsu mai suna ‘’ Zaman Hausawa’’. Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo wasu sanaoin Hausawa waɗanda suka haɗa da: noma, da ƙira da fawa da farauta da kiwo da saƙa da kaɗi da sauransu.

Aikinsu yana da alaƙa da wannan bincike, domin ya shafi sanaoin Hausawa na gargajiya. Abin da ya bambanta su shi ne, sun yi aikinsu ne a kan sanaoin Hausawa na gargajiya gabaɗaya. Wannan bincike kuma, ya shafi sana’o’in Hausawa na zamani kuma ya keɓanta ne a kan Hausar Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau.

  Salihi (2012) a cikin littafinsa mai suna "Sakace A kan karin Harshen Hausa", marubucin littafin ya rubuta abubuwa da dama, inda ya yi bayani a kan ma'anar harshe da ma'anar karin harshe, da bambanci tsakanin harshe da karin harshe.   Haka kuma ya tattauna a kan matakan da ake bi wajen fito da bambancin harshe da karin harshe da dai sauransu.

   Bugu da ƙari, a cikin littafin ya yi magana a kan tsarin matsayi a cikin al'ummar Hausawa, karin harshen zamantakewa ko matsayi, da kare-karen harshe na matsayi na sana'a wanda a nan ne ya kawo ire-iren Hausar masu sana'a kamar haka;

1. Hausar masu gyaran Wayar Salula.         

2. Hausar Mahauta.

3. Hausar masu Gurasa.

4. Hausar ‘Yan Karta.      

5. Hausar Ɗalibai.

6. Hausar ‘Yan tasha.

7. Hausar ‘Yan caca.       

8. Hausar Maƙera. 

9. Hausar ‘Yan sanda.

10. Hausar Teloli.   

11. Hausar Manoma.        

12. Hausar ‘Yan daba, da kuma

13. Hausar Direbobi.

 Salihi, (2012).

   Don haka, wannan littafin yana da alaƙa da wannan bincike domin an yi tsokaci a kan wani yanki na masu sanaar waya (Hausar masu gyran waya).

   Ayyukan suna da alaƙa da juna ta fuskar sanaar waya. Haka kuma, sun bambanta da juna domin a littafin Hausar masu gyaran waya kawai aka yi tsokaci a kai. Bugu da ƙari, ba a bayyana cewa Hausar masu gyaran wayar gari kaza ce ba. Amma, shi wannan binciken an yi shi ne a kan ‘’Hausar Masu Sana’ar Sayar da Waya a Garin Gusau’’ ba Hausar Masu gyaran Waya ba. Kuma wannan binciken ana yin sa ne a farfajiyar garin Gusau kaɗai. Wannan shi ne ya bambanta su.

     Yakasai, (2012) a cikin littafinsa mai suna "Jagoran Ilimin Walwalar Harshe" wanda marubucin ya rubuta a kan babi-babi inda ya rarraba littafin har babuka ashirin (20). A cikin littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan harshe da al'ada, da ma'ana da nau'o'in jinsi. Ya yi magana a kan yanayi da tsarin sadarwa da dai sauransu. A babi na takwas (8) na littafin mai taken "Dangakatar Harshe Da Rukunan Jama'a" marubucin ya yi magana a kan yanayi da tsarin rukunin jama'a, salo cikin dangantakar harshe da rukunin jama'a da harshe. Marubucin ya kawo nau'o'in Hausa kamar haka;

1. Hausar Kasuwanci.

2. Hausar Mawaƙa.

3. Hausar Sarakuna.

4. Hausar Malamai.

5. Hausar Dattijai.

6. Hausar Matan aure.

7. Hausar Gidan Magajiya da makamantansu.

 Yakasai, (2012).

  Saboda haka, wannan littafin yana da alaƙa da wannan bincike. Dalili a nan shi ne, a cikin littafin an yi magana a kan nau'o'in Hausa na wasu rukunan jama'a. Abin da ya bambanta littafin da wannan binciken shi ne, a littafin ba a yi magana ko aka yi bincike a kan Hausar rukunin masu sana'ar waya a garin Gusau ba. Wannan dalilin da ma wasu dalilai suka bayar da damar aiwatar da wannan bincike domin a fito da Hausar masu sana'ar waya na garin Gusau a sarari, kuma a fagen nazari da ilimi.

  East, (1968) a cikin littafinsa mai suna "Labaru na Da da na Yanzu" wanda ya rubuta a kan babuka goma (10). A babi na ɗaya, ya kawo tarihin fitattun sana'o'in Hausawa na gargajiya tare da bayaninsu. Inda a babi na biyu kuma ya bayyana wasu sana'o'in mata na gargajiya. Alaƙar wannan littafin da wannan aikin ita ce, suna da alaƙa ta fuskar sana'o'in Hausawa. East ya yi aiki a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya. Yayin da wannan binciken zai kalli sana'o'in Hausawa na zamani. Bugu da ƙari, an keɓance shi a kan Hausar masu sana'ar waya a garin Gusau kaɗai.

  Gusau, (2012) a littafinsa mai suna " Bukukuwan Hausawa" ya yi nazari ne a kan sana'o'in Hausawa daban-daban kama daga fatauci, gini, noma, wanzanci da sauransu. Wannan littafin yana da alaƙa da wannan binciken ta fuskar sana'o'in Hausawa. Amma kuma duk da haka, suna da bambanci domin a littafin ba a yi magana a kan sana’ar waya ba, balantana ma a yi nazari a kan Hausar masu sana'ar. Haka kuma a littafin, an fi mayar da hankali ne a kan sana'o'in Hausawa na gargajiya. Yayin da wannan aikin an yi shi ne a kan sana'o'in Hausawa na zamani. Haka kuma, an iyakance shi a kan Hausar masu sana'ar waya a garin Gusau kawai.

  Zarruƙ, da wasu (1986) a littafinsu mai suna" Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare, Littafi na Ɗaya". A littafin, marubutan sun yi tsokaci a kan abubuwa da dama. Kaɗan daga cikin abubuwan da suka yi tsokaci a littafin akwai sadarwa. A ƙarƙashin kashi na huɗu babi na takwas, marubutan sun bayyana ma'anar sadarwa, hanyoyin sadarwa ta amfani da gaɓoɓi da hanyoyin sadarwa masu nuna baƙin ciki.

 Bugu da ƙari, sun kawo hanyoyin sadarwa na gargajiya da na zamani. Duk da cewa a cikin hanyoyin sadarwa na zamani sun yi tsokaci a kan tangaraho, talabijin, rediyo da jarida to amma, ba su yi magana sosai a kan wayar salula ba. Babu shakka wannan littafi yana da alaƙa da wannan aikin domin an yi magana a kan sadarwar Hausawa ta zamani. Bambancin dake tsakaninsu shi ne, littafin ya yi magana a kan sadarwar Hausawa na gargajiya da na zamani gabaɗaya. Shi kuma wannan bincike ya keɓanta ne a kan nazarin " Hausar Rukunin Masu Sana'ar Waya a Gusau" kawai.

    Fagge, (2001). Ya rubuta littafi mai suna"Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni" wanda shi ma wannan littafin yana da nasaba da wannan aikin sai dai, ba irin sa ba ne. A littafin, an yi tsokaci a kan nau'o'in Hausar rukuni da dama da kuma sauran abubuwa da dama. A littafin, marubucin ya yi tsokaci a kan nau’o’in Hausar rukunin jama’a da dama. Haka kuma, ba a bayyana cewa waɗannan Hausar rukanan jama’ar gari kaza ne ba. Shi kuma wannan kundin binciken ya tattauna ne a kan Hausar masu sana'ar waya a cikin farfajiyar garin Gusau kurum. Wannan ya sa littafin da wannan bincike suka bambanta.

2.1.2. KUNDAYEN BINCIKE.

Salihu, (1987) ya rubuta kundin bincike mai Taken "Code Switching among University of Sokoto Hausa English Bilingual". An yi shi ne da Ingilishi wanda yake magana a kan Ingausar Hausar da ɗalibai ke yi a yayin da suka fara yin magana da Harshen Hausa amma daga ƙarshe a ƙarasa da Harshen Ingilishi inda ya kawo misalai kamar haka;

MISALI NA (1)

 a. Akwai wata close friend ɗinmu, we are family friends'...."

b. Gaskiya abin da Umar ya yi is not good at all.

c. Muna da exams tomorrow.

Dangantakar wannan aikin da wannan binciken ita ce, dukkan su an yi su ne a kan Hausar rukuni na wasu jama’a kuma ɓangaren harshe. Abin da kuma ya bambanta su shi ne, wancan aikin an yi shi ne a kan Ingausar Hausar da dalibai ke yi a Jami’a.Yayin da wannan aikin an yi shi ne a kan Hausar masu sana’ar waya a Gusau.

  Yahaya a cikin kundin digirinsa na farko wanda ya yi shekarar(1998), wanda ya gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato mai taken "Hausa a Jami'a".

A cikin wannan kundin bincike, manazarcin ya kawo misalan Hausa a jami'a kamar haka;

 MISALI NA (2).

ƊALIBAI MAZA.

a. ƘWARO:

    Yana nufin ɗalibi mai ƙwazo.

b. JIRGI:

    Yana nufin Risho(Stove) na dafuwar abinci.

c. WANKI:

    Satar amsa ko juya aikin wani kalma zuwa kalma.

d. AHLIL KITAB:

     Ɗalibin da a kodayaushe yake tare da abin karatunsa yana karatu.

e. FARIN-WATA:

    Na nufin samun wata ‘yar matashiya game da abin da zai fito a wajen    Jarabawa.

MISALI NA (3).

ƊALIBAI MATA.

a. MALAM MAI JAR HULA:

     A wajen mata yana nufin jinin al'ada.

b. ADAMA:

     Na nufin mace mai yawan tsegumi.

c. FARFAƊIYA:

     Na nufin mace mai yawan faɗuwa, ma'ana mai yawan zina.

d. B.Z (widow):

     Suna nufin bazawara, wato wadda ta yi aure ta fito.

e. B.G.Z (Ballegaza-Disorganise woman): suna nufin mace mara kimtsi da dai sauransu.

   Zumuntar dake tsakanin waɗannan kundayen binciken ita ce, dukkansu suna a ɓangaren harshe, kuma an yi nazarin su ne a kan Hausar rukuni na wasu mutane.

  Abin da ya bambanta su kuma shi ne, a wancan kundin binciken an yi nazari a kan Hausar ‘Yan Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto. A wannan kundin binciken kuma, ana nazari ne a kan Hausar Rukunin Masu Sanaar Waya a Gusau.

  Abdulƙadir a cikin kundin bincikensa na neman digiri na farko wanda ya gabatar a Jami'ar Tarayya Gusau, Sashen Nazarin Harsuna da Al'adu a shekarar (2018), wanda ya yi a kan " Hausar Rukunin ‘Yan Banga a Garin Gusau". Shi ma wannan kundin binciken yana da alaƙa da wannan binciken. Kasancewar su duk a ɓangaren harshe kuma a ɓangaren ilimin walwalar harshe wanda ya shafi Hausar rukuni. A cikin kudin bincikensa, manazarcin ya kawo Hausar yan banga kamar yadda za mu gani a nan;

MISALI NA (4).

 

KALMOMI.                    MA'ANA

a. Sabce:                    na nufin kayan sata a wajen yanbanga.

b. Sabci-faɗi:            Bulalace irin ta dorina.

c. Tambaya:              Na nufin maganin tsarin jiki ko buwaya. 

c. Mugu:                    A wajen yanbanga yana nufin Ɓarawo.

d. Makuba:               A wajen 'yanbanga ana nufin wurin zaman 'yan

                                   daba ko  masu aikata laifi.

                                                                                         

                               

  Alaƙar wannan kundin binciken da wancan kundin binciken ita ce dukkansu suna a ɓangaren harshe, kuma ko a ɓanagren harshe duk sun shafi Hausar rukuni na wasu al’umma waɗanda ke zaune ko suke rayuwa a Gusau. Hakazalika, abin da ya bambanta su shi ne, Abdulkadir ya yi a kan Hausar Rukunin ‘Yan Banga a Garin Gusau. Yayin da wannan binciken an yi shi ne a kan ‘’Hausar Rukunin Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau’’.

2.1.3. MAƘALU.

  Shehu da Aliyu (2020) na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto wadda suka gabatar a Sashen Hausa, Kwalejin ilimi ta Adamu Augie Argungu , jihar Kebbi, Nijeriya. Maƙalar mai taken "Tasirin Wayar Salula Wajen Gurɓata Rayuwar Hausawa a Yau". Maƙalar ta yi tsokaci a kan abubuwa da dama kama daga asalin wayar salula, da amfanin wayar salula, da kuma illolin wayar salula ga rayuwar Hausawa. Bugu da ƙari, sun yi bayani a kan illolin wayar salula wajen lalata zamantakewar ma'aurata, da lalata tarbiyyar matasan Hausawa. Haka kuma, sun yi tsokaci a kan ƙulla alaƙa mara alfanu tsakanin mace da namiji ta hanyar amfani da wayar salula ta hanyoyi daban-daban.

 Bugu da ƙari, marubutan sun dubi wasu daga cikin shafukan sada zumunta tare da illolin da suka haifar wa matasa da matan al'ummar Hausawa. Marubutan sun bayar da misalai a cikin shafin sadar da zumunta na (whatsApp) inda suka rattabo sunayen da ake yi wa bidiyoyin batsa a shafin kamar haka;

MISALI NA (5).

a. Taimaka mini fanka.

b. Wada da Jesika.

c. Allah ya kiyashe mu.

d. Mummunan Rabo.

e. Madarar kawobel (cowbell) da sauransu.

Shehu da Aliyu (2020).

Duk waɗannan wuraren da aka ambata a sama, sunayen wasu wurare ne a shafin sada zumunta na (whatsApp) waɗanda babu abin da ke a cikinsu face hotuna da bidiyoyi na batsa kamar yadda marubutan suka ruwaito a maƙalarsu.

Saboda haka, akwai alaƙa tsakanin wannan maƙalar da wannan kundin bincike. Dalili a nan shi ne, kasancewar dukkansu su sun shafi wayar salula. Hakazalika, suna da bambanci domin su marubutan maƙalar sun kalli illolin wayar salula ne. Yayin da a wannan binciken kuma, an yi tsokaci ne a kan Hausar da masu sanaar waya ke yi a farfajiyar garin Gusau.

    Isah, da Abdullahi, (2020) sun gabatar da wata maƙala mai taken Language Switching between Yoruba and Hausas In Ƙaura Namoda, Zamfara State a taron ƙara wa juna sani na huɗu, na Daular Zamfara. A Tsangayar Fasaha da Nazarin addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ranar 24 ga watan biyu a skekara ta(2020). Wannan maƙalar tana da alaƙa da wannan kundin bincike kasancewar dukkansu sun shafi ɓangaren nazarin harshe. Haka kuma, a maƙalar an yi nazari a kan ingausar Hausawa da Yarbawa a ƙaramar hukumar mulkin Ƙaura Namoda. Abin da ya bambanta su shi ne , ita maƙalar an yi ta ne a kan ingausar Hausa da Yaruba a ƙasar Ƙaura Namoda. Yayin da wannan bincike kuma aka kalli Hausar Rukuni na Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau’’.

2.2. HUJJAR CI GABA DA BINCIKE.

Bincike a kan " Hausar rukunin masu sana'ar waya a garin Gusau" yana da hujjar da za a ci gaba da gudanar da shi. Bitar ayyukan da magabata suka yi ne ya tabbatar da hakan da kuma sauran ayyukan da suka gabaci wannan bincike.

  Duk da cewa ayyukan da suka gabata ba an yi su ne kai-tsaye ba kamar wannan bincike ; amma dai abin lura shi ne an yi ayyuka daban-daban a kan waya to amma, ba a yi aiki a kan Hausar masu sana'ar waya ba a garin Gusau. Wannan shi ya bayar da damar da za a ci gaba daga inda wasu masana da ɗalibai ‘yan'uwa suka tsaya domin cike wani gurbi ko giɓin da ba a cika ba. Domin kuwa Hausawa na cewa:" Ganin kafa kuma a rufe ta, shi ma ƙwazo ne."

   Babu shakka masana da damu sun yi rubuce-rubuce a kan waya da wasu abubuwan da suka dangance ta. Ɗalibai ma sun rubuta kundayen bincike  daban-daban a kan waya. To amma duk da haka, wannan bincike yana da hujjar da za a ci gaba da shi domin ba a ba shi muhimmanci da kulawar da ta dace sosai ba musamman a nan garin Gusau. Saboda haka, wannan binciken zai fito da wasu muhimman abubuwa sababbi waɗanda ba a ambata ba a wasu ayyukan da suka gabace shi.

 

 

 

2.3. NAƊEWA.

Bayan an yi shimfida a wannan babi, an tattauna a kan muhimman abubuwa da dama kamar bitar ayyaukan da suka gabata da kuma hujjar ci gaba da bincike. A ƙarƙashin bitar ayyukan da suka gabata, an yi tsokaci a kan abubuwa biyu zuwa uku kama daga samar da bayanai daga bugaggun littattafai da kundayen bincike. Daga ƙarshe kuma, aka yi bayani a kan wasu maƙaloli masu alaƙa da wannan kundin bincike domin samun nagartattun bayanai.

 

BABI NA UKU

SANA’0’IN HAUSAWA

3.0. SHIMFIƊA

A wannan babin wato babi na uku, an yi tsokaci ne a kan abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da; taƙaitaccen tarihin Gusau ta Sambo, da ma'anar sana'a, da rabe-raben sana'a da kuma muhimmancin sana'a. Haka kuma, an bayyana ma'anar waya tare da tarihin samuwarta. Bugu da ƙari, an duba amfanin wayar salula tare da lura ko kuma bayyana wasu matsalolin da ta haifar baya ga alfanunta wajen ci gaban rayuwar Hausawa. Hakazalika, wannan babi ya ƙara haska mana fitila a kan wannan bincike tare da nuni a kan inda binciken ya fuskanta. Saboda haka, an fara yin taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Daga bisani kuma, sauran bayanai suka biyo baya dalla-dalla.

3.1. GUSAU TA SAMBO.

An kafa garin Gusau a shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da sha ɗaya (1811) a hasashen kundayen bincike, wato bayan tasowa daga ‘Yandoto a shekarar (1806).

   Gusau na ɗaya daga cikin manya-manyan garuruwan tsohuwar jihar Sakkwato, kafin garin ya zama babban birnin jihar Zamfara a shekara ta (1996). Kamar yadda kundin bayanin tarihin ƙasa na shekarar (1920) ya nuna, garin Gusau yana kan babban titin Sakkwato zuwa Zaria, wato kilo mita ɗari biyu da goma (210) tsakaninta da Sakkwato, kilo mita ɗari da saba'in da tara (179) tsakaninta da Zaria. A ɓangaren gabas Gusau ta yi iyaka da ƙasar Katsina da Kwatarkwashi, daga Arewa kuma, ta yi iyaka da ƙasar Ƙaura-Namoda. A ɓangaren yamma kuma, Gusau ta yi iyaka da Bunguɗu. A ɓangaren kudu, Gusau ta yi iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe.(Gusau,1912:7).

   Zuwan almajiran malam Shehu Usmanu Ɗanfodiyo wato malam Sambo ɗan'Ashafa ya kafa garin Gusau tare da sauran jama'arsa. Malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa malaman addinin Musulunci ne, don haka, babu ruwan su da bautar iskoki, da tsafi da duk abin da ya shafi imanin Bahaushe na gargajiya da dukkanin camfe-camfensu. Duk irin bautar iskokin da Hausawa ke yi kafin zuwan addinin Musulunci malam Sambo ɗan'Ashafa da almajiransa ba sa yin su ko kuma a lokacin da ya zo Gusau bai samu irin waɗannan abubuwa na bautar iskoki a Gusau ba. Don haka, a wannan lokacin garin Gusau ba ya da tarihin Jahiliyya. Hakan ya sa duk al'adun Gusau al'adu ne irin na addinin Musulunci. Hakazalika, shigowar wasu mutane baƙi a Gusau bai sa garin ya gurɓace ba kuma Waɗannan kyawawan al'adun ba su lalace ba. Dalili a nan shi ne mafi yawan baƙin mutanen da ke shigowa a Gusau malamai ne na addinin Musulunci da kuma almajirai.

Bugu da ƙari, Fulani da wasunsu kan zo garin Gusau domin samun tsira da  addininsu, mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu. Wannan ita ce shimfiɗar da al'adun Gusau ke kwance a kai kuma suke gudana a kan koyarwar addinin Musulunci da kyawawan al'adu irin na Fulani da Hausa waɗanda ba su ci karo da tsarin shari'ar addinin Musulunci ba.

   A Zamanin Mulkin Sarkin Katsinan Gusau wato Malam Muhammad Modibbo aka samu kwararowar baƙi da ƙungiyoyin mutane daban-daban. Zuwan waɗannan baƙin ya sa garin ya samu bunƙasa a cikin ƙanƙanen lokaci. Haka kuma, a  wannan lokaci ne aka samu sukunin gudanar da harkokin addinin Musulunci waɗanda suka shafi karatu, karantarwa, da kuma harkokin ibada ba tare da wata takura ko tsangwama ba. Bugu da ƙari, akwai cikakken tsaron rayukan mutane da dukiyoyinsu. Don haka, a wannan lokaci babu abin da ya sha wa mutanen Gusau kai face harkokin karatu, noma da kuma kasuwanci.

    Zuwan Turawan mulki mallaka a Ƙasar Hausa da tasirin karatun boko ya sa wasu al'adu tsiruwa. Ana cikin haka sai ga shari'ar Musulunci ta sake kawo kai. An samu canje-canje da dama a wannan lokaci, domin an samu mutane da suka shahara da gudanar da tafsiri a masallatan Jumu'a da wasunsu a garin na Gusau. A yanzu dai, garin Gusau yana da masarauta ɗaya rak, babban sarki ɗaya wato emiya (Emir). Wakilai ko uwayen ƙasa goma sha uku(13), yan majalisa goma sha takwas(18), sarautun fada kuma akwai aƙalla ɗari ɗaya da goma (110).

  Daga lokacin da aka kafa garin Gusau ya zuwa yanzu , an tabbatar da cewa an yi sarakuna da dama a lokuta daban-daban kimanin Sarakuna goma sha biyar (15), wato daga shekarar (1806) ya zuwa shekarar dubu biyu da ashirin da ɗaya (2021). Saboda haka, Sarakuna da dama sun Jagoranci masarautar Gusau da mutanen garin Gusau. Don haka, ga jerin sunayen Sarakunan da suka yi mulki a masarautar Gusau daga shekara ta dubu ɗaya da ɗari takwas da shida (1806) zuwa shekara ta dubu biyu da ashirin da ɗaya (2021) kamar haka;

1. Malam Muhammad Sambo (1806-1827)

2. Malam Abdulƙadir (1827-1867)

3. Malam Muhammad Modibbo (1867-1876)

4. Malam Muhammad Tuburi (1876-1887)

5. Malam Muhammad Giɗe (1887-1900)

6. Malam Muhammad Murtala (1900-1916)

7. Malam Muhammad (1916-1917)

Akwai wasu sarakunan da suka yi sarautar Gusau bayan waɗannan Sarakuna waɗanda ba ‘yayan wancan gidan na farko ba. Don haka, waɗanda suka yi Sarautar masarautar Gusau ba daga gidan malam Sambo ba sun haɗa da;

8. Muhammad Ummaru Malam (1917-1929)

9. Muhammad Mai-Akwai (1929-1943)

10. Usman Ɗansamaila (1943-1945)

11. Ibrahim Marafa (1945-1948)

12. Muhammad Sarkin Kudu (1948-1951)

13. Alhaji Suleiman Isah (1951-1984).

Waɗannan su ne suka yi sarauta waɗanda ba ‘yayan malam Sambo ba. Bugu da ƙari, bayan wani lokaci, sarauta ta dawo gida. Sarakunan da suka yi mulki bayan sarauta ta dawo gidan sun haɗa da;

14. Alhaji Muhammad Kabir Ɗanbaba (1984-2015)

15. Alhaji Ibrahim Bello (2015-ya zuwa Yau).

   A taƙaice dai, waɗannan su ne Sarakunan da suka mulki masarautar Gusau daga shekarar (1806) zuwa shekarar (2021). Haka kuma, wannan shi ne taƙaitaccen tarihin Gusau ta Sambo a yayin aiwatar da wannan bincike.

 

 

3.2.  MA'ANAR SANA'A.

    Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma'anar Sana'a. To amma kafin mu bayyana ma'anar sana'a, yana da kyau mu tantance asalin kalmar Sana'a domin sanin inda kalmar ta samo asali.

Junaidu da ‘Yar’Aduwa (2002) sun ce, ‘‘Sana’a kalma ce wadda aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’anar samar da wani abin amfani ta hanyar hikima’’.

   A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da wahalar ƙididdigewa. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai manya akwai kuma ƙanana. Sannan kuma masana sun kasa su zuwa kashi uku da suka haɗa da sana’o’in maza, sana’o’in mata da kuma sana’o’in haɗaka ko gamayya.

  Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi yin su. Ko da an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali, sana’ar ƙira, fawa, da sauransu.

Sana’o’in mata kuma su ne, sana’o’in da mata ne kawai suka keɓanta da yin su. Idan aka ga namiji a ciki irin waɗannan sana'o'i a kan kira shi da ɗan daudu. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai sana’ar kitso, dafe-dafen abinci, da sauransu.

Sana’o’in gamayya kuma su ne sana’o’in da maza da mata suka yi tarayya a ciki. Daga cikin irin waɗannan sana’o’i akwai kiwo, roƙon baka da sauransu.

 A Hausance kuma, kalmar tana ɗaukar ma'anar samar da abin yi ko abin amfani ta hanyar hikima ko fasaha.

   Saboda haka, masana da dama sun tofa albarbakacin bakinsu dangane da ma'anar sana'a. Masanan sun haɗa da;

   Calvin, (1982). Ya bayyana ma'anar sana'a da cewa,  "Ita ce ginshikin rayuwa da tattalin arzikin yau-da-kullum na Hausa". Ya ci gaba da cewa,  ''tana kuma ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin gane martabar mutum da ƙasarsa da kuma matsayinsa cikin al'umma''.

   Bagari, (1986) cewa ya yi, " Sana'a na nufin duk wata hanyar saye da sayarwa wadda ɗan'adam ke bi domin samun kwabon kashewa don buƙatunsa na yau-da-kullum".

  Yahaya, (1992) ya ce, " Sana'a hanya ce ta amfani da azanci da hikima da sarrafa albarkatu da ni'imomin da ɗan'Adam ya mallaka domin buƙatunsa na yau-da-kullum".

  Zarruƙ, (1987) ya bayyana ma'anar sana'a da cewa, " Wata aba ce da mutum ke yi domin samun abin masarufi wajen gudanar da harkokin rayuwa na yau-da-kullum".

  Zabarina, (1987) ya ce, " Sana'a wata aba ce da mutum yake yi domin samun abin masarufi wajen gudanar da harkokin rayuwa na yau-da-kullum".

   Ɗangambo, (2004) ya bayyana cewa, " Sana'a hanya ce ta sarrafa ɗimbin albarkatun ƙasa da dabbobi da abubuwan da ke hannun ɗan'adam da nufin juya shi ya zama abin buƙata don samun abin rufa ma kai asiri." Ya ƙara da cewa, "Sana'a hanya ce da ake amfani da hikima da fasaha domin sarrafa wani abu ko aikata wani abun buƙatar al'umma na saye da sayarwa ko aikin hannu ko ma na ƙarfi don samun abun buƙatar rayuwa ta yau-da-kullum".

  Duba da abin da masana suka ce dangane da ma'anar sana'a, za a iya cewa Sana'a na nufin yin amfani da wata hikima ko fasaha ko basirar da Allah Ya yi wa wani ko wata domin samun abin masarufi daga abin da ya aikata na hannu ko waninsa.

3.3. RABE-RABEN SANA'A.

Masana sun rarraba sana'o'in Hausawa zuwa manyan gidaje biyu kamar haka;

A. Sana'o'in Hausawa na gargajiya

B. Sana'o'in Hausawa na zamani.

3.3.1. SANA'O'IN HAUSAWA NA GARGAJIYA

Zurmi, (2010) da Madabo, (1979) sun kawo sana'o'in Hausawa na gargajiya kamar haka;

1. Farauta

2. Su

3. Noma: Rani/Damana

4. Kiwo

5. Fawa

6. Kaɗi

7. Saƙa

8. Ɗinki

9. Rini

10. Jima

11. Dukanci

12. Gini

13. Ƙira

14. Sassaƙa

15. Fatauci

16. Dillanci

17. Wanzanci

18. Kitso

19. Magani da sauransu.

Mafi yawancin sana'o'in Hausawa na gargajiya jinsin maza ne suka kasa suka tsare a wajen aiwarta da sana'o'in. Amma a wajen sana'o'in Hausawa na zamani, abin ba haka yake ba domin kuwa akwai waɗanda kowa ke yi, wato na tarayya.

3.3.2. SANA'O'IN HAUSAWA NA ZAMANI.

Akwai sana'o'i daban-daban waɗanda zamani ya zo da su a ƙasar Hausa. Sana'o'in sun haɗa da;

1. Sana’ar Sayar da Motoci.

2. Sana’ar Sayar da Mashin.

3. Sana’ar Sayar da Keke.

4. Sana'ar Sayar da Talabijin

5. Sana’ar Sayar da Jarida.

6. Sana’ar Sayar da Littafai na Boko da Addini.

7. Sana’ar Sayar da Kayan Wuta (electrics).

8. Sana’ar Sayar da Wayar Salula.

9. Sana’ar Sayar da Sola.

10. Sana’ar Sayar da injinin Wuta (Generator).

11. Sana’ar Sayar da Awara ko Gala ko Ƙwai-da-Ƙwai.

12. Sana’ar Sayar da Katin Waya.

13. Sana’ar ɗinkin Tela.

14. Sana’ar Sayar da Sutura.

15. Sana’ar Sayar da Kayan Bulawus.

16. Sana’ar Askin Wuta.

17. Sana’ar Aikin Hannu na Tufafi.

18. Sana’ar Sayar da Takin Zamani.

19. Sana’ar Sayar da Maganin Feshin Haki.

20. Sana’ar Fotokofi da Lamineshin da dai sauransu.

 Duk waɗannan sana'o'i ne na zamani amma ba a ce suke nan ba, za a iya samun wasu masu tarin yawa waɗanda ba a ambata ba a wannan kundin bincike.

3.4 MUHIMMANCIN SANA'A

Sana'o'in da Hausawa kan yi na gargajiya da na zamani suna da alfanu ƙwarai da gaske ga rayuwarsu dama sauran al'ummar da suke rayuwa a wuri ɗaya tare da Hausawa. Bugu da ƙari, sana'o'in Hausawa na da muhimmanci sosai kamar yadda za mu ga kaɗan daga cikin alfanun sana'a’o’in kamar haka;

1. Sana'a na taimakawa wajen samar da aikin yi ga Hausawa da    waninsu.

2. Sana'a na sa a samu abin rufa wa kai asiri.

3. Sana'a na hana mutane zaman banza da yawon banza a gari.

4. Sana'a na hana abin da ba naka ba ya tsone ma ido.

5. Tana hana yawaitar samun ɓarayi a gari.

6. Tana haifar da zumunci mai ƙarfi a cikin al'ummar Hausawa da waninsu.

7. Ana ƙulla auratayya sanadiyyar sana'a tsakanin maza da mata.

8. Tana ƙara wa al'ummar Hausawa da waninsu ƙarin ƙarfin tattalin arziki.

9. Sana'a na ƙara ƙarfin tattalin arziki a gari, jiha dama ƙasa baki ɗaya.

3.5. MA'ANAR SADARWA.

 

Masana sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da ma'anar sadarwa. Daga cikinsu akwai;

  Zarruƙ da wasu, (1986) sun bayyana ma'anar sadarwa da cewa, " Miƙa saƙo irin na gargaɗi ko umarni ko dai wata sanarwa ta musamman da kuma aikata wani abu sakamakon wannan saƙon." Sun ƙara da cewa," Irin wannan hulɗa da ke faruwa tsakanin al'umma ita ake nufi da sadarwa."

 

   Yakasai, (2013) ya ce, " Sadarwa hanya ce da ɗaiɗaikun mutane ke musayar bayanai cikin tsari, ana amfani da abubuwa daban-daban da suka haɗa da kalmomi da ishara da gaɓuɓɓa da kuma ɗabi'a’’.

 

  Webster, (1973) an bayyana sadarwa da cewa, " Yanayin sarrafa bayanai ne tsakanin al'umma, cikin tsarin alamomi da ishara da kuma ɗabi'a". Wato kafin sadarwa ta tabbata, to wajibi ne a samu fahimtar juna tsakanin mai magana da wanda ake yi wa maganar.

 

  Akpan, (1980:32) Ya nuna cewa, ‘’ Sadarwa tsakanin al'umma tana damfare ne da ma'ana fiye da bayanai kara zube.’’

 

  Folarin, (2002:18) ya bayyana cewa, " Ai duk wani martani da za a samu ciki hulɗa da mu'amala sun dogara ne ga irin maganar da ke biye da ita. Don haka, kafin saƙo ya yi tasiri daga mai aike zuwa mai karba, to wajibi ne a samu dacewa cikin ma'ana da kuma fahimta".

 

  Bunza, (2002) ya bayyana cewa, " Sadarwa ita ce isar da saƙo tsakanin ɓangarori biyu: mai bayar da saƙo da kuma mai karɓar saƙo ta hanyar kafar isar da saƙo wacce kan iya zama mutum ko waninsa, sannan kuma cikin sigar da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa za su iya fahimta".

 

  A taƙaice dai, matuƙar babu ma'ana, to babu sadarwa . Saboda haka, ta kowace fuska sadarwa na da cikakkiyar fa'ida cikin kowane al'amari na rayuwa.

 

   Saboda haka, duba da abin da masana suka faɗa dangane da ma’anar sadarwa, za a iya cewa, sadarwa na nufin bin wata hanya domin saƙo ya isa tsakanin mai bayar da saƙo zuwa ga mai karɓar saƙon tare da fahimtar maanar saƙon ta hanyar da aka sadar da shi zuwa ga mai karɓarsa.

 

3.6. RABE-RABEN SADARWA.

 

     Sadarwa ta kasu zuwa manyan rukunai guda biyu kamar haka;

i. Sadarwa ta gargajiya.

ii. Sadarwa ta Zamani.

 

3.6.1.i. SADARWA TA GARGAJIYA.

 

Zarruƙ da wasu, (1986) sun ce, ‘’ sadarwa ta gargajiya hanya ce da hukumar Hausawa ke ba da sanarwa zuwa ga alummarta. Wannan sanarwa takan kasance ko a aikata wani abu ko kuwa a bar aikata shi. Sanƙiran gari shi ake umarta da ya zaga gari unguwa-unguwa yana shaida wa jama’a saƙon. A wasu wurare ma ta wannan hanyar ne ake cigiyar abin da ya salwanta".

 

3.6.2. ii. SADARWA TA ZAMANI.

 

Zarruƙ da wasu (1986) sun bayyana cewa: " Hanyoyin sadarwa ta zamani sun haɗa da ƙasidu, da katuna, da tarho, da wayar tangarahu, da wasiƙa da kasat da liƙa bajo da kafa tuta da dai sauransu". Sun nuna cewa: a kan ɗaura ganye a kan abin hawa don nuna cewa wannan abin hawan na sayarwa ne. In kuwa mota ce wanann ya nuna cewa motar tana ɗauke da gawa ne.

 

  Don haka, Zarruƙ da wasu (1986) a cikin littafinsu mai suna "Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Littafi Na Ɗaya" sun rarraba hanyoyin sadarwa zuwa gidaje da dama kamar yadda za mu gani a nan ƙasa;

 

1. Hanyoyin sadarwa masu nuna farin-ciki na Hausawa. A ƙarƙashin

     wannan akwai misali kamar haka: Guɗa.

2. Hanyoyin sadarwa masu nanu baƙin-ciki. Misali, kuka.

3. Hanyoyin sadarwa masu nuna tashin-hankali. Alal misali,ihu da kuma

     kururuwa.

4. Hanyoyin sadarwa na gargajiyar Bahaushe. Alal misali, yekuwa ko  

     shela,kuge/kurya, ƙaho/gwarje, bindiga da kar-ta-kwana da dai

     sauransu.

 

5. Hanyoyin sadarwa na zamani. Misali, Rediyo,Talabijin, Jaridu da

     mujalloli, ƙasidu, katuna, tarho, wayar tangaraho, wasiƙa da kaset da

     bajo da sauransu.

6. Hanyar sadarwa ta amfani da gaɓoɓi. Alal misali, fuska, baki, ido,

     goshi, Kunne, hanci, Kai, gatshine, hannu, ƙafa, tagumi da dai   

     sauransu.

 

3.7.MA'ANAR WAYAR SALULA

 

Masana da dama sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da ma'anar waya. Daga cikinsu akwai;

 

  Abubakar (2015:487) ya bayyana ma'anar waya da cewa, " Ita kalmar suna ce da ke cikin jinsin sunaye na mace, jam'i kuma wayoyi". Ya ƙara kiranta da na'urar sadarwa. Wato "Tarfo".

 

  A kundin ma'anoni na Britannica (2006), an fassara kalmar telephone da cewa, " Na'ura ce da aka shirya domin yaɗawa da kuma karɓar muryoyin ɗan'adam". An nuna cewa, ana amfani da ita wajen sarrafa muryoyin ɗan'adam".

 

  Webster, (1990:1212) ya bayyana ma'anar waya da cewa," Wata na'ura ce da ake sadar da sautin maganganu da ita zuwa ga waɗanda ke nesa da mai magana".

 

 Macmillan, (2007:1118) ya bayar da ma'anar wayar Salula da cewa," Wata na'ura ce da ake amfani da ita wajen sadar da saƙonni zuwa ga wani ta hanyar tarho".

 

  A ra'ayin Newman (2012:277) ta fassara  ma'anar kalmar (TELEPHONE) ta Ingilishi da cewa, " Waya" wato tarho. A yayin da ta ba da misali cikin jimla kamar haka: " ya yi mini waya" wato mun yi magana da shi ta hanyar na'urar sadarwa.

 

 Bayero, (2006) ya bayyana cewa, "Wayar hannu ( cellular phone) wayar tarho ce da ke bayar da damar sadarwa a ƙayyadadden muhalli da ke iya kai ɗaruruwan murabba'in milulluka, ta hanyar amfani da hanyar sadarwar zangon rediyo daga megahatz (800) zuwa (900)".

 

 La’akari da ra’ayoyi mabambanta na masana da suka gabata, za a iya bayyana ma’anar wayar salula da cewa, wayar salula na'ura ce mai ɗauke da abin magana a baki da kuma wanda za a ji a kunne a haɗe wuri ɗaya, ta ƙunshi malatsai ko abubuwan da ake turawa ko dannawa domin aika saƙo ta hanyar amfani da sautin murya ko kuma a aika saƙo a rubuce ko ta wata hanya mai kama da haka.

 

3.8. SAMUWAR WAYAR SALULA.

 

Akwai ra’ayoyi da dama mabambanta dangane da abin da ya shafi tarihin wayar salula da kuma wanda ya fara samar da ita kamar yadda za mu gani.

 A cikin shekarar (1876) Allexander Graham Bell ya samar da wayar na'urar yaɗa sautin magana ta hanyar lantarki. A cikin shekaru ashirin (20 years) aka samu Tarho, tun daga wannan lokacin ba a samu wani sauyi ba, sai zuwa shekarar (1947) kamar yadda tiramsisto ta bayyana a shekarar (2006:1883).

 

   A wani ƙauli kuma, an bayyana cewa; wani Bature ɗan ƙasar Amurka mai suna Martin Cooper shi ya fara tunanin yadda zai fara samar wa jamaa sauƙin sadarwa. Martin Cooper wanda aka haifa a ƙasar Amurka a ranar 26 ga watan Disamba a shekarar (1928). Ya sami nasarar ƙirƙira wayar salula a cikin shekaru goma da ya yi a matsayin daraktan bincike na kamfanin motorola. Bayan shekaru goma da ƙirkiro wayar ne aka fara fito da ita a kasuwa domin sayarwa jama’a. Wannan ƙoƙari na Cooper ya sami yiwuwa ne a cikin shekarun (1960) zuwa farkon (1970). A ranar 3 ga watan Afrilun shekarar (1973) ne Martin Cooper ya sami buga wayar farko mai suna Dynatac a garin New york. D.W, Hausa, (06/08/2007).

 

  A Nijeriya kuma, wayar salula ta shigo ƙasar ne a shekara ta (2000) zuwa (2001). A ɓangaren jihar Zamfara kuma, wayar salula ta zo ne a dai-dai shekara ta (2002) zuwa (2003). Ko kuma, a shekara ta (2003) zuwa (2004). A taƙaice dai, ya zuwa yau, wayar salula ta samu aƙalla shekaru goma sha bakwai (17) zuwa goma sha takwas (18) a jihar Zamfara. Ladan, (2020).

  A yau akwai nau’o’in wayoyi iri daban-daban a Nijeriya da kuma jihar Zamfara waɗanda suka haɗa da; Nokia, da Tecno, da Gionee, da Samsung, da Itel, da Iphone, da Infinix, da Motorola, da Huawei, da Sony Ericsson, da Alcatel, da ZTE, da HTC, da Bird, da BlackBerry, da Nec, da Panasonic, da Sony, da Toshiba, da Vodafone, da T-Mobile, da Siemens, da Oppo, da 02, da Lenovo da dai sauransu da dama.

 

3.9  AMFANIN WAYAR SALULA.

 

   Wayar salula tana da matuƙar muhimmanci da amfani ga rayuwar Hausawa da mutanen garin Gusau da kewayenta. Wayar salula ita ce aka fi mayar da hankali a wajen sadarwa, wadda samuwarta ya jawo wadatuwar sadarwa a tsakanin jamaa. Takan jawo nesa kusa, domin babu lokacin da za a riƙa haɗuwa da ‘yan uwa da abokan arziki a kodayaushe, amma a kan yi amfani da ita a sadar da zumunci a duk lokacin da aka samu dama musamman ga waɗanda ba zaune suke a unguwa ɗaya ko gari ɗaya ko ma a ƙasa ɗaya da ‘yanuwwansu ba.

 

  Wayar salula ta kawo ci gaba ta hanyoyin kasuwanci da sana'o'i daban-daban da kuma ilimi da sauran fannonin rayuwar Hausawa a yau. Domin a yau, ana gudanar da hada-hadar kasuwanci ta amfani da wayar salula sosai-da-sosai. Bugu da ƙari, ta zama wata muhimmiyar hanyar da Kamfanoni da 'yan kasuwa ke hulɗar cinikayya a tsakaninsu tare da gudanar da sauran harkokin kasuwancinsu na yau-da-kullum. Wannan amfani na waya ya sauƙaƙa tsawon lokacin da 'yan kasuwa ke ɗauka kafin ƙulla hulɗa ko haɗuwa da junansu. A yau, Hausawa na hulɗar kasuwanci da wayar salula maimakon haɗuwa ido-da-ido domin ƙulla cinikayya. Bugu da ƙari, kaɗan daga cikin amfanin wayar salula ga al’ummar garin Gusau akwai;

1.Wayar salula ta taimaka wajen taƙaita zirga-zirgar da ‘yan kasuwa ke

    Yi zuwa wajen sayen kayan sana’arsu. A maimakon haka, sai dai su yi       

    amfani da wayar salula domin yin magana, ko aika saƙo ko kuma

    a aika kuɗi a banki ta hanyar tiransifa  zuwa ga asusun wanda za a

    sayi kaya a hannunsa domin ya aiko da kayan da suka saya a    

    hannunsa ba tare da an haɗu ba.

2. Zuwan wayar salula a garin Gusau ya taimaka wajen samar da

    sabuwar Hausar rukuni na masu sana’ar wadda ake nazari a kai a

    cikin wannan kundin bincike.

3. Wayar salula ta taimaka wajen samar da sabuwar sana’ar zamani da 

     Hausawa kan yi domin samun abin da za su rufawa kansu asiri da         

     samun abin dogaro da kai.

4. ‘Yan kasuwa Hausawa musamman mazauna garin Gusau da kewaye

      kan yi amfani da wayar salula ta hanyar tallata hajojinsu a kafafen

      sadar da zumunta kamar WhatsApp da Facebook da Instagram ta

      hanyar amfani da manhajar sitatus a kafafen.

5.  Wayar salula ta taimaka wajen jawo nesa kusa.

6.  Waya tana taimakawa ɗalibai da malamai da kuma manazarta domin

     samun sauƙin ƙarin bayanai a yanar gizo.

7. Wayar salula tana matuƙar taimakawa wajen sadar da zumunci ga

     yanuwa da abokan arziki na kusa da kuma mazauna wurare daban- 

     daban musamman waɗanda ke nesa da junansu.

8. Wayar salula na taimakawa ainun wajen isar da saƙo nan take a

     tsakanin al'umma ba tare da wata wahala ba.

 

 

 

 

3.10. ILLOLIN WAYAR SALULA.

 

  Baya ga alfanun da wayar salula ta samar wajen ci gaban al’ummar Hausawa da kuma mutanen garin Gusau, akwai wasu abubuwa marasa alfanu da dama waɗanda wayar salular ta haddasa aukuwarsu musamman a nan cikin garin Gusau da kewayenta. Don haka, daga cikin abubuwa marasa alfanu da wayar salula ta haifar a cikin birnin Gusau da kewayenta akwai;

1.Wayar salula ta haddasa yawaitar ƙarya a cikin alummar garin Gusau

    da kewaye.

2. Ana amfani da wayar salula domin damfarar mutane.

3. Wayar salula ta ƙara zama wata hanyar da wasu ɓata gari ke amfani

     da  ita domin cin amana da kuma ha’inci a tsakanin al’umma.

4. Wayar salula ta sa an samu ƙaruwar ta’addanci da sace-sacen

     dabbobi da kuma yawaitar garkuwa da mutane a Gusau da

     maƙwabtanta.

5. Wayar salula tana lalata zamantakewar wasu ma’aurata ta hanyar sa

     shakku da zargi a tsakanin ma’aurata.

6. Wayar salula tana lalata tarbiyyar yara ƙanana da matasa maza da

     mata da kuma manyan mutane.

7. Wayar salula ta taimaka wajen koyar da munanan halaye da dabi’u

     ga yara maza da mata da kuma manya maza da mata.

 

3.11. NAƊEWA

Kamar yadda aka yi bayani a baya cikin wannan babi, an yi tsokaci a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau da sarakunan da aka yi a masarautar. Haka kuma, an yi bayani a kan ma’anar sana’a, da rabe-rabenta da kuma muhimmancin sana’a. Hakazalika, an bayyana ma’anar sadarwa da rabe-raben sadarwa. Bugu da ƙari, an bayyana maanar wayar salula da kuma tarihin samuwarta. Daga ƙarshe kuma, mun fahimci cewa wayar salula tana da amfani da kuma illolin da ta haifar a cikin garin Gusau da kewaye.

 

BABI NA HUƊU

 

IRE-IREN WAYOYI DA AMFANIN SU

 

4.0 SHIMFIƊA

 

   Bayani a kan taƙaitaccen tarihin Gusau da maanar sanaa da rabe-raben sanaa da kuma muhimmancin sanaa sun gabata a babi na uku. Haka kuma, an yi bayani a kan maanar sadarwa da rabe-benta. Bugu da ƙari, an bayyana maanar wayar salula da tarihin samuwarta. Daga ƙarshe kuma, an bayyana  muhimmancin waya da kuma illolin wayar salula a cikin garin Gusau da kewayenta.

     Saboda haka, a wannan babin, an ƙara nutsawa sosai da sosai a cikin wannan bincike domin kalato abin da ya samu musamman abubuwan da suka shafi rabe-rabe ko kuma  ire-iren wayoyi. Bugu da ƙari, an zaƙulo wasu muhimman wurare waɗanda ake sayar da waya a Gusau kama daga tsofaffin wurare da kuma sababbi.

     Hakazalika, an ɗan yi tsokaci a kan masu sana’ar waya a garin Gusau. Daga ƙarshe kuma, an rattabo sunayen wayoyi da kalmomi da kuma jimlolin da masu sana’ar waya ke amfani da su a wurin cinikinsu na yau-da-kullum.

 

4.1 WURAREN DA AKE SAYAR DA WAYA A GUSAU

 

   Wuraren da ake sayar da waya a Gusau za a  iya cewa sun kasu kashi biyu kamar yadda za mu gani:

1. Wuraren da aka fara sayar da waya a Gusau can da.

2. Wuraren da ake sayar da waya a Gusau yanzu.

 

4.1.1 WURAREN DA AKA FARA SAYAR DA WAYA A GUSAU.

 

       A yayin gudanar da wannan binciken, an yi ƙoƙarin zaƙulo  wasu muhimman wuraren da aka fara sayar da waya a Gusau, wato shekaru goma sha biyar zuwa goma sha bakwai da suka gabata, ta hanyar tattaunawa da waɗansu tsofaffin yan kasuwar waya. Mukhtar coach ya tabbatar da cewa a lokacin da waya ta zo a Gusau wuraren da aka fara sayar da waya sun haɗa da;

 

1. Rambo comunication unguwar Ahmadu Bello way.

2. O.D Ventures Tudun-Wada bakin sha-tale-tale.

3. Macmillan communication tsohuwar Kasuwa.

 

    Waɗannan su ne wuraren da aka fara sana'ar sayar da waya a Gusau. Abin lura a nan shi ne, duk waɗannan wurare da aka fara sayar da waya a Gusau, wuri ɗaya tak ya rage daga cikin uku wato Macmillan communication kuma har yanzu ana sayar da waya a wannan shagon.

 

4.1.2. WURAREN DA AKE SAYAR DA WAYA A GUSAU YANZU

 

Akwai wurare da dama waɗanda ake sana’ar sayar da waya a cikin gari a halin yanzu. Saboda haka, wannan binciken ya yi ƙoƙarin tsakalo wasu muhimman wurare musamman manya-manya  da kuma ƙananan wurare waɗanda ake gudanar da hada-hadar kasuwanci waya zalla da kuma kayayyakinta kama daga tsofaffi da sababbin wayoyi kaloli daban-daban gwargwadon irin wayar da mutum ke so ya yi amfani da ita. Saboda haka, ga wasu kaɗan  daga cikin wuraren da ake sayar da waya a garin Gusau kamar haka;

1. Xcell communicattion unguwar Dallatu kusa da masallacin idi.

2. Ya musamu communiction unguwar Dallatu bakin titi.

3. Yabagi communication kan titin Amadu Bello way.

4. Annur communication bakin gidan gwamnati.

5. Ba ka sheri communication gangaren kwata kusa da gidan Haido.

6. Gamji plaza kusa da babbar tasha Gusau.

7. Bebeji plaza kusa da tankin ruwa Sabon Gari.

8. Jari-bola bayan asibitin Farida.

9. Macmillan communication bakin folo.

10. Mannir easy communication tsohuwar kasuwar Gusau kusa da     Sule Mamuda plaza.

 

A halin yanzu, waɗannan su ne fitattun wuraren da ake sayar da waya a cikin farfajiyar garin Gusau.

 

4.2 MASU SANA’AR WAYA A GUSAU.

 

   Masu sana’ar waya a Gusau mutane ne maza akasarin su yara, samari da kuma magidanta. Don haka, maza su ne suka kasa suka tsare a wajen gudanar da sana’ar sayar da waya a garin Gusau da kewayenta. Duk da cewa, akwai wasu shaguna da kantuna waɗanda ake samu an yi haɗaka wajen gudanar da kasuwancin, wato maza da mata kan sayar da wayoyi a shagunan ko kuma kantuna. Alal misali, Xcell communication da makamantansu.

 

     Bugu da ƙari, masu sanaar waya a garin Gusau sun kasu kashi daban-daban. Domin akwai abubuwa da dama waɗanda suke jingine a jikin sana’ar waya. Amma dai wannan binciken ya ci karo da wasu nau’o’i na masu sana’ar waya a Gusau kamar haka;

1.  A wasu shaguna da kantuna wayoyi sababbi kaɗai ake sayarwa.

2. Wasu shaguna da kantuna kuma ana sayar da sababbi da tsofaffin

     wayoyi.

3. Akwai masu sana’ar gyaran waya idan ta samu wata matsala.

4. Wasu kuma leda suke yi wa sababbi da tsofaffin wayoyi.

5. Akwai masu sayen wayoyi marasa lafiya su gyara domin su sayar.

6. Wasu kuma memorin waya suke sayarwa.

7. A wasu shaguna da kantuna kuma, ba a sayar da komai sai kayan

    waya wato sassanta (spare parts). Misali kamar batir, da sikirin, da

    tocin da sikirin gad da dai sauransu.

A taƙaice dai, waɗannan su ne nau’o’in mutane masu sana’ar waya da kuma nau’in abubuwan da suke sayarwa a cikin kasuwannin sayar da wayoyi a farfajiyar garin Gusau.

4.3  IRE-IREN WAYOYI.

 

An rarraba wayoyi zuwa rukuni-rukuni dangane da irin aikin da waya ke iya yi. Rukunan wayoyin sun haɗa da;

 = Simat fon

 =  Kemara fon

 = Muisik fon

 = 3G fon.

 Bayan wannan rukuni wayoyin, akwai wani rukuni na wayoyi kamar haka;

 

A. Anduroyid. (Android).

B. Kifad. (keypad).

C. Simbiyan (symbian).  

 

 

4.3.1.( A) ANDUROYID (ANDROID).

 

Kamfunna da dama na yin wayoyi anduroyid kama daga Tecno, da Itel, da Samsung, da Sony Ericksson, da Lava, da Gionee, da Infinix da dai sauransu. A ɓanagren wayoyi anduroyid  ƙirar Tecno kuma, za a iya samun misalai kamar haka;

 

MISALI NA (6).

 

 K7, da Camon11, da W3, da W4, Cammom Cm da Pouvour3 da dai sauransu. Buga da ƙari, kamfanin Itel ƙirar anduroyin kuma za a iya samun misalan wayoyi irin su; P33 plus,da P33, da  P12, da P32 da makamantansu. A ɓangaren Kamfanin Samsung ƙirar anduroyid kuma, ana iya samun misalan wayoyi irin su  tab E, da Hot4, da Hot6 da hot9, da samsung galaxy da ire-irensu.

 

 

4.3.2. (B) KIFAD  (KEYPAD).

 

Wayoyi ƙirar kibod (key-board) sun kasu kashi-kashi. Daga cikin kashe-kashensu akwai;

1.Kibod (key-board); Wannan wani rukunin waya ne wanda ake samun

    waya ɗaya tare da kifad da tocin. Irin waɗannan wayoyin su ake kira

    kibod  (key-board).

 

   MISALI NA (7).

 

    Blackberry Q10 da Q5, da Nokia C2 silaida (slide), da C3, da

    Sony Errickson K500 da K750, da Tecno D1 da Q1 da dai sauransu.

 

2. Kifad nomal (keypad normal); Wannan rukunin kuma, wayoyi ne

     waɗanda ake yin kira ko aika saƙo kaɗai da su. Ba su yin komai baya

     ga kira ko aika saƙo. Bugu da ƙari, ba su  burawuzin (browsing) ko

     kaɗan.

 

      MISALI NA (8).

 

     Nokia103, 1800, da 105. Duk waɗannan wayoyin layi ɗaya gare su            

     kuma ba a komai da su face kira, aika saƙo da wasanni wato

     (games).

 

3. Kifad jaba (keypad java): Wannan rukunin wayoyin kuma wayoyi ne

     masu tsarin burawuzin wato suna buɗe opera kuma ana burawuzin    

     da su.

     MISALI NA (9).

 

    Tecno 660 kuma tana da layi biyu.

 

4. kifad mai layi ɗaya. Waɗannan wayoyin ba su burawuzin sannan

     kuma layi ɗaya gare su.

 

     MISALI NA (10).

 

     Nokia 1110 da 1030 da 105.     

 

5. Kifad mai layi biyu ko uku amma kuma suna burawuzin sai dai ba

     sosai ba.

     MISALI NA (11).

 

     Tecno 401 layi uku gare ta, kuma tana burawuzin amma kaɗan wato

     ba ta da sauri wajen yin burawuzin.

 

4.3.3.  (C) SIMBIYAN  (SYMBIAN).

     

Waɗannan wayoyi su ma sun kasu kashi biyu kamar haka;

1. kibod  (keyboard).

 

     MISALI NA (12).

 

     Nokia Asha 210, da Nokia 6300, da 6200.

2. kifad  (keypad).

 

     MISALI NA (13).

 

      Nokia E5, da E6.

 

    Duk waɗannan wayoyi ne da ake amfani da su domin yin kira, da aika saƙo ta hanyoyi dama musamman ta hanyar amfani da kafafen sadar da zumunta da kuma akasin haka. A taƙaice dai, wayoyi ne masu tsarin burawuzin sosai-da-sosai.

 

 

 

 

4.3.4. SUNAYEN DA AKE YI WA WAYOYI (BAHAUSHEN SUNA).

 

   Masu sana'ar waya kan yi wa wayoyi Bahaushen suna gwargwadon yadda waya ta samu karɓuwa ga mutane masu saya su yi amfani da ita. Amma kuma ba kowace waya ce take da Bahaushen suna ba. Hasali ma, wayoyin da ba su da Bahaushen suna sun kai kashi casa'in a cikin ɗari. Don haka, wayoyin da ake yi wa Bahaushen suna ba su taka kara suka karya ba. Amma dai duk haka, akwai wayoyi ƙalilan waɗanda ke da Bahaushen suna. Saboda haka; wayoyi masu Bahaushen suna sun haɗa da;

 

MISALI NA (14).

 

1.Tecno T528 ita wannan waya tana da sunaye da dama kamar haka;     

     -  Sha kiɗinka baƙauye

     -  Waken suya

     -  Rarara

     - ‘yar kwara

     -  A kori gionee

     -  Gurin manoma/ burin manoma.

     -  Gwanja.

 Amma abin lura a nan shi ne, wannan suna wato gwanja an fi amfani da shi a Kano duk da dai ko a nan garin Gusau akwai tsirarun mutane da kan kira ta da wannan sunan.

 

MISALI NA (15).

 

2.Gionee L800 ana kiranta da sunaye biyu kamar haka;

-  Dimɓaru

-  A shiga daji Fullo.

 

    MISALI NA (16).

 

 3.Itel 2160 ana kiranta da sunan fiyo wota (pure water).

 

     MISALI NA (17).

 

4. Itel 2625 tana da sunaye kamar su;

   -Gafara baro

   - Rarara.

 

      MISALI NA (18).

 

 5.Tecno 484 ana kiranta da sunan a kori Gionee.

 

     MISALI NA (19).

 

6. Itel 2160 ana kiranta da suna kamar haka;

   - Abba gida-gida.

 

      MISALI NA (20).

   

7. Tecno 474 ana kiranta da suna

     riƙe ta ka miƙa/ wuce.

 

     MISALI NA (21).

 

8. Nokia 1110. Ana kiranta da sunan tsitsiya.

 

     MISALI NA (22).

 

9. Nokia 1600. Ana kiranta da suna raka ni kashi.

 

 

 

4.3.5.  SUNAYEN DA AKE YI WA KUƊI A KASUWANNI  WAYA GUSAU

      

MISALI NA (23).

                         

   S/N            SUNA.           MA'ANA.

LAMBA

SUNA

MA’ANA

1.

Wan gig

Dubu ɗaya

2.

Wan giga

Dubu ɗaya

3.

Wan k

Dubu ɗaya

4.

Wantawa

Dubu ɗaya

5.

Kilo daya

Dubu ɗaya

6.

Wanlet

Dubu ɗaya

7.

Guda

Naira  ɗari

 

   Abin lura a nan shi ne, duk waɗannan sunaye ana yi wa takardar kuɗi ta naira dubu ɗaya ne a kasuwanni da kantuna ko shagunan wayoyi a cikin garin Gusau da kewaye. Bugu da ƙari, masu sayar da manya-manyan wayoyi musamman ƙirar anduroyid kan yi amfani da waɗannan kalmomi domin gudanar da cinikayya a tsakaninsu da ‘yan kasuwa ire-irensu. Domin kuwa, ba kasafai ake yin amfani da ire-iren waɗannan kalmomin ba a yayin gudanar da ciniki a tsakanin  mai sana'ar da kuma mai saye ya yi amfani da waya ba.

 

4.4  KALMOMIN DA AKE MAFANI DA SU WAJEN SANA’AR WAYA A

        GUSAU.

Masu sana’ar waya a garin Gusau musamman masu cin kasuwanni daban-daban cikin garin Gusau kewaye kan yi amfani da wasu kalmomi domin ɓatar da bami a yayin gudanar da kasuwancinsu na yau-da-kullum. Saboda haka, wannan binciken ya yi kokarin kalato wasu daga cikin kalmomin da masu sana’ar waya ke amfani da su a yayin cinikyya kamar yadda za mu gani  a nan;

MISALI NA (24).

 S/N         KALMA             MA’ANA  

LAMBA

 

KALMA

 

MA’ANA.

 

1.

Ranƙam

 Matattar waya.

2.

Jini

Kuɗi.

3.

Shaƙe

Mutum ya sayi waya da tsada amma kuma ba ta da lafiya.

4.

Darasi

 Saɓa alƙawari/ alƙawali.

5.

Kilin(clean)

 Wayar da ba ta da kowane irin naƙasu.

6.

Kurciya

 Mutum ya gudu da waya.

7.

Zana masa

 Faɗa masa farashin wayar/ ko kuma faɗa masa kuɗin wayar.

8.

Tsamiya

Kuɗi.

9.

Guduma

Waya mai girma sosai wato babbar waya.

10.

Chaina

Waya mai ƙara sosai musamman  ƙananan wayoyi masu kifad.

11.

Babbar waya

Waya mai tsada ko mai daraja sosai.

12.

Makaranta

Ƙaddara maras kyau ta sami wani mai sana’ar waya.

13.

Ɗaya

Naira ɗari (100) ko naira dubu (1000).

14 .

Rabi

Naira hamsin (50) ko naira ɗari biyar (500). Ya danganta da yanayin maganar da ake yi a yayin ciniki.

15.

 Ƙetare

Da an ce ƙetare, ana nufin kar ka sayi wayar da kake yin ciniki.

16.

ƙundu

Bandur ɗin kuɗi.

17 .

Sumuni

Dubu ɗari.

18.

Ankare

Da an ce ankare ana nufin ɓarawo ne zaka sayi waya a hannunsa.

19.

tsallake

Kar ka sayi wayar nan, domin wayar za ta yi wahalar sayarwa saboda an bar yayinta.

20.

Jagwal

Waya maras lafiya sosai

                                      

4.5. JIMLOLIN MASU SANA'AR WAYA A GUSAU.

 

MISALI NA (25).

 

S/N  JIMLOLI              MA’ANA

 

1.

Kawo ɗai da rabi.

 Ba ni naira ɗari da hamsin (150).

2.

 Ba ni goma da rabi.

Ba ni dubu biyu da naira hamsin (2050).

3.

Ba da talatin da biyu.

Kawo naira dubu uku da ɗari biyu (3200).

4.

Ba da sha biyar.

Ba da dubu ɗaya da ɗari biyar (1500).

5.

Kilo ɗaya da rabi.

Dubu ɗaya da ɗari biyar (1500).

6.

Kawo sittin.

 Bada dubu shida (6000).

 

 

    Saboda haka, a wajen Hausar masu sana'ar ƙananan wayoyi musamman masu sayar da waya kifad (key-pad), idan aka ce ɗai ana nufin naira ɗari (100). Amma kuma a wajen masu tu'ammali da anduroyid sukan yi amfani da kilo, da giga, da tawa da dai sauransu. Bugu da ƙari, masu sana'ar waya musamman manyan wayoyi suna amfani da sunayen yan ƙwallo musamman idan za su sayi waya a hannun wanda ba sana'ar yake yi ba. Alal misali, idan wani ya kawo wayarsa zai sayar wa wani ɗan waya, sai ya saya dubu ashirin da biyar, idan ba a sayar masa ba  zai nemi shawarar wani daga cikin abokan sana'arsa a kan ya ƙara ko kar ya ƙara daga abin da kuɗin da ya saya. Sai ya ce masa;

 

MISALI NA (26).

 

1.

Wa zai yi yawo a nan?

 Wayar nan za ta yi nawa?

2.

Ka sa mata Chilwell

Ka saya dubu ashirin da ɗaya.

3.

Akwai alheri cikin Chilwell

Idan na saya dubu ashirin da ɗaya zan samu wani abu?

4.

Akwai na kai cikin Chilwell

 Za ka samu wani abu idan an bar maka hakanan, ka saya.

5.

Akwai nawa nan?

Za a sayar min da wannan wayar?

6.

Gaskiya ba naka ciki

Baka iya sayenta.

7.

Akwai na kai?

 Zan samu wani abu nan?

8.

Ya kaga wannan huɗɗar?

 Kana ganin wannan wayar za a samu nawa?

9.

Huɗɗ mai kyau

Cinikin da aka samu riba sosai.

10.

Huɗɗar banza

Cinikin da ba a ci riba ba.

11.

Matattar huɗɗa

Ɗan kasuwa ya sayi wayar da bai ci riba ba, a maimakon haka sai ya faɗi.

12.

Ya tsallake da ƙyar.

Ya yi kuren tafka asara a kan wata waya.

 

 

 

4.6   NAƊEWA.

Hausawa kan ce:” sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba”. Hakazalika, masu iya magana na cewa: “ inda rai, wata rana jariri  ango ne”. Kamar dai yadda aka sani cewa duk abin da ya yi farko, tabbas zai yi ƙarshe, laakari da matakin da aka kawo a wannan babin, za a iya cewa wannan bincike ya cimma ga ci ko kuma ace haƙa ta cimma ruwa. Bugu da ƙari, bayanai sun gabata dangane da  wuraren da ake sayar da waya a Gusau kama daga tsofaffin wurare da sababbin wurare. Hakazalika, an yi tsokaci kaɗan a kan masu sana’ar waya a Gusau. Bayan haka, an rattabo ire-iren wayoyi da sunayensu na Hausa. Daga ƙarshe kuma, an zayyano kalmomi da jimloli waɗanda masu sana’ar waya ke amfani da su a wajen harkokin kasuwancinsu na yau-da-kullum.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

BABI NA BIYAR.

SAKAMAKON BINCIKE.

  5.O. SHIMFIƊA.

  Wannan babi  shi ne babi na ƙarshe, wanda ke nuna kammaluwar wannan kundin bincike wanda aka gudanar a kan ‘’ Rukunin Hausar Masu Sanaar Waya a Garin Gusau’’. Kamar yadda bayani ya gabata, wannan kundin bincike an rarraba shi zuwa babi-babi. A kowane babi akwai bayanai da dama tun daga babi na ɗaya har zuwa babi na huɗu. A  wannan babin kuma, wato babi na biyar an tattauna ne a kan sakamakon bincike da kuma shawarwari daga ƙarshe  taƙaitaccen bayanin naɗewa.

5.1. SAKAMAKON BINCIKE.

  A  lokacin da aka kawo ƙarshen wannan bincike, an gano cewa sana’ar waya tana da matuƙar muhimmanci da amfani sosai ga alummar Hausawa musamman a ɓangaren sadarwa da kuma ƙarin ƙarfin tattalin arziƙi ga su kansu masu sanaar, da wasunsu, da jiha dama ƙasa baki ɗaya.

    Haka kuma, bayan kammaluwar wannan bincike, an gano wasu wurare muhimmai waɗanda ake sana’ar sayar da waya a cikin garin Gusau kama daga tsofaffin wuraren da aka fara sayar da wayoyi can da; da kuma sababbin wuraren da ake sayar da wayoyi a yanzu a Gusau.

  Binciken ya tabbatar da cewa, wayoyin salula suna da wasu rukunai waɗanda suka bambanta wayar wani rukuni da ta wani rukuni na daban musamman a kan abin da ya shafi ayyukansu. Wato waya ta wani rukuni tana da wasu abubuwan da take iya yi wadda ta wani rukuni ba ta iya yin su.

Daga cikin sakamakon wannan bincike akwai gano waɗansu sunaye da masu sana’ar waya da kuma masu saya domin su amfani da ita kan yi wa wayoyi wato    (Bahaushen suna) dangane da yadda waya ta samu karɓuwa ga jama’a masu saya domin amfanin kawunansu kamar yadda aka bayyana a baya.

     Hakazalika, an gano cewa, wannan sana’a ta sayar da waya ta samar da sabuwar Hausa ga harshen Hausa da Hausawa musamman mazauna garin Gusau da kewaye.

Haka kuma, daga cikin abubuwan da aka gano a lokacin da aka kammala wannan bincike, an gano cewa  masu sana’ar sun samar da sunaye sababbi waɗanda sukan yi wa kuɗi baya ga sunayensu na ainihi ko asali musamman dubu ɗaya (1000), da naira ɗari biyar (500), da naira ɗari (100), da kuma naira hamsin (50) a yayin gudanar da hada-hadar kasuwancinsu.

     Bugu da ƙari, binciken ya samu nasarar gano waɗansu keɓaɓɓun kalmomi da masu sana’ar waya kan yi amfani da su a tsakaninsu ta hanyoyi daban-daban a lokacin da suke sana’arsu kamar yadda bayani ya gabata.

  Har ila yau, binciken ya gano cewa masu sana’ar waya na yin amfani da jimloli na fannu wato keɓaɓɓu a yayin gudanar kasuwancinsu da sauran hulɗoɗinsu na yau-da-kullum a wajen sana’arsu.

Hakazalika, an gano gudunmuwar sunayen ‘yan ƙwallo musamman Turawa wajen samar da sababbin kalmomi da jimloli a lokacin da suke gudanar da cinikin waya a tsakaninsu ( masu sanaar waya) da kuma kwastomominsu.

5.2 SHAWARWARI.

Hausawa kan ce: ‘’ Mai shawara aikinsa ba ya ɓaci, sai dai kuma babu sirri a cikin al’amuransa’’. Babu shakka harshen Hausa yana ƙara ɗaukaka da bunƙasa a duniya gaba ɗaya wanda wannan kuma ba ƙaramin ci gaba ne ba ga harshen.

     Kasancewar yaɗuwar da harshen Hausa ke yi da al'ummar Hausawa zuwa lokaci zuwa lokaci yasa ana samun keɓancewar jama'a zuwa rukuni-rukuni daban-daban. Wannan ya haifar da samuwar Hausar rukuni na wasu jama'a waɗanda suka keɓe kansu a wani muhalli na daban tare da samar da wata maganar da ta keɓance su. Hakan yasa a yanzu an samu wata sabuwar Hausa a garin Gusau wadda aka samu sanadiyyar zuwan wata sabuwar sana’ar zamani a ƙasar Hausa da kuma jihar Zamfara wato sanaar Waya.

   Zuwan wannan sana’a ne yasa aka samu sabuwar Hausa fil ta masu sana’ar, wato ‘’ Hausar Rukunin Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau’’. Saboda irin wannan yaɗuwar da wannan harshen Hausa ke yi yasa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a cikin waƙarsa yake cewa:

                       ‘’ Yau harshenmu ya zamo gagara badau,

                           Furce Afirika har ƙasashen Turawa’’. ( Bunza.2004)

   Bugu da ƙari, harshen Hausa ya samu karɓuwa a ƙasashen duniya musamman a Jamioi, da kafafen yaɗa labarai, da kafafen sada zumunta musamman a yanar gizo.

Saboda haka, an yi amfani da wannan damar domin bayar da shawarwari tare da jawo hankalin ‘yanuwa musamman ɗalibai domin a ƙara bunƙasa harshen ta hanyar nazarin harshen Hausa a makarantu daban-daban musamman a manyan makarantun gaba da sakandare.

     Shawara ta farko ita ce, ɗalibanmu na wannan lokaci  su yi ƙoƙari su riƙa zaɓar harshen Hausa a matsayin abin da za su yi nazari akai idan za su tafi makarantun gaba da sakandare, wannan shi zai  ƙara bunƙasa harshen.

Shawara ta biyu ita ce, masu gudanar da bincike musamman ɗalibai, idan za a yi nazari ko bincike a kan wani abu daga sassa ko rassan Hausa guda uku wato Harshe, da Adabi, da kuma Al’ada, ya kamata a tsaya tsayin-daka a natsu tare da bin ingantattun hanyoyi domin gudanar da bincike mai inganci da nagarta. Bugu-da-ƙari, a riƙa yin amfani da harshe mai sauƙi domin samun sauƙin fahimta.

 Shawara ta uku ita ce, kira ga ɗalibai ‘yan’uwa gabaɗaya musamman masu nazarin harshen Hausa da su ƙara faɗaɗa karatu idan an samu dama.

  Haka kuma, ana ba da shawara zuwa ga malamanmu na wannan sashe mai albarka, wato sashen nazarin harsuna da al'adu, da su ƙara ƙaimi da ƙoƙari a kan wanda suke yi domin ganin samun nasarar ɗalibansu da su kansu kamar yadda suka saba.

  Shawara ta ƙarshe ita ce, zuwa ga masana, da masu ruwa da tsaki, da kuma masu shawa da harshen Hausa su riƙa ɗaukar nauyin wasu ɗalibai suna tura su jami’o’i daban-daban na gida da na waje domin nazarin harshen Hausa, da kuma ɗaukar nauyin buga littattafai da rarraba su zuwa makarantu da ɗakunan karatu na makarantu daban-daban.

 

5.3. NAƊEWA.

Hausawa kan ce, ’’ Komai nisan jifa, ƙasa za ta faɗo’’. Haka kuma, masu iya magana na cewa, ’’ Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba’’. Alal haƙiƙa, komai ya yi farko tabbas zai yi ƙarshe. A nan ne cikin ikon Allah da iyawarsa ya ƙaddara naɗe tabarmar wannan kundin bincike mai taken ''Rukunin Hausar Masu Sana’ar Waya a Garin Gusau’’.

   A babi na farko wato gabatarwa , an yi tsokaci a kan  manufar bincike, da hasashen bincike, da kuma farfajiyar bincike. Haka kuma, an tattauna a kan matsalolin bincike, da muhimmancin bincike. A ƙarshen babin kuma aka yi bayanin hanyoyin da aka bi a yayin aiwatar da wannan bincike.

   A babi na biyu, an yi bitar wasu ayyuka da suka gabaci wannan kundin bincike. A babin, an yi bitar ayyukan da suka gabata, kama daga duba bugaggun littattafai, da kundayen bincike na digiri na ɗaya zuwa na uku. Bugu da ƙari, an waiwayi wasu maƙalu waɗanda suka gabata masu alaƙa da wannan kundin bincike. Daga ƙarshe kuma, an yi bayanin hujjar ci gaba da bincike da kuma jawabin naɗewa.

 Yayin da a babi na uku, an tattauna a kan tarihin garin Gusau ta Sambo, da ma’anar sana’a, da rabe-ben sana’a, da kuma muhimmancin sana’a. Hakazalika, an bayar da ma’anar sadarwa, da rabe-raben sadarwa. Haka kuma, an bayyana ma’anar wayar salula, da samuwar wayar salula. A ƙarshe, an rattabo amfanin wayar salula tare da  kuma wasu illolin wayar salular ta haifar.

  A babi na huɗu kuma, an fara bayyana wuraren da ake sayar da waya a Gusau, da wuraren da aka fara sayar da waya a Gusau, da kuma wuraren da ake sayar da waya a Gusau a yanzu. Haka kuma, an yi bayani a kan masu sana’ar waya a Gusau, da ire-iren wayoyi kama daga: anduroyid, da kifad, da kuma simbiyan. Bugu da ƙari, an bayyana sunayen da ake yi wa wayoyi na Hausa, da kuma sunayen da ake yi wa kuɗi a kasuwannanin wayar Gusau. A ƙarshen babin kuma, an rattabo kalmomin da ake amfani da su wajen sanaar waya a Gusau, da jimlolin da masu sana’ar kan yi amfani da su a wajen sana’arsu tare da taƙaitaccen bayanin naɗewa.

A babi na biyar, wato babi na ƙarshe a wannan bincike, an bayyana sakamakon wannan bincike tare da ba da wasu shawarwari. A ƙarshe kuma, aka naɗe tabarmar wannan kundin bincike tare da manazarta.

 

MANAZARTA

Abdulƙadir, M. (2018). Hausar Rukunin ‘Yan Banga a Garin Gusau. Kundin Neman Digirin Farko A Jami’ar Tarayya Gusau.

Abubakar, A.T (2015).  Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria Nothern Nigerian Publishing Company.

Al-hassan, da wasu (1982). Zaman Hausawa. Lagos Islamic Publication Bureau.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary. London. Oxford University Press.

Bayero, J. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyayar  Nazarin Harsuna Nijeriya, Jami’ar Bayero.       

 Bunza, A.M. (2004). Waƙaƙen Ƙaidojin Rubutun Hausa. Lagos Ibrash Islamic Publication Center ltd. 51 Adelabu Street, Surulere.

Bunza, A.M (2017). Dabarun Bincike. Zaria, Ahmadu Bello University press Limited.

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancin sa ga Rayuwa Hausawa. Kano: Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur.

Ɗanlami, H.(2019).   Birkila Mesin a Garin Kwatarkwashi. Kundin bincike na Neman digiri na farko, a Sashen Nazarin Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

East, R.M (1968). Labaru na da da na yanzu. Zariya: Nothern Nigeria Publication Company.

Fagge, U.U. (2001). Ire-iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, G.U. (2012). Bukukuwan Hausawa. Gusau. Ol-Faith Prints Gusau.

Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano. No 29 Benchmark Publishers L.T.D.

Isah, S.F, da Musa, A. (2020). Language Switching Between Yoruba and Hausa’s In Ƙaura Namoda, Zamfara state. Fourth National Comfrence On Zamfara Kingdom. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan-Nigeria. Spectrum Books Limited, Ring Road.

Newman, R.M (1974). Dictionaries of the Hausa Language. HN 4:1-25.

Salihi, T.M (2012). Sakace A kan Karin Harshen Hausa. Absur Comprint. F.C.E, Kano.

Salihu, N.A (1987). Code Switching among University of Sokoto Hausa-English Bilingual. Kundin binciken digirin farko a Sashen Nazari Harsunan Nijeriya: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.

Shehu, M. da Aliyu, L. (2020). Tasirin Wayar Salula Wajen  Gurɓata Rayuwa Hausawa a Yau. Maƙala a Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi: Adamu Augie, Kebbi. 

Yahaya, I.Y, da wasu (1992).  Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi na biyu. Ibadan: University press Plc. Ibadan-Nigeria.

Yahaya, I.Y. (2002). Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: Kamfanin Buga Littafai na Nijeriya ta Arewa.

Yahaya, S. (1998). Hausa a Jami’a. Kundin Neman Digirin Farko A Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.

Yakasai, S.A. (2012). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto- Nijeriy Garkuwa Media Services L.T.D. Gida mai Lamba 52 Layin Sarki Yahaya.

Zarruƙ da wasu, (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire. Littafi na Biyu. Ibadan-Nigeria. University Press P.L.C.                            

Zarruƙ da wasu, (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire. Littafi na Biyu. Ibadan-Nigeria. University Press P.L.C.

Zurmi, Y.S (2010). Matakin Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. (Babu maɗaba’a).

 

FIRA/ TATTAUNAWA.

 

Ali Abbas mai sayar da a Kasuwannin wajen garin Gusau. Ranar 08/03/2020.

Ali Rodi mai sayar da Waya a Gusau. Ranar 17/04/2020 da ƙarfe 10:00 zuwa 11:30.

Hamza Muhammad Ladan mai sayar da Waya a kasuwar Bebeji Plaza. Gusau. Ranar 18/09/2020 da ƙarfe 4:00 zuwa 6:00.

Nasuru Aminu Sakatare na masu sayar da Waya a Kasuwar Bebeji Plaza, Gusau. Ranar 27/02/2020 da ƙarfe 2:00 zuwa 4:30, da 28/02/2020.

Nuhu Ibrahim Kotorkoshi mai sayar da Waya a Gusau. Ranar 12/03/2020, da ƙarfe 12:00 zuwa 1:30, da ranar 15/03/2020 da ƙarfe 11:00 zuwa 12:30.

 

Post a Comment

0 Comments