𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam Barka da safiya. Malam don Allah meye matsayin Azumin Wanda baya Sallah kwata kwata, amma kuma zai ɗauki Azumi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Wanda ba ya sallah ba'a karɓar aikinsa na azumi ko
zakkah ko hajji, ko duk wani aiki.
Imamul bukhari yaruwaito hadisi (520) daka buraida ya
ce: Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce:( Duk wanda ya bar sallar
la'asar hakika ya rusa aikinsa).
Ma'anar ya ɓata aikinsa shi ne ya rushe ba zai amfane shi ba,
wannan hadisi yanuna wanda baya sallah ba'a karɓar aikinsa, wanda baya
sallah ba zai amfana dakomai na aikinsa ba, aikinsa ba za a kaishi zuwa ga
Allah ba.
Ibnul ƙayyeem rahimahullah ya ce:
dangane da ma'anar wannan hadisin acikin littafinsa Assalah (65) " Abun da
ya bayyana acikin hadisin, barin sallar iri biyu ne, barin sallah na har abada
shi kwata kwata bayayi wannan yana ɓata aikinsa gaba ɗaya, da kuma barinta na wani
lokaci kamar wuni guda sananne wannan yana ɓataa aikinsa na aiya wannan
yinin, Barin sallah gaba ɗaya shike lalata aikinsa
gaba ɗaya, barinta na wata rana yana ɓata aikin wannan ranar ko
ranakun dabaya sallar.
An tambayi Shaik Usaimin acikin fatawarsa (87) game da
hukuncin azumin wanda baya sallah. Sai ya amsa; Wanda baya sallah azuminsa ba
ingantacce bane ba karbabbe bane, domin wanda baya sallah kafirine wanda ya yi ridda
saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki a Suratul
Tauba aya ta 11:
فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ ۗ
Idan sun tuba sun tsai da sallah sun bada zakkah to
sun zama 'yan'uwanku a'addini.
Da faɗin Annabi sallallahu Alaihi
wasallam ( Banbanci da ke tsakanin musulmi dawanda bashiba shi ne yin sallah
wanda ya bar sallah hakika ya kafirta) Turmuzi ( 2621) Albani ya inganta shi acikin sahihu turmuzi.
Saboda kuma shi ne maganar sahabbai gaba dayan imma
baizama ijma'insu akaiba, Abdullahi bin shaƙeeƙ rahimahullah yana cikin tabi'ai wadanda suka shahara ya ce:
Sahabbai sunkace ba sa ganin wani aiki cikin ayyuka wanda barinsa kafircine
inba sallah ba, a bisa wannan idan mutum ya yi azumi kuma baya sallah to
azuminsa anmayar masa ba za a karɓa masaba, kuma ba zai amfane
shiba ranar alkiyama, zamuce da shi yi sallah sannan kayi azumi, amma kai azumi
baka sallah azuminka ba karbabbe bane za a mayar maka saboda kafiri ba'a karɓar duk wata ibada tasa.
An tambayi malaman lajnatul da'imah (10/140) tambaya
kamar haka: idan mutum yakanyi kwada yin yin azumi kuma yana sallah da azumi
amma kuma dazarar azumi yawuce shikenan ya dena sallah, shin yana da azumi? Sai
suka amsa: sallah rukunice daga cikin rukunan musulunci muhimmai wanda daka
kalmar shahada sai ita, tana cikin farillai na tilas wajibi, duk wanda ya bar sallah
yana maikore wajabcinta ko kuma saboda wula kantata ko saboda kasala hakika
yakafirta, amma masu azumi suna sallah acikin azumi kawai waɗannan suna yaudarar Allah
ne, tir da mutanen dabasu san Allah ba sai awatan azumin Ramadan, azuminsu bai
ingantaba tare dabarin sallarsu alokacin da ba na azumi ba, sudin kafiraine
kafirci babba, koda basu kore wajabcin sallar ba amafi inganci maganganun
malamai.
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.