Mijinta Yana Shaye-Shaye Ba Ya Kula Da Ita, Sai Ta Fara Kula Tsohon Saurayinta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Aslm. Malam ya ƙoƙari? Wallahi ina cikin damuwa, Yar'uwa ta ce za ta jefa kanta cikin halaka da auranta, wlh malam ni nasan tana cikin damuwa tun ba yanzu ba tun da komai tana gayamin nice me ba ta haƙuri kuma hadda shi na sha yin sulhu, auran shekara 2 ke nan kuma ba tare suke da mijin ba sai weekend yake zuwar mata amma duk zuwan nan nashi fa har ya tafi ba Shi da lokacinta ko da yaushe yana joint na shan SHISHA har cikin dare, ita da iyayenshi wallahi sai fama suke a kan wannan halin nashi amma yaki bari babanshi har baki ya ce zai mishi amma yaki ya yi hankali ya daina, yanzu dai jiya ma tace min ta kamashi da kwaya a gidan, kuma haƙuri idan ya dawo hankalinshi ba irin wanda ba ya ba ta sai ya ce ta yi ta mishi addu'a zai bari amma fa har yau bai taɓa ƙoƙarin daga kafa ba, dama zancen hakkinta na aure sai idan ta nema shi ma sai in yana hayyacinshi da safe don bacci kawai yake zuwar mata gidan kuma tana masa complain dan tace tana cutuwa dan Allah ya yi ta mabukaciya ce dan tace rashin sa a tare da ita har blue film take gani, yanzu dai malam inda matsalar take wallahi har ta fara kula tsohon saurayinta suna waya shi ma kuma yana da aure kaddara ce ta raba su basu auri juna ba, kuma a binciken da na yi har sun fara shirin yadda za su haɗu, wallahi malam a yadda nasan soyayyar da sukai a baya komai zai iya faruwa wallahi za ta bashi kanta su lalace ne dan Allah malam meye shawara duk da jiyan na mata faɗa sosai kuma na ba ta rashin gaskiya amma da abin na kwana Wallahi. Mijinta komai yana mata na dawainiyyar da Allah ya dora mishi ba ta rasa komai ba wallahi sai wannan matsalar tashi yaki ya gyara..

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Da yawa Mata sun Tsinci Kansu cikin irin wannan Mawuyacin halin na Rashin Tarbiyyar Mazajensu. Sakamakon Addu'ar iyaye da Addu'ar Waɗannan Matan nasu kuma Cikin Taimakon Allah sai kiga sun Gyaru, sun shiryu sun dena Abin da suke yi na shaye-shaye ko Shiririta. Sabida Haka Abin da ya dace shi ne ki Dukufa da yi Masa Addu'ar Shiriya ke da iyayensa. Lokaci ɗaya sai kiga ya zama Mutum Kamili ya dena duk Abin da yake yi. Wannan shi ne Nawa Shawarar. Tinda ba ya dukanki. Baya Wula kanta Ki, baya hana ki Ci da Sha da sauran Haƙƙoƙinki. Da a ce kafin Aure ne, zan baki shawara a kan kar ki Aure shi. Amma Tinda kin riga da kin Aure shi kuma har da yara. Ga shi Kuma Baya Wula kanta Ki, baya tauye miki Hakkinki na Auratayya. Ina ga sai a yi Haƙuri ake yimasa Addu'ar Shiriya. Sai dai fa idan yana dukanki ko yana Gaya Miki bakaken Maganganu za ki Iya cewa ya sake ki. A nan Baki yi wa Allah Lefi ba. Sabida haka acigaba da Addu'a.

    Maganar Kula Wani Saurayi Kuma bayan Aurenta da Wani ai Bai Wuce Hauka ba da kuma Rashin Tunani. Ina mamakin Mata. Sabida ta yaya wani yana Ikirarin yana cewa yana son ki kuma Bai Aureni ba. A Haka wani ya Rufa Miki Asiri ya Aureki. Amma kuma kina harin wanda bai Aureki ba.? Wannan zaisa ki Wula kanta Aurenki, ki Wula kanta Rayuwarki, Ki Wula kanta Rayuwar 'yayanki. Ki bar Musu Abin Magana. Har a gidan Aurensu. Domin in kika sake aka kai Diyarki gidan Kishiya. Alhalin kin taɓa aikata wani Abin Kunya da wani Namiji daban wanda ba Mijinki ba. Wallahi sai wannan kishiyar taki ta sami Labari, kuma an dinga yi wa Diyarki Habaici a kan wannan. kin ga ke nan kece kika wula kanta Diyarki.

    Ga Kuma Azabar da za ki Haɗu da ita a Lahira. Sakamakon Abin da Kika Aikata. za ki Rayu a duniya Kuma Kina cikin Fushin Allah. Ai Masifar ta yi Yawa. Kuma duk Namijin da ya yi Iskanci da ke. To zai Iya yi da Kowacce Kalar Mace. Ma'ana zai Iya Yin Iskanci da lafiyayyiyar Mace da wadda ma ba Lafiyayyiya ba. Wanda kuma zai Iya dakko wannan Jinyar ya Goga Miki. Ke kuma ki Gogawa Mijinki na Asali. Masifa Kan Masifa ke nan.

    Allah ya Gyara Halayenmu. Ya kare mu, ya kare Mana 'yayanmu da Matan Mu da Gidajen Mu.

    Allah shi ne Masani.

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.