Motar da nake ciki baƙaƙen gilasai gare ta waɗanda ake yi wa kirari da fa’illan takun tarahu... Gaba tsaro, baya tsaro... Kai! Mulki da daɗi!
Atishawar da na yi ta katse
mini tunani. “Yarhamakalla ranka ya daɗe.” Mai tuƙa ni ya faɗa duk da ban
ambaci komai ba. Na ci gaba da kallon talakawa da ke gefen hanya. Wasu na faɗin:
“Sai ka yi takwas...” Wasu na cewa: “Ba ma yi...!” Jami’an tsaro kuwa na famar
musu korar kare. “Htch” na sake. “Kai! A wannan lokacin korona?” Na raya a
zuciyata. Na daidaita zaman takunkumin da ke fuskata.
“Htch! Htch! Htch!”
Daga jeranton atishawa sai na ɓarke da tari mai tsanani. Cikin gaggawa ɗan
sandan da ke zaune gefen mai zaman banza ya sadar zuwa sauran motocin da
ke cikin taragon rakiyata: “Honorable is in unsual situation. Do you copy?”
Idanuwana suka daina
kallon komai sai wasu baƙaƙen halittu masu jajayen idanuwa mai kama da
garwashi. Gabana ya ba da ras! Ɗayansu ya daka mini tsawa: “Ciro rayinka da
kanka!” Sautin muryar ya fi rugugin aradu. Nan na ji wani abin da ba zan
iya fasalta shi ba. Tamkar dai duka jijiyoyin jikina sun tsittsinke. Kowane
ƙofar gashin jikina kuma kamar an soka allura.
Mutanen nan suka
matso. Kowannensu yana hucin wuta mai tsananin zafi. Suka fara tsintar wani
farin abu da ya warwatse a jikina. Ciran kowane ɗayansu ya fi yankan wuƙa zafi.
Na fara buge-buge da wafce-wafce. Na jiƙe wandona da fitsari.
Ban sani ba ashe mun
iso gidan gwamnati. Likitocina na kewaye da ni yayin da ake ta rirriƙe ni. Sai
dai ina... ƙaddara ta riga fata. Kafin a yi wani yunƙuri na ce ga garinku nan!
Wai korona ce ta kashe ni, don haka ba za a mini wanka ba.
Baƙaƙen mutanen suka
nufi sama da farin abin da suka tsittsince a jikina bayan sun lulluɓe da wani
bargo baƙi mai zafi da ƙayoyi. Can sai ga su sun dawo da abin dai riƙe a hannuwansu. Sai ga ƙasa ta buɗe. Suka luluƙa ciki
da shi.
***
Yanzu kam ba na iya
motsi, amma ina jin duk maganganu da ake yi kusa da ni. Ga mamakina, kowa sai
ya fara baya-baya da ni. Ko mai tuƙa ni a mota da yake ɗan ga-ni-kashe-ni gare
ni, sai ya ja baya. Amma ba damuwa... Na san ko da waɗannan sun ƙi ni, matana
da ‘ya’yana ba za su ƙi ni ba, musamman amaryata Zee.
Kafin in gama tunani
kuwa sai ga su. Daga nesa suka tsaya. Uwar gidata tana ta faman share
hawaye. Zee kuwa, kamar ba ta damu ba. Ta zaro wayarta ta ɗauki hotona daga
nesa. Wani likita da ke kusa da su ya ce: “Hajiya za ku iya tafiya. Kun san
yanayin wannan cuta...” Ba musu suka juya suka nufi hanyar fita. Na yi mamaki!
Zee ba ke ce kika ce za ki so ni rai da mutuwa ba? Amma ko na tambaya ba ta ji
na. Wayyo ni! Kowa na gudun taɓa ni tamkar wata annoba. Waɗanda za su saka ni a
leda sai da suka yi wata shiga kamar doduna. Aka tsattsaya a tazara aka mini
salla. Aka doshi maƙabrta da ni. Hankalina ya ƙara tashi.
***
Na hango kabarin da
aka tona. Wuta ce ke ci a ciki tamkar gobarar daji. Na fara kururuwa. Duk da
haka ba sa ji na. Ba dama in yi motsi. Da aka matso kusa, na hango macizai da
kunamai a ciki. Tsananin tashin hankali ya sa na fara tunanin halayyana tun
daga yarinta har zuwa
yau. Sai yanzu na gane annabi-ya-faku. Yau ne kaɗai na yarda da cewa ƙarshen
alewa ƙasa. Aikina na ƙarshe yaudara ce. Na tuna kalamaina na ƙarshe ga
talakawa: “Mun fitar da maƙudan kuɗi domin yaƙi da korona...” A haƙiƙanin
gaskiya kuwa kwarona farin ciki muka yi da zuwanta. Dalili shi ne ta samar mana
da hanyar ƙafar ungulu da kuɗaɗe cikin ruwan sanyi.
Na tuna adadin
dukiyata. Ni da kaina abin ya ba ni takaici. Na kasa gane da ko ni wawa ne ko
mahaukaci? Haƙiƙa dukiyata ta kai in ci da mutane ɗari na tsawon shekaru ɗari.
Kash! Ban yi aikin neman lada da ita ba sai ma ƙoƙarin neman ƙari da nake yi.
Wai me ya toshe min ƙwaƙalwa ne? Lallai ko “duniya mai idanu a tsakar ka.” Ko
ba komai dai na san iyalaina za su yi ta sadaka da ita da sunana. Ladan zai
biyo ni kabari.
Na ci gaba da kururwa
yayin da balbalin bala’in da ke fita daga ciki ya fara bugu na. Su ba sa kallon
komai. Suka turbuɗe ni. Suka watse. Kabari kuwa ya matse ni. Na ji wani tashin
hankalin da ya fi ƙarfin tunani. A nan na tuno da dukkanin labaran da nake ji
game da rayuwa bayan mutuwa. Kaico! Da-na-sani ƙeya ce!
***
Wani baƙin mutum mai
ban firgici riƙe da ƙatuwar guduma ya bayyana tare da wata ƙara mai rikitarwa.
Ya tambaye ni cikin murya mai kaushi: “Wane ne Ubangijinka?” Ruɗewa da razana
suka ɗauke duk wani sani nawa. Ya danƙara mini gudumar hannunsa sai da na nutse cikin ƙasa. Ƙasa kuwa
ta watso ni waje... Ashe da gaske ne a lahira ba a mutuwa.
***
Yau a matsayin fatalwa
na fito. Kai tsaye na nufi gidana, wato gidan gwamnati. Burina shi ne in ga me
ya dakatar da iyalaina ba su fara sadaka da dukiyata ba ko zan samu sauƙi? Na
wuce ta babban ɗakin taron da ke gefen gidan gwamnati. Na tuna lokutan da aka
yi ta gayyata na tarurrukan gwangwajewa. Ina ma a ce zan iya musu wa’azi?
Na ɗan leƙa ɗakin
taron. A dandamalin da ke sama sai ga babban ɗana Abba da yarinyar nan da na
hana shi aura. Suna taka rawa ana musu yayyafin kuɗi. Kamar in je in tsinke shi da
mari, sai kuma na tuna ni fatalwa ce. Cikin takaici na ƙarasa gidan gwamnati.
Na dudduba amma iyalaina ba sa nan. Sati biyu kacal ashe har an maye gurbina!
Na kuwa gane wanda aka sanya. Wani tsohon abokin gabana ne da ake kira Alhaji
Nera.
Alhaji Nera na tare da wata
mata cikin ɗakin hutu. Na kunna kai ciki domin kallon ƙwaƙwaf. Me zan gani? Matata
ce Zee ke kishingiɗe gefen Alhaji Nera. “Kai shege ne.” Ta faɗa yayin da ta ba
shi hannu suka tafa cikin shewa. Ta ci gaba da magana: “Ka ga dabarar nan ta
yi. Ko wa dai ya san koronar ce ta kashe shi. Amma babu wanda zai yi tunanin
ina ya same ta. Ni da kaina na sanya masa takunkumin a fuska lokacin da zai
fita.” Ta ja numfashi.
“Hmm...” Alhaji ya
katse ta: “Yanzu dai ba wannan ba... kin san dai gadonsa ina da Kaso talatin.
Rayuwa kuwa za mu ci gaba kamar yadda muka fara da ke...” “Wallahi Alhaji ka
cika zalama.” Ta katse shi. Suka
sake tafawa cikin shewa... Ashe da matata aka haɗa baki aka ga bayana? Banza ba
ta kai zomo kasuwa. Da ma na san da walakin goro a miya. Ba don kuɗina ba kaɗai
take zaƙewa a soyayyata.
***
A sabon gidan da
uwargidata ta saya na sake tarar da sabon tashin hankali. Ɗakin yana cike da
mata yara da manya. Na gane fuskokin mafi yawa daga cikinsu. Su ne uwargidan
tawa ta sha fama da ni kan in bi musu hakkinsu game da mutuncinsu da aka ci ta
hanyar fyaɗe. Ta daɗe tana bi na domin mayar da hankali kan fitar da doka ta
musamman game da fyaɗen. A lokacin ba shi ne a gabana ba. Idan jifa ta wuce
kaina, to ta faɗa kan uban kowa. Wasu daga cikin waɗanda aka yi wa fyaɗen,
baƙin ciki ne ya kashe su.
Ina shiga ɗakin wasu
daga cikinsu suka taso. Ashe su ma fatalwowi ne. Na yi ƙoƙarin fita da gudu.
Suka kama hannuna na dama. Cikin firgici da gigicewa na fara ƙoƙarin ƙwacewa. Kowacce
daga cikinsu na ƙorarin mini magana:
“Alhaji lafiya?”
“Alhaji”
“Innalillahi wa inna
ilaihi raji’un!”
“Alhaji lafiya?”
A hankali sai na ji
muryoyinsu na juyewa suna komawa irin na uwargidata.
***
Firgigit! Na farka daga bacci. Tana riƙe da hannun nawa tana mini nasiha kamar yadda ta saba. Duk da yanayin sanyin ɗakin, na jiƙe shirgif da gumi. Da sauƙowana daga gado na yi sujada don gode wa Allah da ya nuna mini gaskiya tsirararta. Na ji tamkar na mutu ne da gaske na dawo. To ai gani ga wane ma ya ishi wane tsoron Allah ballantana ni da na ga zahiri.
Na kira mai tsara mini rubuce-rubuce. Na karanta jawabin da ya rubuta mini game da kuɗin korona. Na yi ajiyar zuciya. Na dube shi na ce: “Ka je ka tsara mini jawabin da zan gabatar wa ‘yan majalisu da kwamishinonina. Ƙumshiyar jawabin ya kasance wa’azi ne. Takensa kuwa ya zamto cewa mu ji tsoron Allah, domin akwai ranar ƙin dillanci.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.