Gudummuwa ga Ranar Rubutacciyar Waƙa ta Duniya, 21/03/2022.
Daga:
Rubutawa, Abubakar S Sabiu (Sarki Asuk)
MA'ANAR RUBUTACCIYAR WAKA.
Masana da dama sun bayar da ma'anar waƙa a cikin su akwai:
Ɗangambo (1981) ya bayyana rubutacciyar waƙa da cewa " wani saƙo ne da aka gina kan tsararriyar ƙa'ida ta baiti, dango, rairawa, kari (bahari) amsa amsa amo (ƙafiya) da sauran ƙa'idojin da suka shafi daidaita kalmomomi, zubinsu da amafani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a magana ba"
RABE-RABEN RUBUTATTUN WAƘOƘIN HAUSA.
Za a iya raba rubutattun waƙoƙin Hausa zuwa gida biyu.
1. Waƙoƙin ƙarni na 19
2. Waƙoƙin ƙarni 20.
1. Waƙoƙin ƙarni na (19) yawanci waƙoƙi ne da aka rubuta su da rubutun ajami ( rubutun Hausa cikin harufan larabci) Babban jigogin wannan ƙarni shi ne jigon addinin musulunci.
2. Wakokin ƙarni na (20) waɗannan waƙoƙi ne da aka rubuta su bayan zuwan turawa ƙasar Hausa. Kuma ana rubuta su ne da rubutun boko.
Babban jigon waƙoƙin wannan ƙarni shi ne harkokin al'amuran duniya duk da dai ana samun jigogin addini.
NAU'OIN RUBUTATTUN WAƘOƘIN HAUSA.
Rubutattun waƙoƙi iri-iri ne dangane da yawan ɗango ko ɗangwaye da suke zuwa a kowanne baitai, Misali:
1. Gwauruwa : wannan ita ce waƙa mai ɗango ɗaya.
2. Yar Tagwai: wannan waƙa ce mai ɗauke da ɗango biyu.
3. Mai ƙwar uku/musallasa : wannan ita ce wakar da take ɗauke da ɗanagwaye uku.
4. Mai ƙwar hudu/ Murabba'a: Wannan ita ce waƙar da take da
ɗanagwaye 4.
5. Mai ƙwar biyar/ muhammasa: wannan waka ce mai ɗango biyar.
6. Tarbi'i: wannan waƙa ce wadda tun asali take da ɗangwaye ba su kai hudu ba a kowane baiti, amma kuma daga baya aka yi mata ƙarin wasu ɗangwayen.
7. Tahamisi: wannan waƙa ce wacce tun asali ba mai kwar biyar ba ce, amma daga baya aka yi mata karin dangwaye ta koma mi kwar biyar.
ABUBUWAN DA WAƘA TA KUNSA.
Abubuwan da waƙa ta ƙunsa ko kuma take tattare da su kafin ta zama rubutacciyar waƙa sun haɗa da:
1. ƊANGO: dogon layin kowacce waƙa. Ma'ana duk layi daya shi ne ɗango ɗaya, sannan karshen kowanne ɗango ana yin waƙafi kafin a sakko na kasa.
2. BAITI: Yana nufin haduwar ɗangwaye da marubucin waƙa ya yi amfani da su wajan isar da sako guda daya tak. Watau kenan baiti yana nufin ɗangwayen da marubucin waƙa ya yi amfani da su dan ƙulla carbin tunaninsa.
3. AMSA-AMO KO KAFIYA: harafin da yake zuwa a karshen kowanne ɗango ko baiti shi ne kafiya. Ana so wannan harafin ya zama iri ɗaya a kowanne baiti.
Amsa amo kala biyu ne.
1. Amsa-amon ciki.
2. Amsa amon waje.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da rubutacciyar waƙa ta kunsa. Abin lura anan shi ne waƙa da magana da bambanci, ita waƙa rereta ake yi bisa wasu ƙa'idoji na musamman, shi kuma zance faɗarsa kawai ake yi ba tare da rerewa ba.
MANAZARTA
Diso A, H (2013) Tsokaci a kan Rubutattun Waƙoƙin Hausa.
Yahaya I.Y (1985) "Tarihin samuwa da haɓakar Rubutattun waƙoƙin Hausa"
Lakcar Aji Dr. Khamilu Ligal
1 Comments
Masha Allah rubutu yayi kyau kuma mun amfana
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.