Ticker

Taƙaitaccen Bayani A Kan Hukuncin Bikin Kirsimeti A Musulunci

Bikin kirsimti shine bikin da kiristoci suke yi da sunan tunawa da ranar haihuwar Annabi Isa (AS), wannan ranar kuwa ita ce 25 da watan Disamba sukan kuma hada da bikin shekuwa sabuwar shekara taa miladiyya,  sukan dafa abinci tare da shagali don murnar zagayowar wannan ranar ta haihuwarsa, sukan bada kyauta, sukan kuma hura wuta, wadda ayanzu sun zamanantar da shi, suna yin knock out, sukan hadu a shoci shocinsu suna ta ihu hade da tambele.

MAGANGANUN MALAMAI KAN BIKIN KIRSIMETI:

Imamu Malik da Ibn Ƙasim (RH) suka ce:

" MUSULMI YA NISANCI ABIN HAWA NA KIRSIMETI, IN DAI ABIN HAWAN DON KIRSIMETI NE, SUKA CE MAKHARUHI NE KAI MUSULMI KA HAUTA".

(Duba Iqtida'u Siradil Mustaqim 2/625 da Allami'u fil hawadis wal Bidi'u 1/492).

Wannan hukuncin ya haɗa da duk motar da aka tanadar don kai kiristoci garinsu, su yi kirsimetin, a matsayinka na musulmi bai kamata ka hau ba, kuma bai kamata ka tuka su a matsayinka na diraba ba.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (RH) ya ce:

"WANDA YA YI SHAGALIN KIRSIMETI IN DAI BAI TUBA BA, TO YA ZAMA KAFIRI, DOMIN YA YI DAI DAI DA SU, ALHALI ALLAH (SWA) YANA CEWA:

" YA KU WAƊANDA SUKA YI IMANI DA ALLAH KA DA KU RIƘE YAHUDU DA KIRISTOCI MASOYA, SASHINSU MASOYA SASHI, WANDA YA JIƁINCESU TO YANA TARE DA SU".

Ya ce: WANNAN AYAR HUJJA CE.

(Duba  Allami'u fil hawadis wal Bidi'u 1/492)

Imam Abu Hanifa ya ce :

" WANDA YA BA DA KYAUTA GA KAFIRI RANAR KIRSIMETI SABODA GIRMAMA RANAR, YA ZAMA KAFIRI".

 (Duba Fathul Bari 2/315.

Ibn Taimiyya ya ce :

"AN YI IJMA'IN CEWA HARAMUN NE ZUWA WAJEN KIRSIMETI, WANNAN ITA CE ABIN DA MAZHABOBIN NAN GUDA HUƊU ( ABU HANIFA DA MALIK DA SHAFI'I DA AHMAD) SUKA TA FI AKANTA".

(Duba Ahkamu Ahliz Zimma na Ibn Qayyim 227 – 527/2, da  Iqtida'u Siradil Mustaqim 2/425).

# HUKUNCIN CIN ABINCIN KIRSIMETI.

Ya halasta musulmi ya ci abincin Kirista ba tare da ya tambaye shi wa  ya yanka masa ba, madamar wannan abun halal ne a gare shi.

Amma dangane da abincin KIRSIMETI, wannan kam haramun ne, don babu wani malami daga cikin Malaman Sunnah da ya halasta cin abincin ranar Kirsimeti.

 (Duba  Ahkamul Kur'an na Alqady Abubkar Ibn Arabiy Al'andalusiy Al-Maliki cikin Suratul Ma'idah, Majmu'ul Fatawa na Usaimin 105/3, Iqtida'u Siradil Mustaqim).

Ya kamata mu Musulamai mu kula mu gane cewar ba wasa muka zo yi duniya ba, kuma muna da tsari wanda bai bukatar tsarin Kafirai, ya kamata mu gyara tsarin mu!

Wallahu Wa Rasuluhu A'alam.

Allah ya sa mu wanye lafiya.

Dan uwanku:

Muhammad Albani Misau

Post a Comment

0 Comments