𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum malam brka da asuba dftr an tashi lfy dan Allah inada tammbaya mijina ne to mu biyu ne agurinshi sai matar shi ta tafi gida wanka jego to wlh mlm tun lokacin da tatafi bai kara shiga dakina ba da sunan wai yadawo kasuwa kamar yadda yakeyi in tana nan saidai yashiga ya dauke abin da xai dauka yafita Amman jiya tana dawowa daga jegon sai yashiga dakinta ya yi adalci shin ko baiyi ba Allah yakarawa malam lfy
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikumussalam warahmatullah
Todai farko sai ki tambaye shi ko hakan yana da asali
a addini, domin akwai wadanda suke da tunanin gargajiya, wai idan mace daya tatafi jego
gidansu alhalin yana da wata matar sai ya daina shiga dakin dayar, waikuma
ahakan yana ganin adalci ya yiwa wadda ta tafi gidansu, yanzu dan Allah idan
ban da rashin
tunani ai auren mace sama da daya baiyi masa anfani ba, wannan matsalar kuma
tasamo asaline adalilin rashin karatu, dan haka kifara tambayarsa idan ya ba ki irin wannan hujjar sai ki
fada masa kuskurene cikin hikima, idan bai gane ba a fada wa wadanda yake jin maganarsu, amma zancen
gaskiya wannan zalunci ne an danne miki hakkinki, a ƙa'ida idan mace ta yi tafiya
ba a rama mata kwanakin da ta yi, amma idan namiji ne ya yi tafiya yadawo to dole ne a sake sabon rabon kwana sai dai idan ya tafi da ragowar bashin
kwanan wata a kansa wannan dole sai ya rama mata
Allah ya sa mu dace.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.