Za ka iya kiran kowane layi ba tare da sun taɓa maka kuɗin cikin wayarka ba.
Jama’a barkanmu da war haka. Fatan duk kuna lafiya?
A cikin posting ɗina na yau zan kawo muku cikakken bayani a kan yadda za ka kira kowane layi ba tare da an taɓa maka kuɗin account ɗinka ba.
Abin da muke buƙata shi ne ka karanta wannan bayani daki-daki kuma dalla-dalla, sannan ka karanta wannan bayani tun daga farko har ƙarshe, domin fahimtar yadda abin yake.
Idan ka tsallake wata gaɓa ba tare da ka fahimta sosai ba, hakan na iya sakawa abin ya ƙi yiwuwa.
To da farko dai kowa ya san cewar mafi yawan wayoyin da muke yi ana cire kuɗi. To shi ne nake sanar da ku cewa ba yadda za a yi ka yi kira ba tare da an cire maka kuɗi ba.
Sai anjima.
An zo a ci banza
Banza ba ta samu ba
Sai a tashi a je gida
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.