Al'adar Wasan Tashe A Ƙasar Hausa
ABUBAKAR
S SABIU (SARKI)
07039311880
MA'ANAR TASHE
Masana da dama
sun bayyana ma'anar tashe kamar haka:
Umar M.B
(1987) Ya bayyana ma'anar tashe da cewa, "Tashe wata al'ada ce da ake yi a lokacin azumin watan Ramalana.
Da wannan ana
iya cewa tashe wani wasan kwaikwayo ne da ake yi cikin raha da annushuwa da kayatarwa a a goma farko ta cikin
watan azumin Ramalana.
ASALIN
KALMAR TASHE
kalmar 'tashe' ta samo asali ne daga kalmar 'tashi' wato mutum ya tashi domin sahur
yayin ɗaukar azumi. Wasannin tashe sun samo asali ne daga
Nalako, wanda sarki
ne yake naɗa shi a matsayin sarkin
gwagware - wadanda suka daɗe ba su yi aure ba.
Nalako yana
kewayawa ne yana wasanni don tashin gwagware daga bacci saboda ba su da matan da za su riƙa tashin su. Kuma da daddare ne Nalako yake wasa bayan
an gama sahur, daga nan ne mutane
suka fara kwaikwayonsa suna yin tashe.
Wannan Al'ada
ce bayan zuwan addini musulunci ƙasar Hausa, don haka galibi irin waƙen da ake yi ana shigar da abin da ya danganci addini, musamman kalmomi da ke
nuna Bahaushe addininsa musulunci ne.
RUKUNONIN
MASU TASHE
Akwai rukuni
na masu aiwatar da Tashe.
1-Tashen Maza
2-Tashen Mata.
1- Tashen
maza: akwai wasan yara maza na nuna jarumta misali: wasan tashen 'inda hali ya yi ba gudu ba tsoro" yara
na sanya kayayyaki na al'ada kamar
guru da laya da wuƙa da takobi na katako
suna zagaya wa cikin gari suna nishaɗantar
da magidanta.
2- Tashen
mata: akwai wasan "Mairama da Daudu inda 'yan mata sukan yi shiga ta namiji a shimfiɗa tabarwa ana rera baituka kamar
"Dauko
ruwansa ki ba shi
Dauko tuwonsa
ki ba shi
Dauko furarsa
ki ba shi
Sai kin durƙusa ki
ba shi, sai kin rausaya ki ba shi".
Wa ake yi wa tashe?
Nalako yana yi
wa sarakuna tashe
Lokacin Tashe
ana shiga gidaje ne in da yara suke shiga gida-
gida suna
aiwatar da wasanninsu na tashe. Wani lokaci ana
tashe da rana amma an fi yi bayan sallar isha'i.
Muhimmacin tashe
1- Tashe yana taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihi.
2-Tashe yana
nishaɗantar da masu
azumi.
3- Tashe yana ɗauke ko mantar da gajiyar Azumi.
Kammalawa
Tashe Al'ada
ce da take koyar da kyawawan abubuwa kala-kala. A gefe guda kuma tana nishaɗantar da al'umma da saka
mutane raha.
Yana da kyau a ƙara farfaɗo da wannan Al'ada ta tashe, duba da yadda ake nema a yi watsi da ita.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.