Ticker

Hukuncin Wanda Ya Ci Abinci Bayan Alfijir Ya Keto

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe Alfijir ya keto tun kafin na fara ci, sai dai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To Malam, mutukar ba da saninka kayi haka ba, to Azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai Azumi ya yi kokwanton hudowar Alfijir, to ya halatta a gare shi yaci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali, kamar yadda Ibnu-Abbas yake cewa: "Allah ya halatta mana cin abinci - a Ramadana - mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir", sai dai in da zai yi kokwanton faɗuwar rana to bai halatta a gare shi yaci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.

Allah ne mafi sani.

 Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments