Ticker

Wani Ruwa Yana Fitomin A Gabana Amma Kuma Ba Jini Ba Ne

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu,

tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma kuma ba jini bane. Ina ganinsa kasa kasa babu wari ko ƙarni tare dashi, ina ganinsa idan na yi Azumi ko na yi aiki sosai se marata ta yi ciwo shi ne yake fitomin. Yaya Azumi na da sallah ta take shin zan cigaba da yansu ? sannan yana fitomin wajan ƙarfe 3 na rana ne .

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, mutukar ba jini ba ne, kuma ba baki ba ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya daga cikin siffofinsa.

Allah ne mafi sani

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments