Yaya Annabi (SAW) Yake Yin Salla Da Dare A Ramadan?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Ina so a gaya min haƙiƙanin yadda Annabi yake yin sallar daren Ramadan?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Toh Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace shi Annabi (s.a.w) baya wuce Raka'a 11 a cikin Ramadan ko a wajen Ramadan. Kuma idan kakoma Rubuce Rubucenda Malamai suka yi a kan Sallar Daren Ramadan za ka samu su Magabata sunayin Tarawihi iri biyu ne.

    Na farko shi ne abunda suke kiransa Tarawihi, ita kuma yadda suke yin ta shi ne bayan anzo an yi Sallar Isha'i Angama se kowa yatafi gida aje aci Abinci aɗan huta se Asake dawowa Masallaci afara yin Sallar dare, kuma Sallah suke yi Me kyau sosai ba wai Haya Haya suke yi ba A'a sallah ce suke yi me tsawo tayadda kafin Agama Raka'a Biyu kowa ya gaji, se a ce toh atsaya aɗan huta masu Buƙatu suje suyi Buƙatunsu se adawo aƙara ɗaurawa asake yin wasu Raka'a Biyun. Toh ahaka ake yi ana hutawa har agama Raka'a 11 wannan shi ne suke kira Tarawihi, kuma ana ce masa Tarawihi ne saboda wannan Hutawarda ake yi a tsakani.

    Watarana kuma sesuce yau ba Tarawihi zamuyiba Tahajjudi zamuyi, shikuma Tahajjudi yadda yake shi ne bayan angama Sallar Isha'i se a ce kowa ya je ya kwanta ayi Bacci a huta, bayan an yi Bacci anhuta se aƙara tasowa adawo Masallaci akama Sallah ita ma haka zasuyita Raka'o'i masu kyau masu tsawo anayi ana Hutawa. Toh ita kuma suna Kiranta Tahajjudine saboda ansamu wannan Baccin kafin aka zo aka fara yin ta. Ke nan Tarawihi da Tahajjudi dukansu abu ɗaya ne kawai Bambancinsu shi ne wancan an yi bacci wannan babu bacci. Kokuma kace wannan a Farkon Dare waccan kuma Tsakiyar Dare Kuma su bawai se a Goman ƙarshe Magabata suke yin Tahajjudiba A'a koda yaushe suna iya yin ta a cikin Ramadan.

    Amma mu ayau Raunine irin namu da Kasala shi ya sa Mukeyin Tarawihi daga Alamtara kaifa zuwa Nasi shike nan angama. Kokuma wasuma sekaji kawai ana Karanta wasu gajerun ayoyi se ayi Ruku'u wannan shi ma kaga ba daidai bane son zuciyane amma dai Sallar ta yi tunda dama Asalinta ba wajibi bane, saidai in kuna so ku samu Cikakkiyar lada to sekuyi koyida irin wacce Magabata suke yi.

    Sannan kuma duk wata Sallarda wani zebaka ko wata Addu'a ya ce wai ga Addu'arda ake yi kullun a Ramadana wannan Sheɗancine da son rai kuma Bidi'ane. Annabi beyi wata Sallah ba a cikin Dararen Ramadana inbanda Tarawihi.

    Allah ya sa mu dace

    🏼Jameel Alhasan Haruna Kabo (ABU ZULAIKHA)

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Lvn6zKswf8M8cnTnYUgƘny

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.