Ticker

Abubakar Alu - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

 

Ya sanata na Ɗan Barade,

Allah ya kama ma,

Ka ji mai kujera huɗu jere,

Tun da Rabbana shi ne ya raga ma,

Ka ji mai kujera fuɗu jere,

Tun da Rabbani shi ya raga ma.

 

Na ɗai ka yi difiti gwamna,

Da kag gano kuma aikinsu,

Ka ga ba irin aiki nai ba,

Aliyu ya aje aikinsu,

Yay yi ritaya yai zaune,

A kwan a tashi na Allah na,

Allah ka taimakon dai bawa nai,

Akwan a tashi na Allah,

Aliyu kai takara kuma ka canye,

Idan ka ce ba haka nan ba,

To duk Allah ya yarda,

Allah ka zubin nan kuma daidai,

To Aliyu an koma zaɓe,

Aliyu Allah ya yarda,

To kuma ka zam gwamnanmu,

Kujera ai biyu to sosai,

To ga ka nan sarkin Yamma,

Yanzu Rabbana shi yay yarda

Ɗan Barade Alu as sanatanmu,

Ga sanata nan zauni nai,

Yarima sannu da aikinka,

Baba uban Bello Koc sadauki, sai gayya,

Baba uban Bello Koc sadauki sai gayya,

Farin watanmu baban Ɗan Ama,

Allah shi taya maka aikinka,

Allah shi taya maka aikinka.

 

To sanatanmu Alu baba,

Ɗan Barade mai komi Allah,

Abin da ni nai ma koke,

Ba ni kujera na Haji nau,

Don darajar janaral Daura,

Baban su Bello Koc nai ma koke,

Allah don darajar manzo,

Ya ƙaddara ka ji kokena,

 

Yara ku ban tambarin kiɗan Alu daidai.

 

Allah shi ka lokaci kog gobe,

Shi ɗai ka canza zamani nai,

Allah shi ka lokaci ko gobe,

Sannan shi kaɗai ka canza zamani nai,

In ya ce ka zamo sai ka zam,

Ko ba a so ana dafa ma,

In ya ce ka zamo sai ka zam,

Ko ba a so ana rakiyak ka,

A nemi shawara ta wurinka,

In ka faɗi a ce an gamsu,

Inji kalangai na Ɗan Barade masoyi.

 

Gagari gasa Ali maganin mai gasa,

Ali kai na ba su na ba,

Sannan ba irin waɗannan na ba,

Ka ji mai kujera ukku,

Ali ka yi difiti gwamna,

Sannan ga ka sarkin Yamma,

Dibi mahassadanka Aliyu,

Ali suna gina maka ramu,

Amma ɗiyansu na faɗawa,

Bar su da Allah Alu ko gobe,

Alu Ɗan Barade kak ka ji tsoro,

Ka yi lamba wan kontestin,

Aliyu ka zama gwamna,

‘Yan baƙin ciki na Aliyu,

Sun ka ce haka ba haka ne ba,

Wannan Ali an rushe shi,

Diba an yo zaɓe,

Ɗan Barade ka zan gwamna,

Ka tunda Allah ya so,

Bayan Ɗan Barade ka zan gwamna,

Yanzu ko sanata aka ce ma,

Allah Ubangiji ya yarda.

 

Haba ɗan Barade sayya garaje,

Bahagon gulbi haji Ali,

Alu wuce da mai ganganci,

Sannan ba uban da zai beli nai.

Alu wuce da mai ganganci,

Sannan ba uban da zai beli nai.

 

Kowat taɓa su runtuma tare,

Koli na baƙi garaje sarkin Yamma,

Ga koken Abu Badawa,

Farin wata uban Ɗan Ama,

Uban su Bello Koc ɗan gwamna,

Ɗan gwamna mai buki da Bature,

Ina Bello Koc masoyi,

Inji kalangai suna faɗin sai kai ya,

Alhaji Bello koc na gode,

Ɗan gwamna mai buki da Bature,

Haba ɗan sanata dokto,

Koken da niy gagara gasa,

Ka ban kujeran Hajji,

Don darajar maƙi garaje gwamna Ali,

Ba ni kujerar hajji,

Don sanata ni roƙa,

Haji Bello Koc na roƙa,

Ɗa mai kama da uban shi,

Tun da Allah shi yay yarda,

Ba yin mutum ba yin Allah na,

Dibi in tafiya ta samu,

Yi ƙoƙari ka sami masoyi,

Gama ko’ina shina rakiyak ka,

To ina mai son ka na rabo ko gobe,

Ka bar kwarabniya,

Kana ruɗa shi,

Kuma hassadaƙ ƙuje ko gobe,

Ba ta hana zuma zaƙinta,

Amma iy ya yi izgili ya taɓa ka,

Ka san ba uban da za shi raba ku,

Don Allah gagari gasa,

Ce sanata haji Ali,

Ɗan Barade kura ka zo,

Ɗan Barade kura ka zo,

Allah ka rabo ko gobe,

To ban ɗebe ɗan ba ban samu ba,

Allah Ubangiji ya yarda,

Ɗan Barade gagari gasa.

 

Ga Abubakar Badawa,

Ga Abubakar Badawa,

Wautan da nai gwamna Aliyu,

Ka ba da kujeran Hajji,

To Garba ban samu ba,

Gwamna ka yi rabon motoci,

To gwamna ban samu ba,

Ka ba da gidaje gwamna,

To gwamna ban samu ba,

To amma ban ɗebe ɗan ba ban samu ba,

Idan Allah Ubangiji ya yarda,

Dan Allah ka da nau Ɗan Ama,

Ka ban kujerar Hajji,

Don dabida ƙi garaje baba,

Ka ban kujerar Hajji,

Don gwamna ƙi saki ko gobe,

Ya ɗan Umaru baban Umar,

Babangida mi kac ce min,

Sarkin Gida mi yaf faru?

Da kai da Bello Koc Ɗan gwamna,

Wa za shi ba ni mota in hau?

Sannan a ban kujerar Hajji,

Albarkacin shi sanya garaje,

Ai mai suna Aliyu ba ya da tsoro,

Ƙinshiƙi na Sakkwato kaf ɗai,

Ba yin mutum ba yin Allah na,

Farin watanmu Alhaji Ali,

Ali hito gaban maƙiyanka,

Ko ba su so su duba daidai,

Ba yin mutum ba yin Allah ne,

Don rana in ya taho,

Ya wuce tafin hannu,

To tilas a hanƙure ko gobe,

Sanatanmu Aliyu,

Don Allah ko ni gagari gasa,

Aliyu Sarkin Yamma,

Don Allah abin Hasan da Husaini,

 

Na Barade nai ma koke,

Jirgin sama’u zai tashi,

Haba wuce da ni Hajji Ali,

Don darajar Barade Alhaji Salihu,

Duba idan za ka ban ka ba Ɗan Ama.

 

Han na tuna da Ummaru Manu,

Ubangiji yi ma kammata,

Da lafiya da manyan kuɗɗi,

To sanatanmu Alu baba,

Ɗan Barade mai komi Allah,

Abin da ni nai ma koke,

Ba ni kujerar janaral Daura,

Baban su Bello Koc nai ma koke,

Allah don darajar Manzo,

Ya ƙaddara ka ji kokena.

 

Yara ku ban tambarin kiɗan Alu daidai.

 

Allah shi ka lokaci kog gobe,

Shi ɗai ka canza zamani nai,

Allah shi ka lokaci ko gobe,

Sannan shi kaɗai ka canza zamani nai,

In ya ce ka zamo sai ka zam,

Ko ba a so ana dafa ma,

In ya ce ka zamo sai ka zam,

Ko ba a so ana rakiyak ka,

A nemi shawara ta wurinka,

In ka faɗi a ce an gamsu,

Inji kalangai na Ɗan Barade masoyi.

 

Gagari gasa Ali maganin mai gasa,

Ali kai na ba su na ba,

Sannan ba irin waɗannan na ba,

Ka ji mai kujera ukku,

Ali ka yi difiti gwamna,

Sannan ga ka sarkin Yamma,

Dibi mahassadanka Aliyu,

Ali suna gina maka ramu,

Amma ɗiyansu na faɗawa,

Bar su da Allah Alu ko gobe,

Alu Ɗan Barade kak ka ji tsoro,

Ka yi lamba wan kontestin,

Aliyu ka zama gwamna,

‘Yan baƙin ciki na Aliyu,

Sun ka ce haka ba haka ne ba,

Wannan Ali an rushe shi,

Diba an yo zaɓe,

Ɗan Barade ka zan gwamna,

Ka tunda Allah ya so,

Bayan Ɗan Barade ka zan gwamna,

Yanzu ko sanata aka ce ma,

Allah Ubangiji ya yarda.

 

Haba ɗan Barade sayya garaje,

Bahagon gulbi haji Ali,

Alu wuce da mai ganganci,

Sannan ba uban da zai beli nai.

Alu wuce da mai ganganci,

Sannan ba uban da zai beli nai.

 

Kowat taɓa su runtuma tare,

Koli na baƙi garaje sarkin Yamma,

Ga koken Abu Badawa,

Farin wata uban Ɗan Ama,

Uban su Bello Koc ɗan gwamna,

Ɗan gwamna mai buki da Bature,

Ina Bello Koc masoyi,

Inji kalangai suna faɗin sai kai ya,

Alhaji Bello koc na gode,

Ɗan gwamna mai buki da Bature,

Haba ɗan sanata dokto,

Koken da niy gagara gasa,

Ka ban kujeran Hajji,

Don darajar maƙi garaje gwamna Ali,

Ba ni kujerar hajji,

Don sanata ni roƙa,

Haji Bello Koc na roƙa,

Ɗa mai kama da uban shi,

Tun da Allah shi yay yarda,

Ba yin mutum ba yin Allah na,

Dibi in tafiya ta samu,

Yi ƙoƙari ka sami masoyi,

Gama ko’ina shina rakiyak ka,

To ina mai son ka na rabo ko gobe,

Ka bar kwarabniya,

Kana ruɗa shi,

Kuma hassadaƙ ƙuje ko gobe,

Ba ta hana zuma zaƙinta,

Amma iy ya yi izgili ya taɓa ka,

Ka san ba uban da za shi raba ku,

Don Allah gagari gasa,

Ce sanata haji Ali,

Ɗan Barade kura ka zo,

Ɗan Barade kura ka zo,

Allah ka rabo ko gobe,

To ban ɗebe ɗan ba ban samu ba,

Allah Ubangiji ya yarda,

Ɗan Barade gagari gasa.

 

Ga Abubakar Badawa,

Ga Abubakar Badawa,

Wautan da nai gwamna Aliyu,

Ka ba da kujeran Hajji,

To Garba ban samu ba,

Gwamna ka yi rabon motoci,

To gwamna ban samu ba,

Ka ba da gidaje gwamna,

To gwamna ban samu ba,

To amma ban ɗebe ɗan ba ban samu ba,

Idan Allah Ubangiji ya yarda,

Dan Allah ka da nau Ɗan Ama,

Ka ban kujerar Hajji,

Don dabida ƙi garaje baba,

Ka ban kujerar Hajji,

Don gwamna ƙi saki ko gobe,

Ya ɗan Umaru baban Umar,

Babangida mi kac ce min,

Sarkin Gida mi yaf faru?

Da kai da Bello Koc Ɗan gwamna,

Wa za shi ba ni mota in hau?

Sannan a ban kujerar Hajji,

Albarkacin shi sanya garaje,

Ai mai suna Aliyu ba ya da tsoro,

Ƙinshiƙi na Sakkwato kaf ɗai,

Ba yin mutum ba yin Allah na,

Farin watanmu Alhaji Ali,

Ali hito gaban maƙiyanka,

Ko ba su so su duba daidai,

Ba yin mutum ba yin Allah ne,

Don rana in ya taho,

Ya wuce tafin hannu,

To tilas a hanƙure ko gobe,

Sanatanmu Aliyu,

Don Allah ko ni gagari gasa,

Aliyu Sarkin Yamma,

Don Allah abin Hasan da Husaini,

 

Na Barade nai ma koke,

Jirgin sama’u zai tashi,

Haba wuce da ni Hajji Ali,

Don darajar Barade Alhaji Salihu,

Duba idan za ka ban ka ba Ɗan Ama.

 

Han na tuna da Ummaru Manu,

Ubangiji yi ma kammata,

Da lafiya da manyan kuɗɗi,

To sanatanmu Alu baba,

Ɗan Barade mai komi Allah,

Abin da ni nai ma koke,

Ba ni kujerar janaral Daura,

Baban su Bello Koc nai ma koke,

Allah don darajar Manzo,

Ya ƙaddara ka ji kokena.

Post a Comment

0 Comments