Addu'ar Ruku'u, Sujjada Da Tahiya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Dan Allah mln sonake ababbancemin addu ar dagowa da ruku u da sujaddah da zaman tayhiya ngd

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    ADDU'AR RUKU'U.👇🏻

     سُبْـحانَ رَبِّـيَ الْعَظـيم . (ثلاثَ مَرَّاتٍ)

    (Tsarki ya tabbata ga Ubangijin mai girma (Sau uku).

     سُبْحانَكَ اللّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِك، َاللَّّهُمَّ اغْفِرْ لِي.

    (Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu, tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.)

     سُبُّوحٌ قُـدُّوسٌ، رَبُّ الْمَلاَئِكَةِ وَالرُّوحُ .

    (Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala'iku da Jibrilu.

     اَللَّهُمَّ لَكَ رَكَعْتُ وَبِكَ آمَنْتُ، ولَكَ أَسْلَـمْتُ، خَشَعَ لَكَ سَمْعِي، وَبَصَرِي، وَمُخِّي، وَعَظْمِي، وَعَصَبِي، وَمَا اسْتَقَـلَّ بِهِ قَدَمِي.

    Ya Allah! Gare ka na yi ruku'u, kuma da Kai na yi imani, kuma gare ka na mika wuya. Jina ya yi kaskanci gare Ka, haka ma ganina da bargona, da kashina, da jijiyata, da kuma abin da kafata ke dauke da shi.

     سُبْـحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، والمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءُ، وَالْعَظَـمَة.

    Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka, da girma.

    ADDU'AR DAGOWA DAGA RUKU'U👇🏻

     سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ.

    Allah Ya ji wanda ya gode masa.

     رَبَّنـا وَلَكَ الحَمْـدُ حَمْداً كَثِيراً طَيِّـباً مُـبَارَكاً فِيهِ

    Ya Ubangijinmu! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sawa albarka a cikinsa.

     مِلْءَ السَّمَوَاتِ وَمِلْءَ الأَرْضِ، وَمَا بَيْنَهُمَا، وَمِلْءَ مَا شِئْتَ مِنْ شَيءٍ بَعْدُ. أَهْلَ الثَّنَاءِ وَالْمَجْدِ، أََحَقُّ مَا قَالَ العَبْدُ، وَكُلُّنَا لَكَ عَبْدُ. اَللَّهُمَّ لاَ مَانِعَ لِمَا أَعْطَـيْتُ، وَلاَ مُعْطِيَ لِمَا مَنَعْتَ، وَلاَ يَنْفَعُ ذَا الْجَدِّ مِنْكَ الْجَدُّ.

    Ya Ubangiji! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, (yabo) mai Cika sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu, mai cika duk wani abu da Ka so bayan haka. Ya wanda ya cancanci yabo da daukaka. (wannan yabo) shi ne mafi cancantar abin da bawa ya fada, kuma dukkanninmu bayi ne gare Ka. Ya Allah! Babu mai hana abin da Ka bayar, kuma babu mai bayar da abin da Ka hana, kuma wadata ba ta tsirar da mai wadata daga gare Ka.

    ADDU'AR SUJJADA 👇🏻

    سُبْحَانَ رَبِّيَ الأَعْلَى . (ثلاثَ مَرَّاتٍ)

    Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mafi daukaka. (Sau uku)

    سُبْحَانَكَ اَللَّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِكَ، اَللَّهُمَّ اغْفِرْلِي.

    Tsarki ya tabbata gare Ka, Ya Allah! Ya Ubangijinmu! Tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.

    سُبُّوحٌ قُدُّوس، رَبُّ الملائِكَةِ وَالرُّوحُ

    (Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala'iku da Jibrilu.

    اَللَّهُمَّ لَكَ سَجَدْتُ وَبِكَ آمَنْتُ، وَلَكَ أَسْلَمْتُ، سَجَدَ وَجْهِي ِللَّذِي خَلَقَـهُ وَصَوَّرَهُ وَشَقَّ سَمْعَهُ وَبَصَرَهُ، تَبَارَكَ اللهُ أَحْسَـنُ الْخَالِقِين.

    Ya Allah! Gare ka na yi sujada, kuma da Kai na yi imani, kuma gare Ka na mika wuya. Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya yi mata surarta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta. Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita.

    سُبْحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، وَالْمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءُ، وَالْعَظَمَة.

    Tsarki ya tabbata ga (Allah) mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka da girma.

    اَللّهُمَّ اغْفِرْلِي ذَنْبِي كُلَّهُ، دِقَّهُ وَجِلَّهُ، وَأَوَّلَـهُ وَآخِـرَهُ وَعَلانِيَّتَهُ وَسِرَّه.

    Ya Allah! Ka gafarta mini zunubaina dukkaninsu, kananansu da manyansu, na farkonsu da na karshensu, bayyanannunsu da boyayyunsu.

     اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِرِضَاكَ مِنْ سَخَطِكَ، وَبِمَعَافَاتِكَ مِنْ عُقُوبَتِكَ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْكَ، لاَ أُحْصِي ثَنَاءً عَلَيْكَ، أَنْتَ كَمَا أَثْنَيْتَ عَلَى نَفْسِكَ.

    Ya Allah ina neman tsari da yardarka daga fushinka, da kuma rangwamanka daga ukubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare Ka. Ban isa na tuke ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda Ka yabi kanKa ne.

    ADDU'AR ZAMA TSAKANIN SUJADAR FARKO DA TA BIYU.👇🏻

    رَبِّ اغْفِـرْ لِي ، رَبِّ اغْفِـرْ لِي .

    Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ya Ubangijina! Ka gafarta mini.

     اللّهُـمَّ اغْفِـرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَاجْبُرْنِي، وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي وَارْفَعْنِي .

    Ya Allah! Ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shirye ni, ka wadata ni, ka ba ni lafiya da tsira daga musifu, ka azurta ni, ka daukaka ni.

    ADDU'AR TAHIYA👇🏻

    اَلتَّحِيَّاتُ ِللهِ وَالصَّلَوَاتُ والطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُه .

    Dukkan nau'in ban girma ya tabbata ga Allah, da kuma salloli da kyawawan kalmomi. Aminci ya tabbata gare ka ya Annabi, da rahamar Allah da albarkatunsa. Aminci ya tabbata gare mu, da kuma ga bayin Allah salihai ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.

    SALATI GA MANZON ALLAH ﷺ BAYAN TAHIYA👇🏻

    اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْوَاجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ. وَبَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى أَزْواجِهِ وَذُرِّيَّتِهِ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ. إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

    Allah kayi Salati ga Annabi Muhammad da Alayansa kamar yadda kayi Salati da Annabi Ibrahim da Alayansa, lallai kai abin godewa ne mai girma, kuma kayi Albarka ga Annabi Muhammad da Alayansa kamar yadda kayi Albarka ga Annabi Ibrahim Lallai kai cewa Abin godewa ne kuma mai girma

    ADDU’A BAYAN TAHIYAR KARSHE👇🏻

    اللَّهُــمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ شَرِّ فِتْنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ

    Ya Ubangiji ina neman tsari daga Azabar Kabari, da kuma Azabar Wutar Jahannama, da kuma fitinar Rayuwa da kuma ta Mutuwa, da kuma Sharrin Fitinar Dujal mai shafafen Ido

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَعوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَأَعوذُ بِكَ مِنْ فِتْنَةِ الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ، وَأَعوذُ بِكَ مِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ. اللَّهُمَّ إِنِّي أَعوذُ بِكَ مِنَ الْمَأْثَمِ وَالْمَغْرَمِ

    Ya Ubangiji ina neman tsari daga Azabar Kabari, da kuma fitinar Rayuwa da kuma ta Mutuwa, da kuma Sharrin Fitinar Dujal mai shafafen Ido kuma ina neman tsarinka daga saɓo da kuma bashi

    اللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْماً كَثِيراً، وَلاَ يَغْفِرُ الذُّنوبَ إِلاَّ أَنْتَ، فَاغْفِرْ لِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ وَارْحَمْنِي، إِنَّكَ أَنْتَ الغَفورُ الرَّحيمُ

    Ya Ubangiji ni lallai na zalunci kaina zalunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai kai kadai, kayi mun gafara gafara daga gareka kuma kaji kaina, domin kaine mai gafara mai jin kai.

    اللَّهُمَّ اغْفِرْ لِي مَا قَدَّمْتُ، وَمَا أَخَّرْتُ، وَمَا أَسْرَرْتُ، وَمَا أَعْلَنْتُ، وَمَا أَسْرَفْتُ، وَمَا أَنْتَ أَعْلَمُ بِهِ مِنِّي. أَنْتَ الْمُقَدِّمُ، وَأَنْتَ الْمُؤَخِّرُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ

    Ya Ubangiji kayi mun gafara ga abin da na aikata, da wanda ban aikata ba da wanda na bayyyana da wanda ban bayyana ba, kuma kaine mafi sani da ni kuma kaine mai gabatarwa, kuma kaine mai jinkirtawa babu wani ubangiji sai kai.

    اللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ، وَشُكْرِكَ، وَحُسْنِ عِبادَتِكَ

    Ya Ubangiji ka taimakeni a kan ambatonka da gode maka, da kuma kyautatawa a Ibadarka

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْبُخْلِ، وَأَعوذُ بِكَ مِنَ الْجُبْنِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ أَنْ أُرَدَّ إِلَى أَرْذَلِ الْعُمُرِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ فِتْنَةِ الدُّنْيَا وَعَذَابِ الْقَبْرِ

    Ya Ubangiji lallai ni ina neman tsarinka daga yinwa, kuma ina neman tsarinka daga tsoro kuma ina neman tsarinka kada na koma kaskantacciyar rayuwa, kuma ina neman tsarinka, daga fitinar duniya da kuma Azabar Kabari

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ

    Ya Ubangiji ina rokonka Aljanna kuma ina neman tsarinka daga Wuta

    اللَّهُمَّ بِعِلْمِكَ الغَيْبَ وَقُدْرَتِكَ عَلَى الْخَلقِ أَحْيِنِي مَا عَلِمْتَ الْحَيَاةَ خَيْراً لِي، وَتَوَفَّنِي إِذَا عَلِمْتَ الْوَفَاةَ خَيْراً لِي، اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَشْيَتَكَ فِي الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ، وَأَسْأَلُكَ كَلِمَةَ الْحَقِّ فِي الرِّضَا وَالْغَضَبِ، وَأَسْأَلُكَ الْقَصْدَ فِي الْغِنَى وَالْفَقْرِ، وَأَسْأَلُكَ نَعِيماً لاَ يَنْفَدُ، وَأَسْأَلُكَ قُرَّةَ عَيْنٍ لاَ تَنْقَطِعُ، وَأَسْأَلُكَ الرِّضَا بَعْدَ الْقَضَاءِ، وَأَسْــــأَلُكَ بَرْدَ الْعَيْشِ بَعْدَ الْمَوْتِ، وَأَسْأَلُكَ لَذَّةَ النَّظَرِ إِلَى وَجْهِكَ، وَالشَّوْقَ إِلَى لِقائِكَ فِي غَيرِ ضَرَّاءَ مُضِرَّةٍ، وَلاَ فِتْنَةٍ مُضِلَّةٍ، اللَّهُمَّ زَيِّنَا بِزِينَةِ الإِيمَانِ، وَاجْعَلْنَا هُدَاةً مُهْتَدِينَ

    Ya Ubangiji da iliminka na fake da kuma kudurarka ka raya ni matukar rayuwar ita tafi alkairi a gareni kuma ka karbi raina matukar Mutuwa ita ta fi Alkairi a gare ni, ya ubangiji ni ina rokonka kalmar gaskiya a cikin farin ciki da fushi, kuma ina rokonka Manufa cikin wadata da talauci kuma ina rokonka ni'amar da ba ta karewa, kuma ina rokonka farar idaniyar da ba ta yankewa, kuma ina rokonka yarda bayan kayi hukunci, kuma ina ronka sassanyar rayuwa bayan mutuwa, kuma ina rokonka, jin dadin ganin fuskarka da kuma shauki zuwa ga haduwa da kai ba tare da wata cuta ba ko cutarwa, ko kuma wata fitina mai batarwa, Ya Ubangiji ka kawatani da adon Imani kuma ka sanyani shiryayye mai shiryarwa

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ يَا أَللَّهُ بِأَنَّكَ الْوَاحِدُ الْأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يولَدْ، وَلَمْ يَكنْ لَهُ كُفُواً أَحَدٌ، أَنْ تَغْفِرَ لِي ذُنُوبِي إِنَّكَ أَنْتَ الْغَفُورُ الرَّحِّيمُ

    Ya Ubangiji ina rokonka Ya Allah cewa kai kadai kake wanda ake nufa da bukata wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da kini mai tashin hanci, kayi mun gafara ga zunubai na lallai kai mai gafara kuma mai jin kai

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ لَكَ الْحَمْدَ لَا إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ وَحْدَكَ لاَ شَرِيكَ لَكَ، الْمَنَّانُ، يَا بَدِيعَ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ يَا ذَا الْجَلاَلِ وَالْإِكْرَامِ، يَا حَيُّ يَا قَيُّومُ إِنِّي أَسْأَلُكَ الْجَنَّةَ وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ النَّارِ

    Ya Ubangiji ina Rokonka cewa kai ne godita tabbata a gareka kai kadai babu wani Ubangiji sai kai, mai yawan baiwa, wanda ya kawata sama da kasa kuma ma'abocin girma da daukaka, ya wanda yake rayayye kuma tsayayye da kansa ina rokonka Aljanna, kuma ina neman tsarinka daga wuta.

    اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّي أَشْهَدُ أَنَّكَ أَنْتَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ الْأَحَدُ الصَّمَدُ الَّذِي لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُواً أَحَدٌ

    Ya Ubangiji ina Rokonka cewa lallai na shaida babu wani Ubangiji sai kai makadaici abun nufi da bukata wanda bai haifa kuma ba a haife shi ba kuma bashi da kini mai tashin hanci a gare shi.

    WALLAHU A'ALAM

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.