𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam barka da safiya ya aiki? Allah ya biya. Tambaya: Malam mijina ne yana so na ina son shi kuma yana kyautata min ni ma ina yi mar biyayya, amma wasu lokutan sai ya dinga wula kanta ni kamar ba matarsa ba, malam ni kuma abin yana kona min rai, sai na dinga ramawa, dan Allah malam ina da laifi a wurin Allah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa a gaskiya
yin hakan kuskure ne babba, duk wanda ya munana maka an ce ne kai kuma ka
kyautata masa, kyautatawar mutum ga wanda ya munana masa yakan iya sa mai munana
maka ya zama masoyinka.
A matsayin wannan miji da ke kanki
kin faɗa yana son ki, kuma yana kyautata maki, to duk lokacin da kika ga canji
daga gare shi ya kamata ki yi masa uzuri, saboda wata ƙil ya shiga wani yana yi
ne da ba ya buƙatar yawan damunsa da kusantarsa, domin akwai irin waɗannan
mutanen, da idan suka shiga wani halin ba su cika son a dame su da magana ba,
ko a cika yawan kusantarsu ba.
Saboda haka ki daina rama mummuna
da mummuna, ki kyautata ma wanda ya munana maki gwargwadon hali kowane ne,
kamar yadda hadisai da ayoyi suka koyar. Kuma wannan yana daga cikin babban
kuskuren da mafi yawa daga cikin mata suke tafkawa idan mazajensu suka saɓa
masu, su a ganinsu wai hakan ne zai samar masu da ‘yanci, alhali kuma ba haka
ba ne, duk abin da haƙuri bai ba da shi ba, to tashin hankali ba zai ba da shi
ba, wanda aka ce shugabanki ne, to ya kamata ki riƙa haƙuri da shi musamman ma
wanda aka tabbatar yana kyautatawa daidai gwargwado.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.