𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Da fatan ka tashi lafiya, tambayata ita ce dan Allah a yi min bayani, wata yarinya ce mijinta yana aikin kwana sai ya kawo dan haya gidan, amma kofar kowa daban take, to malam ya nuna kanshi shi kamar yana da kirki suna gaisawa har yake ba wa yaranta kyauta, ya kan siyo musu kyaututtuka tin suna kin karɓa har aka bar su suna karɓa, malam sai ya ce ba komai shi dan Allah yake ba su, to har ya zamana suna gaisawa da matar har suna hira, shi ne har ya fara mata wasan banza, shi ne sai ta daina kula shi, sai ya ba ta hakuri, to malam a takaice dai wataran yana rungumarta har ya kawo maniyyi a jikinta ko a cinyarta, to malam ita ma har ya fara kawo mata sha'awa idan ya danne ta da kayanta yana nishi ita ma takan ji daɗi, amma ba su taɓa haɗa gabansu ba wajen aikata zina, amma yanzu tana ta kuka tana neman gafarar Allah ya tsare ta daga sharrinshi, da na mijinta, saboda shi ma yana ɗaukar hakkinta, ta yi ta yi ya komar da ita gun aikinshi ya ki, to dan Allah mlm shi ne nake neman fatawa ya matsayin abin yake? Shin ya zama zina ko sai an samu saduwa ne tsakanin mace da na miji shi ne zina? a taimaka mana malam, na gode Allah ya saka ma da alkairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, Inna lillahi wa innah Ilaihi Raji'un! Wannan mummunan aiki ne, kuma cin
amana ce, yaya za ta ji idan ta sami labarin cewa mijinta yana neman matan
banza a waje? Wannan aiki ne haramtacce abin ƙyama a addinin musulunci, har ma a
al'adar rayuwa. Duk da cewa kai tsaye ba za a kira wannan aikin da zina ba, to
amma kuma muninsa ya kai na zina, saboda zina kala-kala ne, akwai zina da
idanuwa, akwai zina da kunnuwa, akwai zina da harshe, akwai zina da hannuwa,
akwai zina da ƙafafuwa kamar yadda Annabi ﷺ
ya bayyana a hadisi.
Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ka ga
idanuwa, zinarsu ita ce kallo, zinar kunnuwa kuma ita ce saurare, zinar harshe
kuma ita ce magana, zinar hannu kuma ita ce shafa, su kuma ƙafafuwa
zinarsu ita ce tafiya (zuwa ga zina), ita kuma zuciya sai ta yi ta buri da
sha'awa, abin da ke gaskata waɗannan
abubuwa, ko ya ƙarya ta su shi ne farji (azzakari).
Bukhariy 6612,
Muslim 2657.
Wannan dalili
ne da ke nuna wannan aiki da wannan mata ta yi da wancan bawan Allah, ba za a
kira shi da zina na asali ba, saboda bai sadu da ita kaciya da kaciya ba, inda
za a iya kiran zina yaya da ƙaninsa, da sai a kira wannan baƙin
aiki da suka yi ƙanin zina, Allah ya kare mu.
Abin da za ta
yi shi ne, ta yi cikakkiyar nadama, ta tuba zuwa ga Allah, irin tubar da babu
tunanin komawa ga wannan saɓon
Allah ɗin har abada,
ta yi ta yawaita istigfari. In Allah ya so muna fatan Allah ya karɓi tubanta, Allah ya shiryar
da mu, ya kare mu da mugun ji da mugun gani, amin.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.