Ticker

Hukumcin Azumi Ranar Asabar

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu Alaikum malam Ance ba a Azumi Ranar Asabar, Shin Idan Azumin Nafila ya yi Dai-dai Da Asabar Din Fa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba'aso mutum ya azumci ranar asabar ita kaɗai, saboda Abun da turmuzi ya ruwaito (744) da Abu dauda (1726) daka Abdullahi bin yusur daka 'yar'uwarsa Manzan Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce: kada dayanku ya azumci ranar asabar, saifa azumin da Allah ya wajabtawa bayin sa, ko da mutum bai samu Abun da zaici ba, sai rigar dabino (Abun da ke lullube kwallon dabino), ko ita cen bishiya to yaci ko ya Taunashi)

Albani ya Ingantashi a cikin Irwa'u (960).

Haramcin yana nufin mutum ya keɓance ranar asabar kaɗai da Azumi.

Ibnu ƙudama ya ce: Haramunne azumtar ranar asabar ita kaɗai tilo, amma da mutum zai azumci juma'a ya haɗa da asabar, Babu haramci anan. Saboda hadisin Abu huraira da Juwairiyyah .

Al-mugni (3/52).

Abun da yake nufi da hadisin Abu huraira shi ne wanda bukhari (1985) ya ruwaito daka Abu huraira Allah yaƙara masa yarda ya ce: na ji manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Kada dayanku ya azumci ranar juma'a, sai idan ya azumci ranar da take kafinta ko wacce take bayanta).

Hadisin juwairiyya shi ne wanda bukhari ya ruwaito (1986) daka juwairiyyah bintu haris Allah yaƙara yarda dasu Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya shiga wajanta ranar juma'a tana azumi sai ya ce: (Kin yi azumi jiya? sai ta ce: A'a, sai ya ce: Kina so kiyi azumi gobe? sai ta ce: A'a, Sai ya ce: to Ki karya azumin.).

Wannan hadisin da Hadisin Abu huraira suna nuni ƙarara da halaccin azumtar ranar asabar ko da ba a cikin Ramaḍān ba, idan mutum ya azumci juma'a.

Ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Mafi soyuwar Azumi awajan Allah shi ne irin azumin Annabi Dauda, kayi Azumi yau gobe ka sha ruwa).

Wannan babu makawa watarana sai ya dace da ranar asabar ita kaɗai, awani azumin nasa, sai afahimci idan azumin ya yi dai-dai da ranar asabar a al'adar azuminsa, kamar Ashura ko arfa ko shittu shawwal, to babu laifi mutum ya yi azumin sa ranar Asabar. ko da shi kaɗai ne.

Ibnu hajar ya ce: Hani ya yi togaciya ga wanda Yasaba azumi da wanda haka kawai yakebe asabar ya azumta.

Idan ka fara azumin sittu shawwal sai ya dace da ranar asabar babu wannan haramci akanka.

WALLAHU A'ALAM

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments