Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Dakatar Da Haihuwa Saboda Yawan 'Ya'ya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, barka da wannan lokaci shin ya halatta matar da ta haifi yara guda tara ta tsaida haihuwu saboda halin yau da gobe?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, malamai sun bayyana halascin dakatar da haihuwa zuwa wani lokaci saboda wata buƙata ko lallura, kuma ya halasta a dakatar da haihuwar ta din-din-din idan masana kiwon lafiya suka tabbatar da cewa cigaba da haihuwa ga mace zai haifar da rasa ranta ko wata matsala makamanciyar haka, amma in ba haka ba, to bai halasta a dakatar da haihuwa ta din-din-din ba tare da wata matsala ba, kamar yadda aka bayyana a Amsoshin Tambayoyinku na 032.

Malamai suna kafa hujjar dakatar da haihuwa saboda wata buƙata da hadisin da Sahabin Manzon Allah ﷺ Jabir ɗan Abdullahi ya ruwaito cewa: "Mun kasance muna yin azalu, Alƙur'ani yana sauka".

Albukhariy 5208, Muslim 1440.

Azalu shi ne zubar da maniyyi don hana shi shiga cikin mahaifar mace a lokacin saduwa. Abin da yake nufi da suna yin azalu alhali Alƙur'ani yana sauka shi ne: A lokacin Alƙur'ani na sauka amma ba a hana su ba, in da haramun ne da za a saukar da aya a hana su, tun da alokacin ba a gama saukar da Alƙur'ani ba.

Game da matar da ta haifi ‘ya’ya da yawa, sai take ganin idan ta ci gaba da haihuwa tarbiyyar ‘ya’yan zai gagare ta saboda yawansu, to ita ma malamai sun bayyana cewa ya halasta ta dakatar da haihuwa saboda ta iya samar wa da ‘ya’yanta ingantacciyar tarbiyya kamar yadda waɗannan malaman suka tabbatar:

Asshaikh Abdul'aziz bn Baaz ya ce: "idan ya kasance mace tana da ‘ya’ya da yawa a gabanta, kuma yana ba ta wahala wurin yi masu tarbiyya ta Musulunci saboda yawansu, to ba abin da ke hana yin abin da ke tsara ɗaukar ciki saboda wannan babbar maslaha ɗin, har zuwa lokacin da ɗaukar cikin zai zama a yana yin da ba zai cutar da ita ba, ba kuma zai cutar da ‘ya’yanta ba, kamar yadda Allah ya halasta azalu da abin da ya yi kama da shi".

Fataawá Nurun Alad Darb na Ibn Baaz (21/394), kulawar Asshuwai'ir.

Asshaikh Ibn Uthaimeen ya ce: "Asalin hana ɗaukar ciki halas ne; Saboda Sahabbai Allah ya ƙara masu yarda sun kasance suna yin azalu a zamanin Manzon Allah ﷺ ba a hana su hakan ba, sai dai hakan saɓanin abin da ya fi ne; Saboda yawaita ‘ya’yaye al'amari ne Shar'antacce abin nema".

Fataawá Nurun Alad Darb na Ibn Uthaimeen (22/2).

Saboda haka ya halasta ga macen da ‘ya’ya suka yi mata yawa, kuma ta ga lallai yawansu ba zai bar ta ta samu damar ba su ingantacciyar tarbiyar da Musulunci ya wajabta a kanta ta ba su ba ta yi tsarin iyali saboda wannan maslahar, kamar yadda malaman nan suka faɗi.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments