Hukuncin Fara Azumin Sitta Shawwal Bayan Sallah Da Kwana Ɗaya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Don Allah ina da tambaya. ko mutun zai iya fara azumin sitta shauwal kwana ɗaya bayan sallah?

    Nagode Allah ya saka da Alkhairi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaykumussalam. Jamhurun malamai daga mazhabobi uku wato Hanafiyya, Shafi'iyya da Hanabala duk sun ce anso mutun ya gaggauta yin sitta Shawwal, domin hadisin da manzon Allah yce: Duk wanda ya azumci ramadan sannan yabi bayan sa da azumi shida daga (watan) shawwal...

    Sai suka ce anan an kwadaitar da abi bayan ramadan da yin azumin shawwal wato alal akalli a samu kwana ɗaya ko biyu tsakani...

    Amma mazhab na Malikiyya sun ce makaruhi ne azumtar sitta shawwal 'mubasharatan' wato kai tsaye bayan ramadan don gudun kada a kirga waɗannan kwanakin a matsayin ramadan....

    Babu laifi dai idan an samu kwana ɗaya a tsakani, amma inso samu ne a samu tazara sama da kwana ɗaya.

    WALLAHU A'ALAM.

    Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.