𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam Khamis da
fatan ka wuni lafiya. Allah ya saka da alkhairi. Tambaya ta ana shi ne na
kasance ina yin zina da dabbobi saboda tsananin sha'awa. mene ne Hukuncin Wanda
ya yi zina da dabba a musulunci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi
Wabarkatuh
Allah Ya Tsinewa Wanda duk Ya Sadu
da Babba. Dabban nan Safiya Ce Ko Tinkiya Ko Akuya Ko Agwagwa Ko Kaza; da
Makamantansu. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:
عن إبن عباس رضي الله عنه قال: أن رسول
الله صلى الله عليه وسلم قال: ”ملعون من وقع على بهيمة“.
{رواه أحمد}
An Kar6o Daga Ibn Abbas (ra) Ya ce:
Manzon Allah (ﷺ) Ya ce: “Tsinanne Ne Duk Wanda Ya Aukawa Dabba;”.
{Ahmad Ya Ruwaitoshi}
Saboda Munin Wannan Aiki Ne
Ubangiji ya yi Umurni da Kashe Duk Wanda Aka Kama Yana Saduwa da Dabba, Kai Har
Ita Dabbar ba ta tsira ba Domin Itama Kashe ta Za'ayi. Wannan Ke Nuna Munin
Zakkewa Dabba Yafi Munin Zina. Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:
عَنْ عِكْرِمَةَ عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ
رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
”مَنْ وَجَدْتُمُوهُ وَقَعَ عَلَى بَهِيمَةٍ فَاقْتُلُوهُ وَاقْتُلُوا الْبَهِيمَةَ“
{الترمذي: ١٤٥٥}
An Kar6o Daga Ikramah, Daga Ibn
Abbas (ra) Ya ce: Manzon Allah (ﷺ) Ya ce: “Duk Wanda Kuka Sameshi Yana Saduwa
da Dabba, To Ku Kashe Shi Kuma ku Kashe Dabbar”.
{Tirmizi: 1400}
Amma sai malamai sukayi bayani cewa
hadisin akwai kokonto A ingancisa dan haka sukace ba za a akashe shiba saide
ayi masa bulala kuma akaishi kurkuku wasu malamai kuma su kace yanada hukuncin
mazinaci idan ya yi aure a jefeshi har ya mutu. Idan baiyi aure ba ayimasa
bulala.
ALLAH shi ne mafi sani
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.