Hukuncin Wasa Da Azzakari Ko Farji (Istimná'i)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne Hukuncin Istimna'i (Wasa Da Azzakari Ko Farji Da Hannu Ko Wani Abu, Dan Biyawa Kai Bukatar Sha'awa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Istimna'i (Wasa da azzakari ko farji da hannu ko wani abu don biyawa kai bukatar sha'awa) haramunne saboda dalilai daka Alƙur'ani da Sunnah.

    Ibnu kaseer rahimahulla ya ce: Imamu shafi'i da waɗanda suka dace da shi sun kafa hujjah a kan haramcin istimana'i da hannu dafadin Allah madaukakin Sarki:

    وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ.

    إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ. فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ.

    فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ.

    MA'ANA:

    Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi, sai a kan matayensu ko kuyanginsu anan su ba ababen zargi ba ne, Duk wanda yanemi wata hanya ta biyan bukatar sha'awarsa saɓanin matarsa ko baiwarsa Toshi yana cikin masu ketare iyakokin Ubangiji.

    Imamu shafi'i a cikin kitabul nikah, yana bayyana ambaton kiyaye farjinsu sai a kan matayensu ko kuyanginsu, haramcin abun da ba matarka bace ko baiwa ba, sannan yakarfafa maganarsa da:

    فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ.

    Bai halatta amfani da azzakari ba sai a kan matarka, ko abun da damar mutum ta mallaka, Bai halatta yin Istimna'i ba, Kitabul Ummu Na shafi'i .

    Wasu malamai sunkafa hujja a kan haramcin amfani dawata hanya tabiyawa kai bukata saɓanin mace ko baiwa, da faɗin Allah madaukakin Sarki:

    وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ.

     النور /٣٣

    MA'ANA:

    Waɗanda ba su Samu damar Aure ba su kame harsai Allah ya wadatasu daka falalarsa.

    Umarni da kamewa Ya zartar da Hakuri a kan Abun da ba auren ba ne.

    Dalili daka Sunnah Waɗanda suke nuna haramcin Amfani da hannu ko wani abu wajan biyawa kai bukata.

    Hadisin Abdullahi dan Mas'ud Allah yakara yarda da shi Ya ce: (Mun kasance tareda Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna matasa bamu samu komai dazamuyi aure ba, Sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce damu, yaku taran matasa duk wanda yasamu Abun da zai iya rike iyali da iko ya yi Aure, domin Aure yana kange gani, yana kiyaye farji, Wanda bai samu dama ba na horeshi dayin Azumi domin Azumi kariyane daka fadawa haram) Bukhari (5066).

    Shari'a saita shiryar da wanda bashi da ikon yin aure ya yi azumi tareda wahalarsa, Amma ba ta shiryar zuwa wasa da azzakari ko farji da hannu ko da wani abu ba, duk da saukinsa da kuma ƙarfi da mutum yake da shi na aikata shi, amma duk dahaka shari'a ba ta yarda ba.

    A cikin mas'alar akwai wasu dalilan da suke nuna haramcin istimna'in amma zamu wadatu da wadannan kawai.

    MENE NE MAGANI GA WANDA YA FADA CIKIN WANNAN AL'ADA?

    Magani ga wanda ya fada cikin wannan aiki shi ne wasu nasihohi da matakai dazaibi danya kubuta daka gareshi.

    👉 Wajibine gawanda ya fada cikin wannan aikin ya dunga kwatanta Umarnin Allah da nisantar Abun da ya hana.

    👉 Kare lafiyar jiki tahanyar yin Aure, dan aiki da wasiyyar Annabi sallallahu Alaihi wasallam ga matasa.

    👉 Tunkude hadarin was-wasi dashagaltar dakai datunani zuwa abun da yake zai amfani mutum duniya da lahira, domin biyewa was-wasi da tunani yana kai mutum aikata abun da aka haramta masa.

    👉 Runtse gani daka mutane masu bayyana tsiraici ko hotuna na fitina, Na matattune ko rayayyu, da kin sakin gani, domin sakin gani yana kai mutum zuwa haramun saboda haka ne ma Allah ya Umarci muminai sukame ganinsu, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (kada kabi kallo da kallo) Turmuzi (2777) Albani ya ingantashi a cikin sahihul jami'i

    Saboda kallon farko na ba za ta dazakayi babu zunubi a kansa, kada ka sake na biyu, sannan yakamata mutun ya nisantar da kansa daka guraren da suke zasu tayar masa da sha'awa.

    👉 Shagaltuwa da ibadoji maban-banta da rashin barin wani Space na lokaci ba ka komai a cikinsa.

    👉 Riko da maganin Annabta wato Azumi domin kariyane daka aukawa cikin aikin saɓo,

    👉 Riko da ladubban shari'a wajan kwanciya bacci da farkawa daka bacci.

    👉 Rashin zama adaki kai kaɗai, ko kwana a cikinsa.

    👉 Lura dayanda wannan abun yake sabbabba cututtuka waɗanda barazana ne ga lafiyar jiki, kamar saurin mantuwa, ciwan baya, rashin karfin gabobi, rashin gani sosai raunin gani.

    👉 Duk wanda ya faɗa cikin wannan saɓo wajibne a kansa ya gaggauta tuba, da istigfari da aikata ayyukan ɗa'a tareda rashin debe tsammanin rahma awajan Allah, domin yana cikin manyan laifuka.

    👉 Abu na karshe wanda babu kokwanto a kansa shi ne komawa zuwaga Allah da kan-kan dakai da addu'a da neman taimako daka Allah dan kubuta daka wannan Al'ada wannan shi ne mafi girman magani, domin Allah maɗaukakin sarki yana Amsa addu'ar mai roko idan ya rokeshi.

    WALLAHU A'ALAM .

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.