Hukuncin Zubar Da Ciki!

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Allah ya kara wa malam lafiya. Dan Allah malam na yi sati 7 ban ga al'ada ta ba, sai na je assibiti yau aka tabbatar min ina da ciki, to ina da yaro dan wata 13 ban dade da haihuwa ba, kuma na yi ta fama da matsalar rashin jini kafin in haihu, to yanzu ina jin tsoran barin cikin nan in gamu da wata matsalar wurin haihuwa, kuma mijinaba ya iya ciyar da mu, sai aka ce in ina so za a ba ni magani da zan rabu da shi, to yahalatta in yi haka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salam. 'yar uwa asalin hukunci dangane da cikin mace shi ne ba ya halasta a zubar da shi a dukkan mata kansa har sai idan akwai lallurar da Shari'a ta yarda da ita.

    Idan ya kasance cikin yana halin ɗugon maniyyi ne, wato yana cikin kwana arba'in na farko ko ƙasa da haka, to ya halasta a zubar da shi idan har ya zama zubar da shi akwai wata maslaha ta Shari'a ko ya kasance da nufin kawar da wata cutuwa da aka hararo zai iya faɗa wa matar saboda cikin, to a wannan halin ya halasta a zubar da shi.

    Amma tsoron wahalar tarbiyyar yara ba ya shiga cikin wannan halascin, ko rashin ikon ɗaukar nauyayyakinsu, ko nufin ƙayyade adadin 'ya'ya, da wasu uzurorin da ba na Shari'a ba, duk ba sa shiga ƙarƙashin wannan halascin.

    Har-ila-yau, haramun ne a zubar da cikin nan idan har ya ƙetare kwana arba'in, saboda bayan kwana arba'in sun shuɗe cikin yana zamowa gudan jini ne, kuma shi ne farkon halittar mutum, ba ya halasta a zubar da shi bayan kaiwarsa wannan mataki, har sai idan taron likitoci sun tabbatar da cewa cigaba da zaman wannan ciki haɗari ne ga rayuwar mace, suka ce akwai tsoron kada ta rasa ranta idan cikin nan ya ci gaba da zama tare da ita, to a nan ne ya halasta a zubar da shi.

    Duba Fataawal Lajnatid Dá'ima (21/450).

    Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.