𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, malam dan Allah
ina so a ban maganin mallaka amma a cikin ayoyin Kur'ani dan na ji an ce akwai,
saboda ina son saurayina ga shi za a yi maganar kawo kuɗi, kuma malam wallahi
ban da niyyar cutar da shi saboda Allah. Sannan ina so a ba wa kanwata maganin
farin jini a temaka.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam, ‘yar uwa a
magana ta gaskiya, wacce take duk wani malami na Allah da Annabi, in dai ba kuɗaɗenku
yake son ya karɓe ba, to zai faɗa maku cewa ba wasu ayoyi da Allah ya saukar da
sunan ayoyin mallake miji ko saurayi ko na farin jini ga mace, Allah S. W. T.
Bai saukar da Alƙur'ani da manufar haka ba, sai dai kawai ayoyin Alƙur'ani da
hadisan Manzon Allah ﷺ sun bayyana duk hanyoyin da mutum zai bi don ya sami karɓuwa
a wurin Allah da wurin bayin Allah.
Kyawawan ɗabi'u da kyautata
mu'amala su ne tushe na gaskiya da mutum zai mallake zuciyar abokin rayuwarsa,
matuƙar babu kyakkyawar mu'amala a tsakanin mata da miji, ko saurayi da
budurwa, to tabbas komin siddabarun da boka zai ba mutum ba zai taɓa samun
nasarar mallake abokin rayuwarsa ba, in ma ya samu to na ɗan lokaci ne aka yi
masa talala kafin Allah ya kama shi, sannan kuma ga fuskantar mummunar makoma a
wurin Allah ga wanda yake harka da bokaye da ‘yan tsibbu, ko da mai harka da
bokaye ko ‘yan tsibbu ya ga kamar ya ci nasara, to ya sani ba nasara ya samu
ba, talala Allah yake masa domin ya turmutsa shi a Jahannama,🔥 saboda duk wanda ya mutu yana
mu'amala da waɗannan miyagu to lallai zai haɗu da fushin Allah.
Bisa shawara ga wadda take son
mallake mijinta, ko take son ta yi farin jini, to ta dage da yin addu'a ba dare
ba rana, kuma ta dage da kyautata mu'amala a tsakaninta da mijinta idan matar
aure ce, idan kuma budurwa ce sai ta riƙi kyawawan ɗabi'u da addu'a, da jin
tsoron Allah a cikin al'amuranta, ta dalilin haka sai Allah ya ba ki nasara a
rayuwarki, amma duk wata hanya akasin wannan za ta iya kai mutum ga rasa
imaninsa, saboda idan wannan buƙata taki aka yi rashin sa'a kika faɗa hannun
maras tsoron Allah, to zai ce maki ne akwai maganin farin jini ɗin da na
mallaka kuma ta amfani da ayoyin Alƙur'ani, wadda kuma ƙarya ce tsantsa ya faɗa
maki.
Saboda wasu ‘yan tsibbun suna yin
amfani da Alƙur'anin ne wajen yaudarar kwastamominsu, shi wanda bai sani ba da
zarar ya ga an ɗauko Alƙur'ani, ko an karanto wata ayar Alƙur'ani, sai ya za ta
maganin Allah da Annabi za a ba shi, nan kuwa bai san yaudararsa za a yi ta
hanyar amfani da Alƙur'anin ba, don haka a yi taka tsan-tsan a koma ga Allah
kurum!
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.