Ticker

Ina Soyayya Da Wanda Ba Musulmi Ba, Zan Iya Auren Sa Idan Ya Musulunta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam na kasance ina soyayya da wani Inyamiri ya ce min za ki aure ni? na ce masa babu abin da zai hana in aurenka idan ka musulunta, sai ya ce zai je ya yi shawara yadawo, ya ce zai iya musulumta mlm, shin ni kuma zan iya auren sa kuwa in ya musulumta kokuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Matuƙar an tabbayar ya musulunta, to za ki iya auren sa, saboda ayal Alƙur'ni ta hukunta cewa Kada maza musulmai su auri mata mushirikai har sai sun yi imani, baiwa mumina ta fi ‘yantacciya mushirika, haka nan su ma mata Musulmai kada su auri maza mushirikai har sai sun yi imani, bawa mumini ya fi ‘yantacce mushiriki, kamar yadda aya ta 221 da ke suratul Baƙara ta tabbatar.

Don haka idan an tabbatar ya musulunta za ki iya auren sa, amma dai idan labari ya zo ya bayar ya ce ya musulunta , to kada a yi saurin sallama masa har sai an yi bincike. Sannan kuma soyayyar da kika ce kuna yi da shi a halin yanzu, shi kuma wajibi ne ki dakatar da soyayyar har sai ya musulunta sannan a ci gaba da soyayyar, saboda kamar yadda bai halasta ki auri wanda ba musulmi ba, haka nan kuma bai halasta ki yi soyayyar da ake ƙulla aure da ita da wanda ba musulmi ba.3.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments