Ina Yin Chating Da Wanda Ba Mijina Ba, Mene Ne Hukuncina?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam, mace ce tana da aure sai kuma wani daban wanda ba mijinta ba yana koya mata karatu ta WhatsApp, to malam meye hukuncinsu ya halalta su yi ko kar su yi? Na gode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam. A gaskiya wannan babban kuskure ne suke aikatawa, saboda wannan mataki ne na kaiwa zuwa ga aikata ba daidai ba, domin in dai malamin ya amsa sunansa malami, to shi ma ya san wannan kuskure ne, domin yawan hulɗa da mace a inda babu muharraminta, zai iya haifar da afkawa ga saɓon Allah, ko da kuwa hulɗa ce ta addini, saboda hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas, Annabi ﷺ ya ce: "Kada wani mutum ya keɓanta da wata mace face sai da muharraminta". Bukhariy 4955.

    Saboda haka ta ji tsoron Allah ta dakatar da wannan karatu, ta koma makaranta wurin malamai don yin karatu na haƙiƙa, WhatsApp da Facebook ba shi ne wurin da ya kamata a ce ta mayar da shi makaranta na haƙiƙa ba, saboda ba wurin kowane malami ne ake ɗaukar karatu ko ilimi ba, saboda yadda rayuwa ta gurɓace a wannan lokaci da muke ciki. Kuma na tabbatar matuƙar mijinta ya san haka ba zai ji daɗi ba, kuma ba zai yarda da hakan ba, wannan ke ƙara nuna cewa wannan tsarin karatu ba daidai ba ne.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.