Ticker

Ina Yin Whatsapp Ba Da Yardar Mijina Ba, Ya Hukuncina?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Don Allah malam mene hukuncin wanda mijinta ya saya mata waya, kuma ya ce kada ta yi WhatsApp, ita kuma sai ta yi, amma daga 'yan uwanta da take gaisawa da su, sai tambayah a kan abin da ba ta sani ba take yi, don Allah mene hukunci yin haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

A gaskiya yin hakan da ta yi ba daidai ba ne, domin wannan saɓa wa umurnin miji ne, kuma saɓawa umurnin miji ga mata kuskure ne babba matuƙar umurnin da mijin ya yi mata ba na saɓon Allah ba ne, kuma Allah zai tambaye ta a game da hakan, saboda ai shi yin WhatsApp ba dole ba ne, kuma yin tambaya don a warware abin da ya shige duhu game da addini ba dole sai ta WhatsApp ba, asali ai makaranta ce wajen neman ilimi ba ta Internet ba, musamman ma na addini saboda kaucewa gurɓatattun malamai da muggan aƙidoji na ɓata, samun ilimi da fatawowi a gaban malamai shi ne aula, kuma shi ne asali, don haka ta daina yin WhatsApp ɗin nan har sai ta sami yarda daga wajen mijinta, hakan shi ne mafi alheri a gare ta. Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments