Matar Auren Da Ta Yi Zina, Shin Aurenta Ya Lalace

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Mene ne hukuncin matar auren dataje ta yi zina, shin aurenta yananan kokuma yalalace? Sannan kuma dole ne saitayi ISTIBRA'I kafin mijinta ya sake saduwa da'ita kokuma a'a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    wa'alaikum salam... Hakika laifine babba ga Musulmi yaje ya'aikata zina, Shin yanada da aure ko bashida aure haramunne agareshi ya yi Zina, domin Zina tana daga cikin manyan laifuka da Allah(ﷻ) ya haramta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, Kamar yadda Allah(ﷻ) yakecewa:

    وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا (سورة الإسراء/32)

    FASSARA:

    Allah(ﷻ) ya ce: kada ku kusanci zina, domin ita alfahashace da kuma mummunar hanya:

    Danhaka yazama wajibi agareta ta tubaga Allah(ﷻ) ingantaccen tuban da ba za ta sake aikata irin wannan danyen aikiba.

    To amma dangane da maganar cewa ko auren yananan ko bayanan, zance mafi inganci shi ne auresu yananan, hakanan magana mafi inganci daga cikin zantukan da Malamai sukayi a kan wannan matsala shi ne cewa mijinta zai'iya cigaba da saduwa da'ita batareda ta yi wani ISTIBRA'I ba, duk dacewa akwai Malaman da sukace dole saitayi ISTIBRA'I, wasu sukace jini za ta yi wasu kuma sukace jini za tayi, to amma magana mafi inganci babu wani ISTIBRA'I daza tayi, domin idan ɗaya daga cikin ma'aurata yaje ya yi zina, to wannan zinar ba za ta ɓata auren da ke tsakaninsuba, amma inda a ce mace batada aurene to shi ne za ta yi istibra'i, Sai dai abin da Malamai sukace shi ne idan Miji yasan cewa Matarsa mazinaciya ce to mafikyau yarabu da'ita, domin za ta'iya ɓata masa Zurriyya, to amma idan ya kasance ciki yashiga asakamakon zinar datayi, to ashari'ance za'ajingina wannan cikin kokuma ɗan da tahaifa zuwaga Mijin da take aure amatsayin ubansa, saboda Manzon Allah(ﷺ) ya ce:

    (الولد للفراش وللعاهر الحجر)

    Sai dai idan shi Mijinne yakore ya ce ba ɗansa ba ne to shikenan sai ajinginashi zuwaga Mahaifiyarsa.

    WALLAHU A'ALAM

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.