Ticker

    Loading......

Me Ya Sa Aka Shar’anta Saki?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam na ga Allah yana son aure, to don Allah me ya sa Shari'a ta yarda da saki?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Addinin musulunci ya yi umarni da dukkan abubuwan da za su karfafa aure, sai dai wani lokacin ma’aurata suna haɗuwa da wasu mushkiloli waɗanda za su sanya rabuwarsu ta zama ita ce ta fi alkairi, Allah Ya na cewa a cikin haka: “Idan ma’aurata biyu, suka rabu, sai Allah ya wadata kowa daga yalwarsa”. Suratu Annis’ai aya ta: 130.

Akwai hikomomi da dama, da suka sa Allah ya shar’anta saki, ga wasu daga ciki:

1. Zai iya yiwuwa ɗaya daga cikin ma’aurata ya ga ba zai iya jure dabi’un abokin zamansa ba, ya kuma shiga damuwa saboda haka, sai ya kasance babu wata hanya da za a iya warware mushkilar sai ta hanyar rabuwa.

2. Idan har ba a shar’anta saki ba, to ɗaya cikin ma’aurata idan ya gaji da dan’uwansa zai iya neman hanyar da zai huta daga shi, ta hanyar kashe shi, ko kuma illanta shi, kamar yadda hakan ya faru ga wasu daga cikin ma’aurata, ga wasu misalai dana gani da idona wasu kuma na ji labarinsu:

Akwai matar dana sani, wacce saboda kiyayyar da take yiwa mijinta ta saka masa garin batiri a cikin abincinsa, saboda kawai tana so ya mutu ta huta da shi.

Akwai wanda na sani, saboda da kin da matarsa take masa, ta dauki reza za ta yanki al’aurarsa lokacin da suka zo saduwa.

Akwai wacce ta kashe mijinta, saboda ba ta son shi.

duka waɗannan mushkilolin za a iya warware su ta hanyar saki.

3. Idan mace mijinta ba ya birgeta za ta iya rikar kwarto ya rinka biya mata bukatarta, kamar yadda shima namiji zai iya yin hakan, hakan kuma zai haifar da ɓarna a cikin al’umma.

4. Zai yi wahala namiji ya yi adalci ga matar da ba ya sonta, ka ga saki zai zama hanya mafi sauki wajan warware matsalar.

Allah shi ne Mafi sani

🏼Amsawa

Dr. Jameel Zarewa

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments