𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne Hukuncin Namiji Mai Biye-Biyen Mata Bayan Yana Da Aure Iyalinsa Tana Iya Kokarinta Wajan Bashi Hakkinsa.?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Lallai wannan
mijin bai kyauta ba kuma abun da yake aikatawa haɗarine
mai girma agareshi anan duniya da kuma lahira, kuma abun bakin cikine yakamata
yagane bashi kaɗai
keda hakki a kanki ba, kema kina da hakki a kansa ya nuna kulawa da kishi da
kuma barin abun da duk zai ɓata
miki rai, kozai saki damuwa matukar wannan abun ba saɓon Allah ba ne.
Shi ne wanda
shari'ar musulunci take kira da dayyus, wato sakarai shasaha wandaba ya kishin
matarsa ko kannensa mata ya kyalesu sakaka suna abun da sukaga dama, ko kumaba
ya kishin matarsa kwata-kwata, kawai yadauki matarsa amatsayin mai dafa masa
abunci ba ruwansa, zaije ya yita mu'amala da wasu matayen, wannan sharri ne mai
girma, domin irin waɗannan
matayen ne in ba a samu mai tsoran Allah ba, itama sai tafaɗa wasu dabi'u da ababe
marasa kyau, akwai waɗanda
tsabar lalacewa sune suke baiwa matayan nasu dama cewa suma suna iya yin
mu'amala da kowa, hakika matarka tanada daraja da mutunci domin ita ce
suturarka kamar yanda Alƙur'ani yanuna, ba daidai ba ne kabarta gida kaje kana biyewa
wasu akwararo, kuma ya kamata kasani waɗannan
waɗanda kake biyewa
bawani abu sukafi taka matarba, kai takama tafisu kawai saboda su sun tuɓe rigar mutunci suna fito
na fito da Allah ne har kake ganin wani abu atare dasu, domin suɗin kamar shaddar kasuwa
suke kowa zai hausu ya yikashi.
lallai wanna
miji naki yakamata yaji tsoran Allah yatuba yadena, kuma kicigaba da rokon
Allah Allah ya shiryar miki dashi, sannan kibi duk wasu hanyoyi na hikima da
fasaha ki nunar masa abun da yake yana matukar kona miki rai, kuma ki tunatar
da shi lallai wannan mugun aikine yake, inda hali ki haɗa da abokansa iyayensa da duk wanda kika san
yanajin nauyinsu danya dena wannan dabi'a yadawo gareki, inkinbi duk waɗannan hanyoyin bai daina
ba, kinemi taimakon Allah kawai a raba aurenku Allah ya musanya miki da mai
kishinki mai kiyaye addinin Allah madaukakin sarki.
Hadisi yazo
daka manzan Allah sallahu Alaihi wasallam, daka abdullahi dan umar Allah yakara
masa yarda ya ce manzan Allah ya ce, (mutane uku Allah yaharamta musu aljannah,
wanda ya dawwama yana shan giya har yamutu, da kuma maiyawan saɓawa iyayensa, da kuma
dayyus sakaran da yake tabbatar da ɓarna
a cikin iyalinsa ba ya kishinsu,)
Imamu Ahmad.
Malam haisami ya
ce: a cikin mu'ujamul zawa'id a cikin hadisin akwai rawin da ba a ambata ba,
amma sauran mutanen da suka ruwaito shi dukansu amintattu ne, Dabarani ya
ruwaito daka Ammar bin yasir Manzonn Allah ﷺ
ya ce: (Mutane uku, ba za su shiga aljannaba har abada, Mace mai kamanceceniya
da maza, da kuma wanda yake shan giya har yamutu, da dayyus sokwan da ba ya damuwa da wanda yake shiga wajan
ahlinsa,ba ya kishinsu.
A bisa wannan
duk wanda ya yi duba da hadisn farko duk da hadisi nabiyu akwai rauni a cikin
ruwayarsa, zai fahimci dayyus shi ne wanda yake kyale ɓarna a cikin iyalinsa tana wakana kuma baidamu
ba, ko yake bada kofar da kowacce irin ɓarna
za ta iya faruwa a kan iyalinsa, domin duk wanda bai damu da matarsa baba ya kishinta
yana bin wasu awaje, hakika yakyale babbar kofa ta faruwar fitina a cikin
iyalinsa. Sa'annan kuma wadda keda miji irin wannan kuma ta tabbatar da yana
wannan biye-biyen matan, ba zargi ba ne to sai ta fara masa nasiha cikin hikima
da kuma rokon Allah ya shiryar mata da mijinta da cigaba da gyara jikinta sosai
ta hanyoyin da suka halatta (maganar gaskiya da yawan matanmu na arewacin ƙasarnan
suna wasa da gyaran jikinsu) da yawan mazaje shi yasa shaiɗan ke samun galaba a kansu
sai na wajen suke ba su sha'awa kuma alhali ba komai suka fi na auren ba kawai
su na auren basa gyara jikinsu ne, to idan tabi duk waɗannan matakan tayi-tayi yaƙi
dainawa to sai ta janyo magabata a cikin lamarin, idan ya ƙi bari to za ta iya neman rabuwa da shi Allah
ya musanya mata da wani nagari saboda yana iya dauko musu wani ciwo can wajen
fasikancin nasa. Allah ya kiyaye!
ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.