Mene Ne Hukuncin Yin Addu'a Da Hausa A Cikin Sallah?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamou Alaikum, Malam ina kwana da fatan kun tashi lafiya, Malam ina da tambaya shin ya halasta yin Addu'a a sujada na sallar farillah da Hausa dan na ji wani malami yana cewa bai halastaba, Malam mine ne bayani?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salám, ‘yar uwa malaman Fiƙhu sun yi saɓanin fahimta a kan yin addu'a da harshen da ba Larabci ba a cikin sallah, akwai fahimtar da ta ce:

    1. Ya halasta ga wanda ba ya iya yin Larabci ya yi addu'a da wani harshe a cikin sallah, amma bai halasta ga wanda ya iya kyautata Larabci ba, idan kuma har ya yi da harshensa alhali ya iya kyautata Larabci, to sallarsa ta ɓaci.

    2. Sai kuma fahimtar da ta ce Ya halasta ga wanda ya iya kyautata Larabcin da wanda ma bai iya Larabcin ba su yi adddu'a a cikin sallah da harshensu.

    3. Fahimta ta uku kuma suka ce; bai halasta ga wanda ya iya kyautata Larabci da wanda bai iya ɗin ba ma su yi addu'a da wani harshen da ba Larabci ba a cikin Sallah.

    Duba Almausú'atul Fiƙhiyya Alkuwaitiyya (11/172, 173).

    Amma fahimtar da ta fi zama daidai ita ce ta farko, wato wanda bai iya Larabci ba, ko ba ya iya kyautata shi, to ya halasta ya yi addu'ar da harshensa ko da a cikin Sallah ne, saboda Allah ya san ma'anar abin da kowane harshe yake nufi, kuma ba ya ɗora wa rai face sai abin da za ta iya.

    Shaikhul Islam ya ce: "Addu'a ta halasta a yi ta da Larabci ko ba da Larabci ba, Allah Mai Tsarki ya san nufin mai roƙonsa da abin da yake nema, ko da harshensa bai tsayu ba, lallai Allah ya san abin da amon sautuka ya ƙunsa duk da saɓanin harsuna, duk da mabambantan buƙatu".

    Dubi Majmu'ul Fataawá (22/489).

    Saboda haka, ‘yar uwa ba laifi ga wanda bai iya Larabci ba ko bai iya kyautata shi ba ya yi addu'a da harshen da ba Larabci ba a cikin sujjada, amma makaruhi ne ga wanda ya iya Larabci sosai ya yi addu'a da wani harahe a cikin sallah.

    Allah S.W.T ne mafi sani

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    HUKUNCIN YIN ADDU’A DA HAUSA A CIKIN SALLAH

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Malam, wani ne ya ce wai malamai sun bayar da fatawar cewa ya halatta mutum ya yi addu’a da Hausa a cikin sallah. Ni kuma na ce, gaskiya ban taɓa ji ba! Shi ne nake tambaya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Ba abin mamaki ba ne a samu bambancin fatawa a kan mas’alolin fiqhu, saboda bambancin mahangar da malamai suke duban mas’ala ta cikinsu.

    Muhimmin abu dai shi ne: Kowannensu ya ji tsoron Allaah, kuma ya gina bincikensa da maganganunsa a kan tubali ƙaƙƙarfa na ilimi, ba son-zuciya ko bin sha’awar-rai ko shaci-faɗi ba.

    Babu wani malami guda a bayan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya zama tsararre daga yin kuskure, ko mantuwa, ko zamiya a cikin maganganunsa na ilimi.

    Don haka, dole ne duk malami na-Allaah ya zama cikin shirin karɓar gyara daga duk inda ta fito, matuƙar dai kuskurensa a cikin maganganunsa da fatawoyinsa sun bayyana.

    Nau’ukan addu’a a cikin Sallah iri biyu ne: Akwai Du’aa’ul Mas’alah da kuma Du’aa’ul Ibaadah.

    1. Na-farkon shi ne wanda a cikinsa akwai nema da roƙon Allaah a fili cewa ya biya wata buƙata, ko dai ta hanyar tunkuɗe wani sharri, ko kuma ta hanyar janyo wani amfani ga mai yin addu’ar. Alal misali: Addu’ar Buɗe Sallah mai lafazin

    اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ ؛ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ ، اللَّهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدِ

    Ya Allaah! Ka nisantar da abin da ke tsakanina da kura-kuraina, kamar yadda ka nisanta a tsakanin Gabas da Yamma! Ya Allaah! Ka tsaftace ni daga kura-kuraina, kamar yadda ka tsaftace farar tufa daga datti! Ya Allaah! Ka wanke ni daga kura-kuraina da ruwa da ƙanƙara manya da ƙanana.

    Amma Du’aa’ul Ibaadah kuwa ita ce, wadda a cikinta babu roƙo ko neman wata buƙata a fili daga Allaah Maɗaukakin Sarki, sai dai kawai karanta kalmomin girmamawa da kambama Ubangiji Ta’aala, kamar wani lafazin na addu’ar Buɗe Sallaah, cewa

    سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ ، وَتَعَالَى جَدُّكَ ، وَلَآ إِلَهَ غَيْرُكَ

    Ya Allaah! Tsarki ya tabbata gare ka haɗe da godiyarka; kuma Sunanka ya yi albarka; kuma martabarka ta ɗaukaka; kuma babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai kai!

    Sannan yawancin wuraren da ake yin karatu a cikin sallah sanannu ne, kuma kafaffu ne, waɗanda mutum ba shi da ikon sauya su, ya zo da waɗanda ba su ba, kamar haka

    1. Bayan kabbara kafin a fara karatu: Addu’o’in Buɗe Sallah. Kafaffu ne.

    2. A tsaye kafin Ruku’u: Karatun Fatihah da Surah. Kafaffu ne.

    3. A bayan Fatihah: Ameen. Kafaffe ne.

    4. Addu’a don kawar da waswasi: Isti’azah. Kafaffiya ce.

    5. A cikin ruku’u: Zikirori da Addu’o’i. Kafaffu ne.

    6. Dagowa daga ruku’u: Zikiri ne kafaffe.

    7. A cikin Sujada: Zikirori da Addu’o’i. Kafaffu ne.

    8.  A zama tsakanin sujada-biyu: Zikirori da Addu’o’i. Kafaffu ne.

    9. Kafin ruku’un raka’ar ƙarshe: Qunuut na Wutri , kafaffe ne.

    10. Bayan ruku’un raka’ar ƙarshe: Qunuut na Naazilah , ba kafaffe ne. Amma yana dacewa da yanayi ne.

    11. Zaman Tahiya: KaratunTahiya, kafaffe ne. Addu’ar neman tsari daga sharrin abubuwa huɗu, kafaffe ne. Sauran addu’o’i da zikirori kafin sallama, kafaffu ne.

    Daga nan an fahimci cewa

    1. Yawancin wuraren yin addu’o’i a sallah kafaffu ne, mutum ba ya iya zuwa da wata addu’arsa ta musamman a tare da su, ko a maimakonsu.

    2. Addu’o’in Al-Qunuut da aka ce ana iya ƙarawa, ana ƙarawa da abin da ya dace da yanayin da ake ciki ne. Kuma da Larabci ake yi, ba da wani yare kamar Hausa ba.

    3. Ko a cikin Sujada da aka riwaito cewa: Ku yawaita yin addu’a a cikinsa, da kuma Zaman Tahiya da aka riwaito cewa: Sannan sai ya zaɓi addu’ar da ya fi so ya yi , manyan malamai irinsu Al-Imaam Ahmad sun zaɓi cewa: Ma’anarsa ita ce: Ku zaɓo daga cikin waɗanda suka inganta daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).

    Kuma duk mun san cewa: Ba da Hausa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi addu’o’insa ba.

    Sannan kuma ga Sahabi Mu’awiyah Bn Al-Hakam (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya gai da mai atishawa a cikin sallah a masallaci. Daga baya kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kira shi, ya gaya masa cewa:  Wannan sallar, babu wani abu na maganar mutane da ke gyara ta. Ita dai tilawar Alqur’ani ce da zikirin Allaah kawai.

    Idan kuwa har yin maganar Sahabi da harshen Larabci a cikin sallah za a nuna cewa ba ya gyara sallah, to ina kuma ga wanda ya yi da wani yaren da ba Larabcin ba, kamar Hausa?!!

    Kuma idan muka yarda da cewa, ya halatta a yi addu’a a cikin sallah da Hausa saboda hujjar wai mai yin addu'ar bai iya Larabci ba, to ranar da wani ya zo da cewa, ya halatta a yi karatun Fatihah ko Surah a cikin sallar da harshen Hausa ko Fulatanci ko wani harshen da ba Larabcin ba, saboda irin wannan dalilin cewa bai iya Larabci ba, me za mu ce masa?!

    Tun da akwai sauran wuraren da Shari’a ta bayyana cewa ana karɓar addu’a a cikinsu, waɗanda ba cikin sallah su ke ba, kamar: A tsakanin kiran sallah da iqamah; da ƙarshen dare; da lokacin saukan ruwan sama; da lokacin da musulmi ke cikin tafiya; da ranar Jumma’a, musamman daga bayan la’asar kafin faɗuwar rana, da sauransu. Meyasa musulmi ba zai yi addu’a a waɗannan lokutan da yarensa ba? Meyasa zai nace sai ya yi addu’a da yarensa a cikin sallah, ta yadda zai iya samun matsala dangane da sallarsa?

    A ƙarshe: Kar mu manta: Wanda ya bayar da fatawa a kan halaccin hakan, ba fa wata aya ko hadisi ya janyo a fili ƙarara mai nuna halaccin hakan ba, a iya saninmu. Illa dai kawai a fahimtarsa da addini ne yake ganin babu matsala idan musulmi ya yi addu’a da yarensa a cikin sallah! Shi ne muke cewa: Idan aka tafi Lahira kuma ya zama an samu matsala fa?!

    Don gudun hakan gara dai mutum ya nisanci saka kalmomin da ba daga harshen Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suka fito ba, a cikin sallarsa.

    Wannan fahimtarmu kenan a kan wannan mas’alar a yanzu. Wanda ya zo da hujjar da ta fi wannan a shirye mu ke, mu karɓa daga gare shi, kuma mu sauya matsayinmu, in shaa’al Laah.

     WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

    08164363661

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.