Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Yana Tilasta Mini Zubar Da Ciki, Yaya Matsayina?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalmu alaikum malam ina da tambaya, ni ce muke tare da mijina muna zaman lafiya amma ya ce mun ba ya son haihuwa, in na samu ciki sai ya sani dole na zubar, in na ki sai ya ba ni a wani abu in sha ban sani ba, sai cikin ya zube, malam meye hukuncina a wurin Ubangijina?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu, ‘yar uwa lallai Allah ba ya hukunta wata rai da laifin da wata rai ta aikata, saboda yin hakan zalunci ne, shi ko Allah ba ya zalunci, kamar yadda ya hana a yi zalunci. Duk wani laifi da aka tilasta wa mutum ya yi shi, to idan ya yi wannan laifi saboda an fi ƙarfinsa, to Allah ba zai kama shi da laifin wannan aiki ba, saboda hadisin da Abu Zharril Gifáriy ya ruwaito cewa: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Lallai Allah ya share wa al'ummata abin da suka yi da kuskure, da abin da suka yi da mantuwa, da abin da aka tilasta masu yin sa". Ibn Majah 2043.

    Lallai shi mijin ne za a ɗora wa laifin, musamman ma idan cikin ya kai watanni huɗu an hura masa rai.

    Saboda ba ya halasta a zubar da ciki bayan ya cika wata huɗu, zubar da shi a bayan ya kai wata huɗu kisan rai ne, saboda a lokacin an riga an hura masa rai, kamar yadda Bukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 3208, Muslim kuma a hadisi mai lamba ta 2643.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.