Mijina Ya Tafi Shekara Uku Ya Ƙi Dawowa, Me Yakamata In Yi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum, malam miji ne ya tafi wata kasa ya bar matarsa har tsawon shekara uku, kuma ta ce yaushe zai dawo? Ya ce babu lokaci, ita kuma ta gaji da wannan yana yin, domin tana tsoron kada ta fada wata hanyar daban, to malam me ya kamata ta yi? Mene hukuncin wannan Aure? Ina yi wa malam fatan Alkhairi, na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salám. Macen da mijinta ya bar ta na lokaci mai tsawo, to ba ta fita daga cikin hali guda biyu:

    1. Ko dai mijin nata ya ɓace na tsawon lokaci ba tare da jin labarinsa a ko'ina a faɗin duniya ba, to wadda ta sami kanta a irin wannan hali, mafi yawan malamai sun ce za ta jira ne har tsawon shekaru huɗu daga lokacin da ba a gan shi ba zuwa cikan shekaru huɗun, idan bai dawo ba, kuma ba a sami labarinsa ba kwata-kwata, to sai ta yi idda irin ta wadda mijinta ya rasu, wato iddar wata huɗu da kwana goma.

    2. Ko kuma ta zamana rashin ganin mijin nata ba na gaba ɗaya ba ne, ana da labarin inda yake, za a iya zuwa a iske shi a inda yake, to wannan matarsa ba za ta yi wani aure ba a bisa ijmá'in malamai, sai dai idan rashin ganinsa ya riƙa cutar da ita, to a nan tana da damar neman Alƙali ko wanda ke madadin Alƙali da ya ɓata wannan aure, sai ta yi idda ta auri wani.

    Saboda haka wannan aure na wannan mata da mijinta ya tafi shekara uku bai dawo ba, kuma ya ce ba lokacin dawowa, to har yanzu auren nan yana nan ingantacce, sai dai a nan matar tana da damar kaiwa alƙali ƙara don ya ɓata auren saboda cutuwa da take yi na rashin cika mata haƙƙoƙin aure, Shari'a ce kawai ke da wannan damar bayan ta nemi ya dawo ya ƙi dawowa.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.