Mijina Yana Kira Na Da Ummiy, Shin Wannan Zihari Ne?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

     Assalamu alaikum, malam Allah ya saka, don Allah ya halasta iyaye maza ko mata su dinga bin bakin yaransu wurin koya masu kira? Misali miji yana so yaronsa ya dinga kiran matansa da Ummi, to zai iya cewa ga ummi nan ta dawo ko ga daddy nan. Shin ba shi da kamanceceniya da ZIHARI?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam, ‘yar uwa ya fi kamata mazaje su guji kiran sunan matayensu da irin waɗannan kalmomi irin su mama ko momi ko ummi da makamantansu da nufin su koya wa ‘ya’yansu, saboda akwai ‘yar shubha a ciki, sun yi kama da zihari, sai dai abin da ke bambanta su da zihari shi ne manufar yin kowanne daga ciki, amma dai kai tsaye wannan ba zihari ba ne, saboda shi mai yin zihari yana nufin haramta wa kansa matarsa ce ta hanyar daidaita ko kamanta matsayin mahaifiyarsa ko wani sashe na jikin mahaifiyarsa ko duk wata muharramarsa da matarsa a zance mafi inganci, kamar mutum ya ce wa matarsa; 'ke a wurina kamar cinyar mahaifiyata ce', ko 'ke a wurina kamar farjin mahaifiyata ce ko na ‘yar uwata, ko na ‘yar uwar mahaifiyata, ko kamar na ‘yar uwar mahaifina', da makamantan haka, duka waɗannan zihari ne, duk wanda ya yi wannan matarsa ta haramta a gare shi har sai ya yi kaffara.

    Shi kuwa wancan mai kiran matarsa da momi ko ummiy ba yana nufin mahaifiyarsa ba ce ta haihuwa, yana faɗi ne da nufin koya wa yaransu don kada su riƙa kiran sunan mamarsu da sunanta na asali, don haka ne ya zama ba zihari ba ne, dalilin da ke nuna wannan ba zihari ba ne shi ne:

    Abu Dawud ya ruwaito hadisi cewa; wani mutum ya ce wa matarsa: "Ya ‘yar uwata", sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa: "‘Yar uwanka ce ita?", sai Annabi ﷺ ya ƙyamaci hakan, ya kuma hana shi ci gaba da faɗin hakan. Duba Abu Dawud 2210.

    Al'Imam Ibn Katheer Addimashƙiy ya ce: "Wannan maganar ta Manzon Allah ﷺ inkari ne ga wancan mutum, amma kuma duk da haka bai haramta masa matarsa saboda wancan maganar ba, domin ba yana nufin ‘yar uwa ta jini ba ne, da a ce haka yake nufi, da ta haramta a gare shi, domin babu bambancin hukunci tsakanin uwa da sauran muharramai kamar ‘yar uwa, da ‘yar uwar uba, da ‘yar uwar uwa, da makamantansu". Duba Tafseerul Ƙur'anil Azeem 4/452.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.