Mu san tauhidi 02: shin rubuta alƙur'ani da hadisi da sahabbai (RA) suka yi bidi'ah ce? Shin sallar tarawee bidi'ah ce?

    Domin da yawan '‘yan bidi'ah suna cewa hakanma Bidi'h ne.

     GA YADDA ABIN YAKE

     Dukkan wanda ya raba bidi’a zuwa bidi’a mai kyau da mara kyau to wannan ya yi kuskure,

     Kuma ya saɓawa faɗin Manzon ALLAH {s.a.w} saboda faɗinsa: Dukkan bidi’a ɓatace.

    [Abudawud ya ruwaito shi].

     Domin Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi hukunci a kan bidi’o’i da cewa baki ɗayanta ɓata ce,

     Ya yin da shi kuma wannan yana cewa ba kowacce bidi’a bace ɓata, harma wasu na cewa akwai wata bidi’a wai mai kyau.

     Babban malami Ibnu Rajab (RH) yana cewa a sharhin da ya yi wa Arba’una

    Hadis:

     Faɗin shi {s.a.w}: Dukkan bidi’a ɓatace, yana cikin tararrun maganganu da babu wani abu da zai fita daga ciki, kuma babban tushe ne mai girma daga cikin tushen addini,

     Kuma ya yi kama da faɗinsa {s.a.w}: Duk wanda ya farar a cikin al’amarin nan namu abin da babu shi to an mayar masa.

     To dukkan wanda ya farar da wani abu

    kuma ya jingina shi ga addini, alhali kuma ba shi da wani asali a addini to za a mayar masa kuma ɓata ne.

     Addini kuma ya barranta dashi, ko da abin yana cikin abin da ya shafi aƙida ne ko ayyuka ko kuma zantuttuka na zahiri ko na baɗini.

     Wato shi ɗan bidi'ah bashi da wata hujja na cewar akwai wata bidi’a mai kyau sai dai suna hujja da maganar Umar (RA) a kan sallar tarawihi, a inda ya ce: Madalla da wannan bidi’ar.

     Suka kuma ce: Ai waɗansu abubuwa sun faru, waɗanda yake magabata ba su yi inkarin suba,

     kamar haɗa Alƙur’ani a littafi guda, da kuma rubuta Hadisi da haɗa shi.

    To amsar anan ita ce:

     Lallai waɗannan al’amura suna da asali a addini ba ƙagaggu ba ne.

     Maganar Umar (RA) Madalla da wannan bidi’ar’.

     Anan bawai yana nufin sun ƙirƙiro wani aiki a cikin addini ba ne a'a, sai dai wata sunna ce da ta yi bacci su kuma suka farkar da ita.

     Bayan rasuwar Manzon ALLAH {s.a.w} Umar Ɗan Khaddab (R.A) ya haɗasu a bayan liman guda, kamar yadda suka kasance a bayan Manzon ALLAH {s.a.w} wannan ko ba bidi’a ba ne a addini.

     Domin kuwa Manzon ALLAH {s.a.w} shi yafara sallatar wannan sallah a masallaci har sau uku a mabanbanta lokuta,

     Hujjar kuwa ta nan cikin hadisi mai lamba 1129 Sahih Bukhari.

     Haɗa Alƙur’ani da akayi a littafi guda yana da asali a shari’a,

     Domin Manzon ALLAH {s.a.w} Ya kasance yana umartar a rubuta Alƙur’ani,

     Sai dai ya kasance a rubuce ne daban-daban sai sahabbai (R.A) suka haɗa shi a littafi guda, domin a kare shi, daga rasashi a kan ƙasa.

     Haka shima rubutun Hadisi yana da asali a addini, domin haƙiƙa,

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi umarni da rubuta wasu hadisai ga wasu cikin sahabbansa a lokacin da aka nemi hakan,

     Kuma babban abin da akaji wa tsoro na rashin rubuta shi a zamanin Manzon ALLAH {s.a.w} shi ne gudun kada a haɗa shi da Alƙur’ani alhalin ba Alkur’ani ba ne,

     To a lokacin da Manzon ALLAH {s.a.w} ya rasu sai wannan abin tsoron ya kau, domin Alƙur’ani ya cika an kuma haddaceshi kafin rasuwar Manon ALLAH {s.a.w},

     Sai al’ummar musulmi suka rubuta Hadisi bayan haka domin bashi kariya daga ɓacewa, ALLAH ya saka musu da alkhairi a kan wannan

    aiki da suka yi wa Musuluunci da kuma Musulmai,

     Yadda suka kare littafin ALLAH da kuma sunnar Manzon tsira {s.a.w} daga ɓacewa a doron ƙasa.

    ALLAH kabamu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka gafartamana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.