Shin Dole ne Mai Niyyar Azumtar Sittu Shawwal Ya ƙulla Niyya Tun Dare?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Dole ne Mai Niyyar Azumtar Sittu Shawwal Ya ƙulla Niyya Tun Dare?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    An tambayi Shaik Usaimeen Rahimahullahu Shin azumin Sittu shawwal da Azumin Arfa hukuncinsu ɗaya da Azumin Nafila wajan ƙullah niyyah, Sharadine tabbatar da niyyarsu cikin dare, ko hukuncinsu daya da Azumin nafila wanda yake a sake ba ƙayayyade lokacin yin sa ba, dole sai an ƙulla niyyarsa a cikin dare kafin fitowar Alfijir?

    Sai ya ba da Amsa: Azumin Sittu shawwal da Arfa Ba kamar Sauran Azumin nafila ba ne, Dole ka ƙudurci niyyar yin sa cikin dare akafin alfijr ya keto.

    Da Mutum Zai tashi bayan hudowar alfjir baici komai ba sai atsakiyar rana ya niyyaci azumtar sittu shawwal bayan nan ya azumci kwana biyar, ba za a ce ya Azumci kwana shida ba, sai dai a ce ya azumci kwana biyar da rabi, domin dukkan ayyuka saida niyya.

    Bazai Samu ladan Ragowar yinin dabai niyyaci azumin a cikinsa ba.

    Babul Maftuhu (21/55) da Sharhin Mumti'i (6/360)

    Amma Azumin nafila wanda yake (Mudlaƙ) A sake yake ba ƙaidi, basharadi ba ne saika ƙulla niyyar yin sa cikin dare ba, shi duk lokacinda ka ƙulla niyyar yin sa da rana har zuwa faduwar rana azuminka ya yi, da sharadin in ba ka ci komai ba, ko ba ka aikata wani Abu da yake karya Azumi ba.

    Amma Azumin Nafila wanda aka iyakanceshi da lokacin yin sa dole ne ka ƙulla niyyar yin sa cikin dare kafin hudowar alfjir.

    WALLAHU A'ALAM .

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.