𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malan ina wuni.
Dan Allah ina da tambaya: An ce in mace tana da janaba a jikin ta babu kyau ta
shayar da ɗan ta. Shin yaya abun yake? Nagode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa
barakatuhu.
Gaskiya dai ni ban san wata ayah ko
hadisin da a cikinsa aka haramta wa mace ta shayar da yaronta alokacin da take
da janabah ba. Hasali ma ban taɓa jin haka daga bakin wani Malami daga Maluman
Fiƙhu ba, ko awani littafi daga litattafan Fiƙhu.
Sai dai abin da ya zamto tabbatacce
shi ne ya halatta mace mai haila ko mai janabah ko mai jinin biƙi ta shayar da
jaririnta awannan yana yin da take ciki. Domin babu abin da yazo a kan haramcin
yin haka, kuma shi addinin musulunci sauki gareshi babu Ƙuntatawa.
Abin da bai halatta gareta ba, shi
ne aiwatar da wata ibadah wacce ake bukatar tsarkin jiki a cikinta. Misali
kamar sallah, ko dawafi ko ɗaukar Alƙur'ani Mai girma. Hakanan ba ya halatta ga
mijinta ya sadu da ita bayan daukewar jini har sai ta yi wanka.
WALLAHU A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.