Shin Uwa Ce Take Da Haƙƙin Riƙe Yara Bayan Mutuwar Aure Ko Mahaifinsu?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Mal. Barka da yau da fatan anyi sallah lafiya. Tambayata ita ce shin idan mutum ya rabu da matarshi sannan akwai 'ya'ya tsakaninsu shin wa keda haƙƙin rike yaran domin kula da tarbiyarsu? Bayan haka ita matar ta yi aure sannan shi miji bai gamsu da yana yin natsuwarta ba. Nagode a huta lfy.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullah.

    Shi haƙƙin rikon yaro bayan rabuwar aure yana wuyan mahaifiyar yaron ne, mutukar dai ba a samu wata matsalar da za ta hana ita uwar ɗaukar dawainiyar kulawa da yaron ba.

    Dalilin da ya sa ake fara gabatar da uwa fiye da uban yaro awannan matakin saboda ita uwa tafi uban yaro sanin halayensa da kuma hanyar da za ta bi wajen tarbiyyantar da yaron bisa kyawawar dabi'a.

    Kuma ita uwa tafi uban yaro nuna tausayi da tausasawa da soyayya da hakuri da juriya wajen ɗaukar wahalhalun kulawa da rayuwar yaro. Misali kamar irinsu wanka da wanki da ɗaukar yaro zuwa duk inda za taje.

    Sayyiduna Abdullahi bn Amr bn Al aas (Allah ya yarda dasu) ya ruwaito cewa "Wata mata tazo wajen Manzon Allah ﷺ sai ta ce masa "Ya Rasulallahi wannan yarona ne. Cikina ya kasance shi ne wajen ɗaukarsa (Madaukinsa) Kan cinyata ya kasance shi ne matattarinsa, kuma nonona ya kasance shi ne abin shansa, amma yanzu kuma mahaifinsa (wato mijina wanda muka rabu) yazo yana raya cewar zai kwaceshi daga gareni".

    Sai Manzon Allah ﷺ ya ce mata "KE KIKA FI CHANCHANTA DA RIKESHI, MUTUKAR BAKIYI AURE BA".

    Imamu Ahmad da Abu Dawud da Baihaƙiy da Hakim ne suka ruwaitoshi.

    Amma akwai sharudan da shari'a ta shimfida kafin ita kanta uwar ta chanchanta da rikon yaron. Daga cikin sharudan nan akwai:

    1. HANKALI: Matar da ta samu tabuwar hankali ba ta chanchanta a bar mata rikon yaro ko yara ba.

    2. IKON BAYAR DA TARBIYYAH: Idan uwar ta kasance ita kanta ba ta da tarbiyyah, to ba ta chanchanta da rikon yaro ba, domin ita kanta ba ta da tarbiyyah ballantana har ta bayar.

    3. RIKON AMANA DA KYAWUN HALAYE: Idan ta kasance fasiƙa ko barauniya, ko mai bayyanar da ayyukan saɓon Allah, to ba ta chanchanta abar mata rikon yaro ba.

    4. MUSULUNCI: mafiya rinjayen maluman musulunci sun tafi a kan cewa bai halatta abar wa mace kafira tarbiyyar yaro Ƙarami ba.

    5. 'YANCI: Bai halatta ga mace baiwa ta rike yaro Ƙarami ba, saboda rashin isassun lokutan kulawa da rayuwar yaron.

    6. RASHIN YIN AURE: Idan ta yi aure to shikenan haƙƙin kulawa da yaron ya faɗi daga kanta.

    Idan ta kasance kamar yadda ka faɗa cewar ba ka gamsu da yana yin tatbiyyarta ba, to abin da yafi dacewa shi ne abar yaron akarkashin kulawar kakarsa ta bangaren uwa, ko 'yar uwar mahaifiyar yaron.

    WALLAHU A'ALAM.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.