𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ya halart a fara ramuwar azumi washe garin
sallah ko biyu ga sallah ko uku ga sallah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idin ƙaramar
Sallah rana ɗaya ne
kawai, shi ne ranar ɗaya
ga watan Shawwal.
Abun da ya
shahara a bakunan mutane na cewa idin karamar Sallah yana wanzuwa har zuwa
kwana uku bayan ranar idi ko bakwai ko abun da ya yi kama da haka, wannan kawai
Abun da mutane suka samu yankinsu ko Al'adarsu akaine kawai, wanda ya shahara
tsakanin mutane ba a dora hukuncin shari'a a kansa.
Imamul Bukhary
Allah ya jiƙansa
da rahama ya ce: Babin da zai yi magana a kan azumi ranar idin ƙaramar
Sallah.
Sannan ya koro
hadisin Abu sa'eed Allah yaƙara masa yarda ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya
hana azumi ranar idin ƙaramar Sallah, da Babbar Sallah.
Saboda haka
ranar idin ƙaramar
Sallah rana ɗaya ce, ita
ce ranar da Azumi a cikinta yake haramun, amma rana ta biyu data Uku ga watan
shawwal ba Haramun ba ne azumi a cikinta, ya halatta yin azumin ramuwa kona
nafila.
WALLAHU
A'ALAM.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.