Ticker

Shin Ya Halasta Waɗanda Suka Yi Zina Su Yi Aure?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam idan mace ta sadu da namiji sai ya nemi su yi aure, to ya za su yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, asali dai malamai sun ce ba ya halasta mutum ya auri mazinaci ko mazinaciya har sai idan sun tuba, to amma idan mazinaciya ta tuba daga wannan zina, to ya halasta a aure ta, haka nan idan mazinaci ya yi tuba ta gaskiya daga yin zina shi ma ya halasta a aure shi.

Haka nan namiji da macen da suka yi zina da junansu, ya halasta su yi aure a tsakaninsu matuƙar sun yi tuba ta gaskiya. Wannan tubar ita ce za ta ba su damar auren. Allah shi kyauta ya ƙara shirya mu.

Don neman ƙarin bayani a duba ALMUHALLÁ (9/618.)

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments