Ticker

Shin Ya Halatta Mace Mai Haila Ta Dauki Takardar Alƙur'ani?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam Shin ya halitta mace ta taɓa alƙur'an wanda ba cikakke ba idan za taje islamiyya lokacin da take haila?

sako daga aisha sani katsina

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A'a bai halatta mace mai haila ta taɓa Alƙur'ani cikakke ko wanda ba cikakke ba. Domin kuwa ko da ayah ɗaya ce arubuce ajikin takarda, hukuncinta da alfarmarta kamar na cikakken Alƙur'ani ne, wajen girmamawa da wajibcin kiyaye alfarmarsa.

Domin kuwa yazo a cikin Muwatta Malik, hadisi daga Amru bn Hazmin (Allah ya yarda dashi) ya ce Manzon Allah ﷺ ya ce: "KADA WANI YA TAƁA ALƘUR'ANI SAI WANDA YAKE DA TSARKI (CIKAKKEN TSARKI)". - Hadisi na 468.

A cikin sharhul Umdah, juzu'i na 1 shafi na 385, an tambayi Shaikhul Islam Ahmad bn AbdilHaleem Al Harraniy (Ibnu Taimiyyah) game da hukuncin taɓa takardun da ke ɗauke da rubutun Alƙur'ani ya yin da mace take cikin jinin haila. Sai ya ce: "duk abin da akwai rubutun ayoyin Alƙur'ani ajikinsa, to hukuncinsa daidai yake da ɗaukar mus'hafi (wato cikakken Alƙur'ani) idan zallar rubutun Alƙur'anin ne ajikinsa.

Amma idan akwai wasu abubuwan da ke rubuce awajen tare da ayoyin Alƙur'anin, to anan kuma hukuncin ya danganta ne da abin da yafi rinjaye. Ya halatta a taɓa litattafan tafseeri da hadisi da fiƙhu waɗanda ke ɗauke da wasu ayoyin Alƙur'ani".

A takaice dai bai halatta gareki ki ɗauki cikakken Alƙur'ani ko juzu'i ba, amma ya halatta ki buɗe application na Alƙur'anin da ke cikin wayarki ki karanta, ko da kina cikin hailar.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments