Waƙar Damina Ta Sheikh Na'ibi Sulaiman Wali

    Bismillahi Allah madawwami
    Shi mahallicin mu Rahimi
    Mai yawaita alheri magami
    wanda ya yi ɗari ya yi gumi
    Wanda ya yi rani da damina.

    Komai yanayi mai ma'ana
    Dan hikimominsa Rabbana
    Masu yawa ko a ko'ina
    Tabaraka Sarkin sarakuna
    Ya sa ni'imomi ga damina.

    Nomau manomi mai dariya
    Tsaya inai maka tambaya
    Shin me yake saka dariya
    Ko kana da jikkar zinariya
    Koko ka ci riba da damina.

    Sai ya kada baki da hanzari
    Ya ce da ni kai albishiri
    Yau zuciya ta ta yi fari
    Zaƙin ta ya zarce sukari
    Na ga alama ta damina.

    Daga kai ka dubo samaniya.
    Ka ga gajimarai na tafiya
    Kafin na bushe da dariya
    Sai na ji tsawa da walkiya
    Suna bushara da damina.

    ....................................

    ....................................

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.