Wata Shida Mijina Bai Kusance Ni Ba, Ya Matsayin Aurenmu?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Da fatan an tashi lafiya malamanmu Allah ya kara muku lafiya da nisan kwana mai amfani. Dun Allah malam tambayata ita ce kamar yanzu miji ba ya biyanma matarsa bukata ta kwanciyar aure har na tsawon wata shida, mene ne matsayin wannan auren? kuma ta ki takai karansa, to malam na ji wasu sun ce wannan aure sai a hankali, don Allah malam a warware min. Allah ya kara basira.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salámu, idan miji ya ƙauracewa saduwa da iyalinsa na tsawon wani lokaci saboda ƙin ba shi wajiban haƙƙoƙinsa na aure da ke kan matar, kuma matar ta toge a kan haka, bayan kuma ya yi mata wa'azi ya tsoratar da ita Allah a kan haƙƙoƙin aure da suka wajaba a kanta amma duk ta ƙi gyarawa, to a nan miji yana da damar ƙaurace wa matarsa a shimfiɗa gwargwadon yadda ya so, don ya zama ladabtarwa a gare ta, har sai ta bayar da haƙƙoƙin mijinta da ke kanta a bisa yardarta.

    Saboda Annabi ﷺ ya ƙaurace wa matayensa na tswon wata ɗaya bai shiga wurinsu ba, amma ta fuskar magana kuwa bai halasta ya ƙaurace wa yin magana da ita fiye da kwana uku ba, saboda ya inganta daga Annabi ﷺ a hadisin Anas bin Malik Allah ya ƙara masa yarda ya ce: "Ba ya halasta ga Musulmi ya ƙaurace ma ɗan uwansa fiye da kwana uku." Albukhariy (6076), Muslim (2558).

    Amma idan miji ya ƙaurace wa saduwa da matarsa na fiye da wata huɗu, don kawai manufar cutar da ita, ba don tana ƙin bayar da wajiban haƙƙoƙin mijinta ba, to wannan hukuncinsa kamar wanda ya yi EILÁ'I wa matarsa ne, ko da kuwa bai yi rantsuwa a kan yin hakan da ya yi ba.

    Idan kimanin lokacin Eilá'i (إيلاء) ya cika, wato wata huɗu a ɗaya daga cikin fahimtar malamai, kuma ya ƙi dawowa ya sadu da matar nan tasa, tare da kasancewar yana da ikon yin hakan amma ya ƙi, ba kuma don tana cikin al'ada ko nifasi ba ne, to a nan za a umarce shi ne cewa ya sake ta, idan har ya ƙi ya dawo wa matar tasa, kuma ya ƙi ya sake ta, to Alƙali sai ya sake masa matar, ko kuma ya ɓata auren, amma idan ita matar ce ta nemi yin hakan.

    Duba FATAAWÁL LAJNATID DÁ'IMA (20/261) domin ƙarin bayani.

    Ko a duba BIDÁYATUL MUJTAHIDI WA NIHAYATUL MUƘTASIDI (3/118).

    Saboda haka 'yar uwa, matar da mijinta bai kusance ta ba fiye da na tsawon wata huɗu aurensu yana nan a matsayin aure, amma tun da har ya wuce wata huɗu, wanda kuma su ne tsawon lokacin kwanakin Eilá'i amma bai dawo ya sadu da ita ba, alhali yana da ikon yin hakan, to a nan tana da damar kai shi ƙara a inda ya dace, don a tilasta masa kusantarta, ko alƙali ya sake ta ko ya ɓata auren idan tana son hakan, tana da wannan damar.

    Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.