Ya Hukuncin Miji Mai Yawan Rantsuwar Zai Yi Saki

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, barka da warhaka malam, Don Allah ya namijin da duk abin da ya haɗa shi da iyalinsa, sai ya dunga ikirarin zan iya sakin ki wallahi, kuma ba ɗaya ba, zan iya sakin ki uku? Allah ya kara maka daukaka.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu, mijin da ke ce wa matarsa zai iya sakin ta ba za a ce ya yi wani laifi ba idan ya kasance wacce ba ta jin nasiha ce har sai ya haɗa mata da tsoratarwar sakin, wata ƙil hakan ne kaɗai kan sa ta natsu idan ya hana ta yin wani abin ta ƙi hanuwa. Kuma wannan magana tasa ba saki ba ne.

    Sai dai bai dace mutum ya zama duk abin da matarsa ta yi masa babba da ƙarami ya riƙa mata barazanar saki ba, saboda wani abin bai kai girman da za a yi barazanar saki ba. Haka nan bai dace yawan yin rantsuwa a duk lokacin da zai faɗi kalmar ba, sai dai faɗakar da mace da kalmar saki a inda aka buƙaci hakan ba laifi ba ne kamar yadda ya gabata.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.