A KAN WA LAYYA TAKE WAJIBI?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Asssalamu Alaikum Malam. Shin a kan wa layya take wajibi? maza kaɗai aka umarta suyi ko har da mata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Malamai sun yi Saɓani akan layya shin wajibice mutum zai samu zunubi in baiyi ba? Ko sunnah ce mai karfi ba'aso mutum ya barta?.

    Sahihiyar Magana Sunnah ce mai Ƙarfi.

    Sharaɗin Sunnantuwar layya shi ne: Wadatar Mai layya, Ma'ana ya zama Abunda zaiyi layyar dashi ya ƙaru akan buƙatar sane ta yau da kullum, da Buƙatar waɗanda yake ciyar dasu, Idan Mutum Albashi yake karɓa kowanne wata, ko Wani Abun rayuwa, idan Albashinsa yana isarsa, Harya Samu kuɗin layya, layya ta Hau kansa.

    Shardantuwar Wadata a layya shi ne faɗin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Wanda yake da wadata baiyi layya ba, kada yakusanci Masallacin mu.) Ibnu majah (3123) Albani ya Ingantashi acikin Sahihu ibnu majah.

    Layya An shar'antawa mutanen gida saboda faɗin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ( Akan dukkan mutanen gida akwai layya da yankan rajab)

    Ahmad (20207) ibnu hajar ya ce: Isnadinsa mai karfine, Albani ya kyautatashi acikin Sunanu Abu dauda (2788).

    Bau Ban-banci tsakanin Namiji ko Mace, Idan mace tana rayuwa ita kaɗai, ko tare da 'ya'yanta akwai layya akansu.

    Yazo a Mausu'ah fiƙhiyyah (5/81),

    "Mazantaka ba ta daka cikin Sharuddan layya, sharaɗin wajabci ko Mustahabbanci, Kamar yanda ta wajaba akan Maza, haka take akan mata, domin Dalilan wajabci da Mustahabbanci Sun haɗe gaba daya ne.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.