Abokina Yana Mafarkin Saduwa Da Namiji

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Abokina Ne Yake Mafarki Dana Miji Suna Saduwa, Abun Yana Bashi Tsoro Sosai, Takai Inya Zauna Cikin Abokansa, Sai Yaji Sha'awa Ta Kamashi Saidai Ya Tashi Daka Wajan, Bayason Jinsin Sa Na Miji Ya Zauna Kusa Dashi, Kuma Bai Dena Mafarkin Ba, Ya Zai yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Irin Wannan mafarki damai Kama dashi suna cikin mafarkai waɗanda ba a san gani, suna kunnowa daka Shaiɗan ne, Abun da Musulmi ya dace ya yi idan yai irin waɗannan mafarkan munana ko yaga mafarkin da bayaso, yai tofi aɓarin hagu ɗinsa sau uku, ya nemi tsari daka sharrin Wannan mafarkin da sharrin Abun da ya gani, sannan sai ya juya akan ɗaya ɓarin nasa yaci gaba da baccinsa, Mafarkin Ba zai cutar dashi ba, kada ya baiwa kowa labari, saboda faɗin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (Mafarki Mai kyau daka Allah ne, Mummuna ko baragadan mafarki daka Shaiɗan ne, idan ɗayanku yai mafarkin da yake tsoro yai tofi aɓarin hagu ɗinsa ya nemi tsarin Allah daka Shaiɗan mafarkin ba zai cutar dashi ba, Bukhari Babin Bad'ul kalƙi (3049).

    Idan Kai mafarki wani yana jima'i dakai, Wannan ya Saɓawa dabi'a.

    Abun da ya kamata kabayar da kulawa akai shi ne lazimtar Neman Tsarin Allah da Shaiɗan, da kuma lazimtar Koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, riƙo da Zikirorin yini da dare, da zama da Alwala, Kwanciya bacci da Alwala Neman tsari da karanta Falaƙi da Nasi da Ƙul-huwa ka shafe jikinka yayin Kwanciya bacci.

    Lazimtar Karanta Alƙur'ani ko Sauraronsa, Da Abokantaka da Mutanen kirki.

    Da naci Wajan rokon Allah ya tsareka daka dukkan wani Mugun mafarki da Mugun aikin da baya so.

    Da roƙonsa ya fiddaka Wannan marhala ta balagar farko dake ciki lafia ba tare da aikata ko zamewa zuwa aikata abun da baya so ba.

    Babu shakka kana cikin Marhala mafi haɗari arayuwar matashi ta fuskar sha'awa wato Shawa'ar balagar farko, tafi kowacce tashin hankali da hatsari ga Matashi.

    Amma Matuƙar ka lazimci Zikirori da Addu'a da dabbaƙa abun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya koyar yayin kwanciya bacci babu shakka za ka wanye lafiya.

    Muna Roƙon Allah ya tsareka damu Da sauran musulmi daka dukkan Wani mummunan Mafarki da dukkan wani abun ƙi.

    Wallahu A'alamu.

    🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.